Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
Published: 16th, April 2025 GMT
A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Malaysia, daga yanzu manyan kafofin sadarwa kamar kafar yada labarai ta kasar Malaysia za su fara nuna shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay wanda CMG ya shirya.
Shirin ya mai da hankali ne kan muhimman batutuwa kamar gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil Adama, da gadan al’adun gargajiya da kirkire-kirkire, da kare nau’ikan halittu, da mu’amala da koyo a tsakanin al’ummomi, ya kuma gabatar da fitacciyar hikimar shugaba Xi Jinping wajen gudanar da mulkin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai
Kakakin ya kuma jaddada matukar adawa, da tanade-tanaden dokar, yana mai cewa, batun Taiwan shi ne jan layi na farko da ba za a iya tsallakewa ba a dangantakar Sin da Amurka.
Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta mutunta cikakkiyar manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwa uku na hadin gwiwa da Sin da Amurka suka amincewa, ta yadda za ta cika alkawarin da ta dauka na kin goyon bayan duk wani yunkuri na neman ’yancin kan Taiwan, kana Amurka ta kaucewa mika sakwanni na kuskure ga ’yan aware masu rajin neman ’yancin kan yankin na Taiwan, ko shiga duk wata cudanyar ayyukan soji da yankin Taiwan na kasar Sin. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA