Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala biyan sama da naira biliyan 13 na garatuti, wanda ke nuna wani gagarumin mataki na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar.

 

Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2025 da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.

 

A cewar Mummuni, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce wajen ganin ta magance kalubalen da ma’aikata da masu ritaya ke fuskanta a jihar.

 

Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tana sane da korafin ma’aikatan da aka yi kuskuren cire su daga lissafin albashin sakamakon aikin tantance ma’aikatan da aka kammala.

 

“Gwamnati ta riga ta kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan don shawo kan lamarin, muna da yakinin za a kammala hakan nan ba da dadewa ba.”

 

Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa, bisa la’akari da muhimmiyar rawar da ma’aikata ke takawa, gwamnatin Lawal ta dauki kwakkwaran matakai na kyautata jin dadinsu da yanayin aikinsu.

 

“A wani bangare na wannan kokarin, mun fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan gwamnati.

 

Mummuni ya ci gaba da bayanin cewa, bayan albashi, gwamnatin ta ba da kulawa ta musamman ga halin da ‘yan fansho maza da mata ke ciki wadanda suka sadaukar da shekaru da dama wajen yi wa jihar hidima.

 

Ya kuma amsa bukatun ma’aikata dangane da karin girma, inda ya bayyana cewa ana magance batun aiwatar da karin girma, musamman ga wadanda ke da karin girma ko sama da haka ba tare da daidaita albashi ba.”

 

“A wannan rana ta musamman, ina jinjina wa juriya da jajircewa da ma’aikatan Zamfara suke yi, ina yaba wa jajircewarku, Allah Ya saka muku da alheri,” ya kammala.

 

Tun da farko, Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Majalisar Jihar Zamfara, Kwamared Sa’idu Mudi, ya roki gwamnati da ta magance matsalolin da ma’aikata ke fuskanta.

 

Wadannan sun hada da cikakken aiwatar da sabon mafi karancin albashi, sakin tsarin albashin da aka amince da shi, sake duba kudaden fansho, da maido da ma’aikatan da aka yi kuskuren cire su daga lissafin albashi.

 

Kwamared Mudi, ya yabawa gwamnatin jiha bisa nasarorin da ta samu kamar gaggauta biyan albashi da fansho, da kuma biyan kashi 30% na albashin ma’aikatan gwamnati a fadin kananan hukumomin a matsayin kari na wata 13.

 

Shima da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC reshen jihar Zamfara, Kwamared Sani Halliru, ya jaddada muhimmancin ranar ma’aikata wajen ganin irin gwagwarmayar da ma’aikata da kungiyoyin kwadago ke yi na samar da ingantacciyar yanayin aiki.

 

Ya koka da cewa ba a sake duba kudaden fansho na wata-wata ba a cikin shekaru 27 da suka gabata, sabanin dokar fansho da ta tanadi sake duba duk shekara biyar.

 

“Mai girma gwamna, la’akari da cewa ma’aikatan Zamfara ba sa cikin wani shiri na fensho, muna kira ga gwamnati da ta gaggauta aiwatar da tsarin fansho mai dorewa.”

 

Yayin da yake yaba kokarin gwamnati na yaki da rashin tsaro, ya bukaci hukumomi da kada su sassauta, domin rashin tsaro ya kasance babbar barazana a jihar.

 

Ya kuma yi kira ga sauran ma’aikata da su gudanar da bukukuwan farin ciki tare da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da jajircewa da kuma riko da ayyukansu na tallafa wa ci gaban jihar Zamfara.

 

 

COV/AMINU DALHATU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zamfara jihar Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakin Gwamnan Neja Ya Ki Halartar Bikin Ranar Ma’aikata, Ana Zargin Akwai Takun Saka

Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai taɓa kin halartar bikin Ranar Ma’aikata ba tun bayan da ya zama mataimakin gwamna.

Sabanin shekarar da ta gabata, Kwamred Garba bai bayyana a wannan shekarar ba duk da cewa Gwamna Bago da Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas, Sani Musa, sun halarta, lamarin da ya ƙara zafafa zargin rikici tsakaninsa da gwamnan.

Wasu majiyoyi sun ce yana wajen gari, yayin da wasu ke ganin ya ƙi halartar taron ne da gangan don guje wa ƙara dagula yanayi mai cike da rashin jituwa a siyasar jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NLC Kano Ta Yabawa Gwamnati Na Kokarin Kyautata Jin Dadin Ma’aikata
  • Gwamna Abdulrazaq Ya Yi Alkawarin Ci Gaba Da Aikin A Kwara
  • Gwamnan Kabawa Ya Tabbatarwa Ma’aikatan Gwamnati Ingantacciyar Walwala
  • Gwamnan Jigawa Ya Halarci Taron Ranar Ma’aikata Ta Bana
  • Ranar Ma’aikata: Gwamnan Kano Ya Biya Basussukan Fansho, Ya ƙirƙiro Sabbin Ma’aikatu
  • Mataimakin Gwamnan Neja Ya Ki Halartar Bikin Ranar Ma’aikata, Ana Zargin Akwai Takun Saka
  • Al’umma Sun Shiga Fargaba Yayin Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Sun Kashe Limamin Da Suka Sace A Zamfara
  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya