Xi Ya Isa Kuala Lumpur Domin Ziyarar Aiki A Malaysia
Published: 15th, April 2025 GMT
A yammacin yau ranar 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Kuala Lumpur ta jirgin sama na musamman, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Malaysia.
Xi Jinping ya gabatar da rubutacciyar jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama, inda ya ce, yana fatan daukar wannan ziyara a matsayin wata dama ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, da kara amincewa da juna a fannin siyasa a tsakanin bangarorin biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin ayyukan zamanantarwa, da sa kaimi ga yin mu’amala da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi, da inganta gina al’umma mai kyakkaywar makomar bai daya tsakanin Sin da Malaysia zuwa wani sabon mataki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya
Da wadannan shaidu na zahiri, muna iya cewa himmar kamfanonin kasar Sin ta fuskar kirkire-kirkiren fasahohi, ya sanya hajojin kasar zama masu tafiya da yanayin zamani, wanda har kullum ake ta kokarin daidaita ci gabansa da bangaren kare muhalli, da aiwatar da matakai na inganta yanayin duniya.
Tun daga yankin kudu maso gabashin Asiya zuwa Turai, daga Latin Amurka zuwa gabas ta tsakiya har Afirka, ana ta ganin karuwar ababen hawa masu aiki da lantarki kirar kasar Sin, a wani yanayin dake shaida kwarewar kamfanonin kasar a fannin kirkire-kirkire fasahohi na zamani, wanda daga karshe ke dacewa da samar da hajoji irin wadanda kasuwannin duniya ke alfahari da kuma bukatar su. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA