Iran Da Armenia Suna Fara Atisayen Hadin Giwa Don Karfafa Tsaron Kan Iyakar Kasashen Biyu
Published: 10th, April 2025 GMT
Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen.
Burgediya Janar Sayyid Mortaza Mira’in babban hafsan sojojin kasa na IRGC ya bayyana cewa, wannan atisayennn yana nuna irin yadda sojojin IRGC suke da shirin kare kasar daggga duk wata barazana. Da kuma abota da kyautata makobtaka da kasashe mmmakobta.
Labarin ya kara da cewa ana gudanar da rawan dajin ne a kan kan iyakar kasashen biyu na nordooz.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Jihar Jigawa Ta Bukaci Karamar Hukumar Roni Ta Samar Da Karin Ajujuwa Ga Fulani Makiyaya
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya tunasar da karamar hukumar Roni game da bukatar gina wani rukuni mai dauke da ajujuwa guda biyu ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya domin inganta rayuwar su.
Shugaban kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki biyu da kwamatin ya yi a karamar hukumar Roni.
Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce tanadin gina ajujuwan ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya na kunshe cikin kasafin kudin kananan hukumomi.
Ya kuma bayyana gamsuwa da bin kyakkyawan tsarin sadarwa tsakanin bangaren zartaswa da na kamsiloli ta yadda bangaren kamsiloli ya nemi bayani kan jerin ayyukan raya kasa da karamar hukumar ta ke yi a rubuce, bangaren zartaswa kuma ya mayar da jawabi a rubuce.
Da ya ke mika rahoton Karamin kwamatin da aka dorawa nauyin duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Roni ta gudanar daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu, wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari ya duba aikin kwaskwarima ga shaguna guda shida da karamar Roni ta ci gado a garin Kazaure.
Kazalika, Alhaji Usman Tura Wanda ke tare da Wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza ya kuma duba aikin gyaran karamin asibiti da kuma ginin bandaki a garin Tuntube da aikin ginin filin wasannin gargajiya da runfunan kasuwa guda biyu da kasuwar shanu a yankin Daneji na garin Sankau da shataletale a Rani Kan Hawa.
Ya yabawa shugaban karamar hukumar Roni bisa kokarinsa na biyan diyyar filin da aka gina asibitin Tuntube, wadda aka yi jinkirin biya fiye da shekaru 15, da ma kokarinsa na karbo gonakin da ‘yan karamar hukumar Makoda ta jihar Kano su ka ci iyakar karamar hukumar Roni.
Da yake mayar da jawabi, shugaban karamar hukumar Roni Dakta Abba Ya’u ya ce zai shirya taro domin ganawa da manyan ma’aikata da nufin tattaunawa Kan matakan da su ka dace a bi wajen aiwatar da shawarwari da gyare gyaren da kwamatin ya bayar domin cigaban karamar hukumar.
Sauran ‘yan kwamatin sun hada da mataimakin shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama da na Kiyawa da na Buji da na Kanya, sai kuma Oditoci biyu da mataimakin sakataren kwamatin Sadiq Muhammad.
Usman Mohammed Zaria