Gwamna Dauda Lawal Ya Nada Amirul Hajj Bana
Published: 25th, April 2025 GMT
Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Amirul Hajj karkashin wani kwamiti don sa ido kan ayyukan Hukumar Alhazai ta Jiha a Saudiyya don tabbatar da bin ka’idojin gida da na Saudiyya gaba daya a duk lokacin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Sulaiman Ahmad Tudu ya raba wa manema labarai, ya ce kwamitin zai fara aiki cikin gaggawa.
A cewar sanarwar, mambobin kwamitin sune mai martaba Sarkin Maradun a matsayin shugaban tawagar yayin da Alhaji Habibu Balarabe aka nada a matsayin Sakatare.
Sauran wakilan sune Sulaiman Adamu Gummi, Bello Isah Almufty, Murtala Adamu Jangebe, Abubakar Bello Furfuri Alh Rabi’u Ilili Bakura, Malam Ibrahim Izala, Malama Sadiya Mahe da Malama da Hadiza Muhd Gummi.
Gwamna Lawal ya dora wa kwamitin alhakin kula da ayyukan hukumar alhazai ta jiha da kuma tabbatar da samun nasara da jin dadin alhazan Zamfara baki daya a duk lokacin gudanar da aikin Hajjin 2025.
COV/AMINU DALHATU.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni shidan farko na bana, an kafa sabbin kamfanoni 30,014 na masu zuba jari daga kasashen waje a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna karuwar hakan da kashi 11.7 cikin dari a mizanin duk shekara.
Kazalika, bayanai sun nuna cewa, saka hannun jari daga kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 8.8 cikin dari a tsakanin lokacin.
Har ila yau, jarin da aka zuba daga kasar Switzerland ya karu da kaso 68.6, na Japan ya karu da kashi 59.1, na Birtaniya ya karu da kaso 37.6, sai kuma na Jamus da ya karu da kashi 6.3, kana wanda aka zuba daga Jamhuriyar Koriya kuma ya karu da kashi 2.7 bisa dari. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp