2025-09-24@15:50:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 501
«Yahaya Bello»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ko –Council Of Ulema-na Tafawa Balewa a jihar Bauchi na tarayyar Najeriya Sheikh Dan’azuki Musa tafawa balewa, yayi kira ga kasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya da su dauki darasi a jajircewar JMI da turjiyarta ga HKI, a kuma matsayin hanya tilo ta kawo karshen HKI. Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Sheikh Dan’azumi yana fadar haka a lokacinda yayi hira da shi a Bauchi. Sheikh Dan’azumi ya kara dacewa , gwamnatin Amurka ce bayan dukkan ayyukan ta’addancin da HKI take aikatwa a Gaza. Ya ce kafin yakin kwanaki 12 da HKI ta kallafawa JMI, musulmi sun debe kauna da samun mafita ga matsalar al-ummar Palasdinu wacce aka dade ana fama...
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa. Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar. A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya
Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal. Wanda aka yi amfani da ingantattun shaidun hotuna na ta’asar yakin da Japanawa suka aikata a lokacin kisan kiyashin Nanjing, Fim din na “Dead to Rights” ya ba da labari ne na wani rukunin fararen hula na kasar Sin da suka nemi mafaka a dakin daukar hoto a lokacin muguwar mamayar da azzaluman Japanawa suka yi a birnin Nanjing. A wani yunkuri na neman tsira da rayukansu hajaran-majaran,...
Bayan mutane da dama sun nuna ɓacin ransu kan al’amarin, gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar lamarin, tare da umarnin a miƙa masa rahoton cikin mako guda. Gwamnan, ya taɓa goyon bayan jami’an tsaro wajen kama Danwawu, kuma ya umarci NDLEA ka da su sake shi. Wani jami’i ya ce: “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki wannan aiki na Kwamishina a matsayin cin fuska ga gwamnatinsa da kuma yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.” An ruwaito cewar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani shiri a ɓoye domin kama Danwawu, wanda Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Bakori ya jagoranta. Me Ya Sa Gwamnan Bai Kore Shi Ba? Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi niyyar korar Namadi nan take, amma ya dakatar...
A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.” Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take. Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar ta ce, gwamnan da ke halartar wani taro a Abuja ya yanke ziyarar tasa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa. Gwamna Buni ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Chiroma Buba Mashio, Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da ’yan Majalisar Wakilai. Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, ’yan majalisar dokokin jihar, da kwamishinoni,...
Iyalai ‘yan Sudan da dama ne suka taru a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Alkahira, dauke da jakunkuna da kayayyaki a lokacin da suke shirin komawa gida bayan da suka tsere daga rikicin Sudan. Suna cikin dubban ‘yan kasar Sudan da suka rasa matsugunansu da ke kan hanyarsu ta komawa daga Masar zuwa yankunan da sojojin Sudan suka kwato kwanan baya daga dakarun gaggawa na gaggawa a birnin Khartoum da bayanta tun farkon wannan shekara. Iyalan sun kasance suna jiran shiga jirgin kasa da zai nufi birnin Aswan da ke kudancin Masar. Daga nan ne za su yi tafiya ta bas zuwa babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar....
Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin. Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa...
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi. Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa. Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin. “Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi. Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu. Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...

Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...
Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan. A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho. Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar. Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan...
A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan. Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar...
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa nasarar ayyukan tsaro a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah Ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Farfesa Alhassan Gani, rasuwa a safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 66 a duniya. Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Kafin rasuwarsa, Farfesa Gani yana koyarwa a Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Farfesa Gani, ya yi fice wajen sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi, musamman lokacin da yake jagorantar Jami’ar Kashere. Gwamna Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta’aziyyarsa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana rasuwar Farfesan a matsayin babban rashi ga harkar ilimi da...
Babban sufeton ƴansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya sake tabbatar da ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da cikakken tsaro a faɗin ƙasar nan ta hanyar samun bayanan sirri daga jami’ansu. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya ce rundunar ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan, sannan ya buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da goyon baya domin samar da tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
3- Shan miyagun kwayoyi, jike-jiken magungunan karfin maza da sauran nau’o’in kayan karfin maza da ake amfani da su yau da kullum. Don haka, akwai bukatar a lura da hadarin da zuciya take shiga; bayan shan ire-iren wadannan magunguna na karfin maza. A nan, ana tursasa zuciya ne tare kuma da tunzura ta ta yi aiki tukuru fiye da ikon da take da shi na lafiyarta, wanda hakan ko shakka babu, zai haifar mata da gagarumar matsala. Haka zalika, bugun zuciya yana kara sauri tamkar gudun doki, jini kuma yana hauhawa fiye da lafiyayyen hawa yayin saduwa da iyali. Kazalika, bugun numfashi yana karuwa; domin musayar iska fiye da ikon lafiyar da huhu da jijiyoyin jinni suke da shi, sannan...
A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna. Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba...
A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya. Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.” Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya...
A yayin da ‘yan sandan ke gudanar da bincike a yankin, rahotanni sun ce jami’an sun gano wata mata ‘yar Nijeriya a Coach A-2, Seat No. 27, tare da wani yaro da wata jakar balaguro kala-kala. Rahoton ya bayyana cewa bayan an yi mata tambayoyi, ta bayyana sunanta Doris daga Nijeriya kuma ta ce yaron da ke tare da ita, wanda ta bayyana sunansa Miracle, nata ne. RPF ta lura cewa “da aka yi mata tambayoyi a gaban shaidu masu zaman kansu, matar ta amsa cewa tana dauke da kayan maye.” Daga baya an kai ta zuwa gidan RPF a Panbel domin cikakken bincike. Rahoton ya lura cewa a cikin jakar balaguron, jami’an sun gano bakaken fakiti guda biyu da...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack. Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso...
Kamfanin kera manyan motocin dakon kaya na kasar Sin Sinotruk ya kaddamar da motocinsa kirar H2 mai dakon kaya marasa nauyi da ta H3 ta dakon kaya masu matsakaicin nauyi a kasar Kenya, tare da kamfanin CFAO Mobility a matsayin mai rarraba motocin a cikin gida. Babban manajan kamfanin CFAO Mobility na Sinotruk Sarfraz Premji, ya shaida wa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, an kera samfuran motocin ne ne don kawo sauyi ga masana’antar sufuri saboda suna iya daukar kaya masu nauyi, sannan an sa musu manyan tankunan mai, inda hakan zai rage bukatar yawan zuwa shan mai da kuma ba da damar daukar dogon lokaci ana tafiya, kana wannan zai rage yawan kudin da ake...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...
Gwamnatin kasar Brazil tana shirin bayyana goyon bayanta ga Afirka ta kudu a karar da ta shigar a gaban kotun ICJ dangane da tuhumar jami’an gwamnatin HKI da aikaya kisan kiyashi a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata jaridar kasar Brazil Folha De S tana fadar haka. Sannan kamfanin dillancin labaran reuters ya tabbatar da labarin a jiya Laraba. A shekara ta 2023 ne gwamnatin Afirka ta kudu ta shigar da karar don tabbatar da cewa gwamnatin HKI ta na aikata kissan kare dangi kan kasar Amurka. Wanda ya sabawa dokar hana kissan kare dangi ta MDD ta shekara 1948. Sannan a cikin watan Octoban da ya gabata ne, Pretoria ta gabatar da shaidu da...
Jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman a cire su daga shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS). An ga jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya a jihar karkashin kungiyar ‘yan sandan Najeriya mai ritaya (ARPON), dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar su “Shugaban kasa, NASS da IGP ya kamata a girmama ‘yan sanda su kebe ‘yan sanda daga CPS, su kafa hukumar ‘yan sanda ta fensho don gudanar da gratuity da fansho, idan CPS na da kyau haka, me ya sa AIGs da sauran su suka fice daga cikin shirin? Da yake jawabi ga ‘ya’yan kungiyar a lokacin zanga-zangar lumana a Ilorin, shugaban kungiyar, Yakubu Jimoh,...
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan...
Sanatan ya kuma buƙaci jama’ar Kano ta Kudu da Kano gaba daya da su haɗa kai: “Yanzu lokaci ne da ya kamata mu haɗe da juna domin samun cigaba. Mu daina rarrabuwar kai, mu tsaya tsayin daka wajen ganin burinmu ya cika. Idan muka haɗa kai, babu abin da zai hana mu samun ci gaba da makoma mai kyau.“ A ƙarshe, ya roki shugabannin al’umma da sauran ƴan ƙasa da su goyi bayan wannan yunƙuri tare da ƙin amincewa da duk wata dabara ta rarrabuwa da za ta hana nasarar da ake fata daga ƙirƙiro Jihar Tiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro. KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
Shugaban kasar Korea ta Arewa ya bayyana goyon bayan sag a kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine. Kafafen yada labarai na Korea ta Arewa sun bayyana cewa Kim Jong Un ya fadawa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Layrov, a cikin xiyarar kwanaki 3 da ya kai ziyara kasar. Kasar korea ta Areawa dai ta sha taimakawa kasar Rasha da sojoji da kuma makamai ma yakin da take fafatawa da kasar Ukraine fiye da shekaru uku da suka gabata. Kim ya hadu Lavrov ne a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa da ke Wonsan . Kasashen bi yu sun tattauna karin taimakawa juna a bangaren tsaro. KCNA ya bayyanan cewa shuwagabannin biyu sun tattauna al-amura da...
A cikin wannan mako dai an yi ta murna da farin ciki a fadin jihar Kano inda dubban ‘yan fansho suka fara karbar kudaden fansho da garatuti da aka dade ba su yi ba. Kudaden da aka fitar na ‘yan fansho na jihar Kano, sun kasance wani babban ci gaba a kokarin da gwamnan ke ci gaba da yi na biyan bashin zunzurutun kudi har naira biliyan 48 na kudaden alawus-alawus da kuma na mutuwa da ya gada daga gwamnatocin baya. ‘Yan fansho da suka karbi kudadensu sun nuna matukar godiya ga Gwamna Yusuf kan abin da mutane da yawa ke kira a matsayin hanyar rayuwa bayan shekaru da aka yi watsi da su. Daga cikin...
An nada Dabide Ancelotti, dan gidan tsohon kocin Real Madrid kuma kocin babbar tawagar kasar Brazil Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin Botafogo, in ji kulob din na birnin Rio de Janeiro, Ancelotti, mai shekaru 35, ya shirya fara aikin horarwa na farko bayan ya zama mataimakin mahaifinsa a kungiyoyin Real Madrid, Eberton, Napoli da Bayern Munich. Zai maye gurbin Renato Paiba wanda aka kora bayan Botafogo ta fice a zagayen 16 na gasar cin kofin duniya, Dabide Ancelotti ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa karshen shekarar 2026, ya koma kasar Brazil domin kasancewa cikin masu horar da ‘yan wasan kasar Brazil tare da mahaifinsa, amma an sauke shi daga matsayinsa don ba shi damar karbar ragamar horar da...
Dakarun rundunar “Shahid Izzuddin al-kassam’ da kuma ” Sarayal Kuds” sun sanar da kai jerin hare-hare akan sansanonin ‘yan sahayoniya a yankuna mabanbanta na Gaza. A bayanin da dakarun ” Kassam” su ka fitar sun bayyana hare-hare masu yawa da su ka kai wa ‘yan mamaya, da su ka hada da tarwatsa motocin buldoza biyu samfurin D9 a unguwar Zaituna a cikin birnin Gaza. Haka nan kuma sun kai wani harin a ranar 6 ga watan Yuli wanda su ka rusa tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar amfani da wata nakiya mai tsananin fashewa. Bugu da kari , Kassam ta ce a ranar 9 ga watan Yuli din ta kai wani harin akan sansanin da kwamandoji masu bayar da umarnin...
Ya jaddada buƙatar samar da tsarin adalci da zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar cin moriyar ci gaban fasaha da samun rance cikin sauƙi daga ƙasashen duniya. Ya kuma bayyana yadda Afirka ke fuskantar manyan matsalolin muhalli duk da cewa ba ta fitar da gurbataccen hayaƙi sosai. A gefe guda kuma, Tinubu ya bayyana shirye-shiryen gyaran da gwamnatinsa ke yi, ciki har da amfani da makamashi, yaƙi da sauyin yanayi, gina birane da kuma inganta harkar kiwon lafiya ga kowa. Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran ƙasashe masu tasowa. Jawabin Tinubu a taron BRICS na 2025 ya nuna matakin farko da Nijeriya ta taka a matsayin ƙasa mai ƙawance da BRICS. Nijeriya ta...
Ya tunatar da cewa a bara, Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a ya nemi fassarar doka daga Kotun Ƙoli, inda kotun ta tabbatar da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi. “An samu hukunci daga babbar kotun ƙasa da ke nuna cewa kundin tsarin mulkin mu ya tanadi buƙatar ƙananan hukumomi su samu ’yancin kai – su kasance masu cikakken iko da damar aiki a fannoni daban-daban, ko siyasa ko kuma kuɗi,” inji shi. A cewar sa, bai wa ƙananan hukumomi dama za ta ƙarfafa dimokiraɗiyya a matakin ƙasa da kuma samar da cigaba a cikin al’umma. Idris ya nuna damuwa kan yadda tsarin ƙananan hukumomi ya raunana a tsawon lokaci,...
Wata majiya ta tabbatar da cewa, a yayin da tsohon shugaban majalisar dattawan ya je Jihar Binuwai domin daurin auren jikarsa, “watakila zai yi ganawa da shugabanni da masu goyon bayan tafiyar a shiyyar.” Aregbesola ya samu tarba daga magoya bayansa a lokacin da ya isa Jihar Legas jim kadan bayan kaddamar da jam’iyyar a Abuja. A nasa bangaren, Atiku ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC na jihar Gombe a Abuja karkashin jagorancin tsohon minista kuma Sanata Idris Abdullahi a Abuja, a yammacin ranar Juma’a. Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa shugabannin jam’iyyar “sun dawo ne domin tuntubar yankunansu tare da kafa hanyar kulla alaka da jama’a yadda ya kamata.” “Yan Nijeriya sun riga sun yi taro,...
“Bayan ’yansanda sun yi gaggawar shiga yankin domin kwantar da hankulan jama’a tare da dawo da zaman lafiya, a halin yanzu akwai mutane shida da ake zargi suna tsare a kan lamarin.” Ya kara da cewa, ‘yansandan sun hada kan shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya wajen tattaunawa, wanda hakan ya taimaka wajen kwantar da hankula. “Bayan faruwar lamarin, sai muka gana da shugaban al’umma a wurin, sarkin gargajiya yana tare da mu, muka tattauna kuma muka yi kokarin gano abin da ya faru, suka tabbatar mana da cewa za a wanzar da zaman lafiya,” in ji shi. Ya ce har zuwa ranar Alhamis, Kasuwar Gosa ta koma ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tsauraran matakan sa ido kan ‘yan...
Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba. Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya kai sama da kashi 30 cikin 100, duba da cewa; noman da ake yi a karkara na ci gaba yin karanci. Idan har an rabar da wadannan Taraktoci yadda ya dace tare da horar da manoman da za su amfana, an kuma tabbatar da ana bai wa Taraktocin kulawar da ta kamata da sayar da su cikin rahusa, hakan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.” Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya ga munanan ayyukan da HKI take aikatawa wanda yake cin karo da yarjeniyoyin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.” Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; Abinda Jamus din ta aikata zai mayar da ita wacce za ta amsa tambayoyi a matsayin wacce take yin zuga a aikata laifi. A lokacin da HKI ta fara kawo wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hare-hare dai shugaban...
Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta musu dakile harin. A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin Bayero ya taba bi ta wannan hanyar ba. “Bayan isowarmu daga gidan Dantata domin jaje, wasu matasa sun mamaye titin da duwatsu da makamai a Kofar Kudu. “Lokacin da muka isa Kofar Kudu, sai suka fara jifan mu, amma aka yi sa’a, mun yi nasarar fatattakar su zuwa cikin gida, kuma...
Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam
A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adam. A cikin sakonsa, Xi ya jadadda niyyar Sin na hadin gwiwa da kasashe daban-daban, don tabbatar da shawarar raya wayewar kan duniya bisa tushen adalci, da koyi da juna, da mu’ammala da yin hakuri da juna, ta yadda za a kafa nagartaccen tsarin mu’amalar wayewar kan bil Adam a duniya, matakin da zai gaggauta bunkasa wayewar kan bil Adam, da bunkasar duniya cikin lumana. Shugaba Xi ya kuma yi fatan mahalarta taron za su zurfafa mu’amala, da cimma matsaya daya, da taka rawar ganin wajen karfafa cudanyar al’ummun kasa da kasa, da...
Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da Amurka take bawa HKI yasa tana da hannun a kissan kiyashin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan umurnin takunkuman da aka dorawa Francesa Albanese, jami’a mai kula da tattara bayanai na musamman a kan Falasdinu ga hukumar kare hakkin bil’dama da MDD. Rubio ya bayyana cewa sanadiyyar rahoton ta ne kotun ICC ta fidda samacin kama Banyamin Natanyaho, da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yoav Galant. Banda haka takan bada rahoto kan yadda Amurka da...

Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren. Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari. A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata. Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni. Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100. Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe. A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da ‘ya’yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma...
Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya. Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada...
A matsayin sabon babban manaja, Musa ya buƙaci haɗin kai da goyon bayan kowa don tabbatar da gaskiya da amana a dukkan harkokin kulob ɗin. Ya kuma roƙi magoya bayan ƙungiyar su ci gaba da marawa kulob ɗin baya a wannan sabuwar tafiya ƙarƙashin jagorancinsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin...
Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila. Yana...
Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar. Har ila yau wani jirgin maras matuki na abokan gaba ya kai wani harin akan wata mota a yankin “Safful-Hawa” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. A garin Shab’a kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wani gida, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutanen dake cikinsa. Majiyar asibiti a garin Marja’iyyun ta ce an kai...
Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai girma gwamna, da gagarumin nasarorin da ya samu a hukumance, da kuma jagoranci mai tsari da yake kai domin ci gaba da tsara tafiyar dimokuradiyyar kasa. Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8) Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren yada labarai...
“Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban. Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000. Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000. Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa. Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan...
Sheikh Na’in Kasem shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar bata bukatar Izini don kare kasar Lebanon daga makiyanta. Yama fadar haka ne ga wanda suka cika kunnen duniya kan cewa dole ne kungiyar ta mika makamanta ga gwamnatin kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Sheikh Kasim yana fada a wani jawabin da ya gabatar a ranakun Ashoora na Imam Hussain (a) ta kafar Bidiyo. Ya kuma kara da cewa wadanda suke maganar kungiyar Hizbullah ta mika makamanta ga gwamnatinsa kasar, ya fiye masu sauki su fadawa yan mamaya su fice daga kasar Lebanon su kuma dakatar da hare-haren ta’addancin da suke kawo mata. Ya kara jaddada cewa kungiyarsa zata ci gaba da rike makamanta sannan...
A bana ake bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ana kuma daf da gudanar da sabon zagayen taron jagororin Sin da EU. Sakamakon hakan, jerin ayyukan cudanya a matsayin koli tsakanin sassan biyu na kara jan hankali. A baya-bayan nan, an gudanar da dandalin tattaunawa na manyan jami’ai tsakanin Sin da EU karo na 13 a birnin Brussels na kasar Belgium. Kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugabannin EU, tare da ziyartar kasashen Jamus da Faransa. Bangaren Sin ya jaddada cewa, bunkasar tafarkin ci gaban alaka tsakanin Sin da EU ya nuna kyakkyawar dangantakar sassan biyu maimakon adawa da juna, kuma hadin gwiwarsu shi ne...
Bayan an rufe sararin samaniyar kasar Iran saboda yaki na kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa kasar a ranar 13 ga watan yunin da ya gabata, a yau Jumma’a a bude zirga-zirgan jiragen saman a duk fadin kasar daga karfe 5 na safe zuwa 6 na yamma daga ranar Jumma’a 4 ga watan July 4, 2025. Sake dawo da zirga zirgan jiragen sama yana daga cikin matakan da hukumomi a Iran suka dauka don dawo da nutswa a cikin kasar bayan yakin kwanaki 12 da HKI. Hukumar zirga zirgan jiragen sama na kasar ta dakatar da sauka da tashin jiragen samane jin kadan bayan da HKI ta awkawa Iran da ya ki a ranra 13 ga watan yuni don lafiyar...
Kazalika, gazawar Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da kuma sauran hukumomin na jihohi na sauke nauyinsu, hakan ya nuna a zahiri, na irin kalubalen da ake fuskanta, na rashin sauke nauyinsu, na bayar da agajin na gaggawa. Misalii, an ruwaito cewa, a sansanin na ‘yan gudun hijira na Yelwata, musamman yadda suke kwana a kan tandarmin kasa, tare da kokawa da cizon Sauro, ‘ya’yansu ke ci gaba da zama a cikin yunwa, wanda hakan, ya kara harzuka su, fita yin zanga-zangar. Bisa wasu akaluma da aka samu daga Biniwe, sun nuna cewa, a sansanin na Yelwata, an samu haihuwa 15 da kuma mata da suka samu juna biyu, su 122, wadanda kuma suke ci gaba da rashin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kwamandan Sojojin Iran Ya Ziyarci Gidan Babban Jami’in Sojin Kasar Da Ya Yii Shahada Lokacin Yakin Baya-Bayan Nan
Kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin Iran sun shirya tsaf don kare juyin juya halin Musulunci da kasarsu A yayin ziyarar da ya kai wa iyalan shahidi kwamandan tsaron cikin gida na kasar Iran Kanal Mohammad Alizadeh; Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Jajirtattun sojojin kasar Iran a shirye suke da dukkanin karfinsu wajen kare kyawawan manufofin juyin juya halin Musulunci da kuma dukkanin yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin kowane irin yanayi da kuma fuskantar duk wani mai neman wuce gona da iri. Manjo Janar Amir Hatami, babban kwamandan sojojin kasar Iran, tare da rakiyar Hujjatul-Islam Ahmad Jalili Safat, mataimakin shugaban bangaren rukunan siyasa ta sojojin kasar, Manjo Janar Muhammad...
Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
Rundunar Sarayar Kudus dake karkashin kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da kai wa matsugunin ‘yan share wuri zauna na Sydriot hari da makamai masu linzami da su ka yi sanadiyyar kashe da jikkata sojojin mamaya. Su kuwa kafafen watsa labarun HKI sun samar da cewa, an tsinkayo harba makamai masu linzami guda 3 daga Gaza zuwa Sydriot. A gefe daya dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da cewa sun kai wasu hare-haren da makamai masu linzami zuwa yankin Q20 a sansanin ‘yan share wuri zauna na ” Nir-Ishaq” da “Miftahim. Bugu da kari dakarun na “Sarayal-Kuds’ sun sanar da kai wa tankar yaki samfurin Mirkava hari ta hanyar wata nakiya mai karfi akan hanyar Zannah,dake gabashin unguwar Shuja’iyyah a birnin...
Ko da yake ba a bayyana irin rashin lafiyar da ta kama shi ba, wannan bayani ya kawo ƙarshen jita-jitar da ke yawo game da lafiyar Buhari, musamman bayan da mutane suka lura da jinkirin dawowarsa daga ƙasar waje. Buhari ya bar mulki a watan Mayun 2023 bayan ya kammala wa’adinsa na biyu. A lokacin da yake shugaban ƙasa, ya saba shafe lokaci a Birtaniya domin neman lafiya. Shehu dai bai faɗi ranar da Buhari zai dawo gida Nijeriya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Ko da yake ba a bayyana irin rashin lafiyar da ta kama shi ba, wannan bayani ya kawo ƙarshen jita-jitar da ke yawo game da lafiyar Buhari, musamman bayan da mutane suka lura da jinkirin dawowarsa daga ƙasar waje. Buhari ya bar mulki a watan Mayun 2023 bayan ya kammala wa’adinsa na biyu. A lokacin da yake shugaban ƙasa, ya saba shafe lokaci a Birtaniya domin neman lafiya. Shehu dai bai faɗi ranar da Buhari zai dawo gida Nijeriya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic. A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar. A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar...

Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci
Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa ta bai daya, tare da raya tattalin arziki na teku mai inganci da dai sauransu. A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kafuwar babbar kasuwa ta bai daya a ciki kasar Sin ta dace da bukatunmu na bullo da sabon tsarin neman ci gaba da samun bunkasa mai inganci, don haka ya kamata a aiwatar da aikin bisa manufar kwamitin tsakiya, da daidaita ayyuka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin. Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ibtila’in ambaliyar. Domin sauke shirin, latsa nan
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin. Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki watanni biyu bayan ibtila’in ambaliyar. Domin sauke shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus. Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano. Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan. Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari. Ya ce, kafafen yada labarai sun...
A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94. Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano. Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu. Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.” Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara...

Shugaban Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Mexico: Tunanin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil’adama Da Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Ya Kayatar
Shugaban majalisar dokokin jama’ar kasar Mexico Sergio Carlos Gutiérrez, ya bayyana yayin da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya zanta da shi a kwanakin baya cewa, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya burge shi matuka. Ya ce, an gabatar da tunanin don tattauna yadda sassan kasa da kasa za su zauna tare, da taimakawa juna, da amincewa da bambance-bambance a fannonin tattalin arziki, da yawan mutane, da yankunan kasa a tsakanin kasashen duniya, da sa kaimi ga maida bambance-bambance su zama hanyar dinkewa da juna, da kuma samar da kyakkyawan yanayin zaman rayuwar al’ummun kasa da kasa. Kana yana fatan jama’ar kasashen duniya ciki...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki ya bayyana fatansa gare su, bayan da ya ziyarci kauyen cikin watan Yulin shekarar 2021. Ya ce, bayan fahimtar cewa kauyen ya samu sabbin sauye-sauye a shekarun baya-bayan nan, kuma mazaunansa sun samu karin kudaden shiga, ya yi matukar farin ciki. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan karkashin manufofin JKS, mazauna kauyen za su gina yankunan kan iyakoki, tare da kyautata rayuwar al’ummunsu...
Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...
