Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa
Published: 17th, April 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya Suke Bukata
Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab.
Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan.
A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata, jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National ” bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar.
A cikin watan maris da ya gabata ne shugaba Al-Sharaa na kasar Syriya ya rattaba hannu a kan wata yarjeniya da shugaban dakarun kurdawan kasar Siriya SDF Mazlum Abdi dangane da hade dakarunsa da sojojin kasar Siriya, sannan yace tsarin tarayya ya sabawa wannan yarjeniyar.