Ganduje, wanda ya kasance Gwamnan Jihar Kano daga 2015 zuwa 2023, ya zama shugaban APC a watan Agustan 2023 bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu daga yankin Arewa ta Tsakiya. Tun daga wannan lokacin ne wasu daga cikin mambobin jam’iyyar suka fara sukar jagorancinsa, suna ganin naɗa shi ya karya tsarin raba muƙamai na cikin gida da jam’iyyar ke bi. Dama tuni wasu manyan dattawan jam’iyyar da shugabannin yankuna daban-daban suka bayyana rashin jin daɗinsu, inda suka dk ga kira ga jam’iyyar da ta gyara wannan tsari. Majiyoyi sun ce saukar Ganduje za ta samar da haɗin kai a cikin jam’iyyar, da kuma gyara matsalolin rabon muƙamai don sake farfaɗo da APC kafin babban zaɓen 2027. A...
Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos. A yayin ganawarsa da Ousmane Sonko, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal, tare da aiwatar da “Manyan matakai 10 bisa hadin gwiwar abokantaka” yadda ya kamata, da kuma kaddamar da karin ayyukan tallafawa al’umma, tare da sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Senegal domin raya sabbin makamashi, da gina ababen more rayuwa na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan faruwar lamarin ne, wasu fusatattun dalibai matasa suka tare hanyar Agaie-Lapai, suna nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa abokin su. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Yau 23 ga watan Yuni, 2025 da misalin karfe 3 na dare, rundunar ta samu labarin cewa, da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan daba sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai dake unguwar Ndakitabu ta Lapai, amma maharan sun tsere a lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wurin”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na ƙara tsananta, musamman a yankunan Arewa. Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya a kashe su a hanyar Abuja zuwa Kano. A kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a hanyar su ta komawa Kano. Sai na kwanan nan da ya faru a Jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure. NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne da...
’Yan Najeriya mazauna ƙasar Isra’ila sun maƙale bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Isra’ila. Sun nemi agajin Gwamnatin Tarayya game da kan halin ƙuncin da suka faɗa tun bayan ɓarkewar yaƙi. Cikin wani rahoto da Jaridar Punch ta wallafa, ’yan Najeriyar sun zargi gwamnati da rashin kai masu ɗauki yadda da ya kamata, inda suka ce tuni sauran ƙasashe suka fara kwashe ’yan ƙasarsu. Rahoton ya bayyana cewa ’yan Najeriyar sun fi yawa a birnin Ƙudus da Tel Aviv, inda Iran ta tsananta kai hare-hare. A halin yanzu, mazauna Isra’ilar sun bayyana cewa suna ɓoye ne a wurare da babu tabbas kuma rayuwarsu na cikin haɗari, a koyaushe komai na iya faruwa da su.

Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya
Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya da nasara tare, muhimman ginshikai ne na ci gaba mai dorewa na hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fuskar raya tattalin arziki da kasuwanci, inda dukkan bangarorin biyu gami da duniya ke cin gajiya. A halin yanzu, habakar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya, kuma kara hada kai ita ce mafita daya tilo ta shawo kan hakan. Ya ce ci gaban kasar Sin zarafi ne ga...
Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.” Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma hakan ya saɓa da Sashe na 391 na Dokar Laifuka 89, Dokokin Tarayya na shekarar 1990. Hukuncin laifin yana ƙarƙashin Sashe na 392 na wannan doka. A wani tuhumar daban, an zargi Sanata Natasha da yin irin waɗannan kalaman game da Akpabio a cikin wata tattaunawa ta waya da wata Sandra C. Duru a Abuja, a ranar 27 ga watan Maris, 2025. An ƙara tsaurara...
Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna. Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba. Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Ya halarci bikin kuma hakan ba yana nufin ya goyi bayan wata jam’iyya ba ne. Ƙungiyarsa ta nanata cewa Sambo yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma labarin sauya sheƙar nasa ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da ƙoƙarin cimma wasu muradu na siyasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka. Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya. Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike. Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai. NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan matsala da zummar nemo hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan

Cece-Kuce Ya Barke Bayan Ganduje Da Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas Sun Nemi A Sauya Shettima A 2027
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp