Aminiya:
2025-08-16@09:43:42 GMT

Yadda noma ya kankama bayan sulhu da ’yan bindigar Katsina

Published: 16th, August 2025 GMT

A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya.

Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana.

Manoma sun fara noma cikin kwanciyar hankali

Ƙananan hukumomin Batsari, Jibiya da Ɗanmusa na daga cikin wuraren da aka samu wannan ci gaba.

Wasu manoma da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana farin cikinsu da yadda rayuwa ke dawowa dai-dai.

Malam Rabe, manomi daga Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Jibiya, ya ce: “Mu kam yanzu sai mu ce Alhamdulillahi. Lallai sulhu alheri ne a tsakanin al’umma. Ni rabon da na duƙa gonata da sunan noma na fi shekara 8. Amma yanzu gashi ni ne har da yin ɓaɓar shanu.”

Ya ƙara da cewa:  “Jiya sai kusan magariba na baro gona, wanda can baya ƙarfe sha biyu ba ta yi mani. Rabinmu duk hijira muka yi, tun daga nan har Bugaje, Gangara, Zandam da sauran yankuna.”

Sulhu da ’yan bindiga ya sauya fasalin rayuwa

Alhaji Surajo Jibiya, ɗaya daga cikin masu shirya sulhun, ya ce:  “Mun ga canji sosai. Manomanmu duk sun koma gona. Hatta cikin lunguna mun samu labarin sun ci gaba da noma ba tare da wata fargaba ba. Duk inda ba a yi noma ba shekaru biyar da suka wuce, wannan shekarar an yi fiye da tunani.”

A cewar Surajo, hatta tsohon jagoran ’yan bindiga, Abdu Lanƙai, ya koma noma.

“Duk wata yarjejeniyar da aka yi da shi Lanƙai yana bin ta sau da ƙafa. In ya gano mai laifi, zai yanke hukunci nan take.”

Noman kankana ya kankama a Jibiya

Malam Salisu, mazaunin kan iyakar Jibiya da Batsari, ya ce:  “Har waɗanda ba su yi noman kankana ba a baya, yanzu sun yi kuma an fitar da ita zuwa Abuja da sauran kasuwanni. Duk wata matsala da muke tunanin za ta kunno kai, Allah cikin ikon shi har yanzu babu wata matsala da aka samu.”

Koyi da Batsari aka yi

A Batsari, inda aka fara sulhun, ana tafiya da yarjejeniyar yadda ya kamata. Hassan Dogon Faci ya ce:  “Garuruwan da suka kusan zama kufai kamar Batsarin Alhaji, Watangakiyya, Ɗangeza, Zamfarawa, Madogara, Nahuta, Kofa da Dumburawa — a yanzu duk noma ake yi a cikinsu kuma babu wata matsala.”

Ya ƙara da cewa: “Ranar Juma’ar da ta wuce har wa’azi muka je muka yi a garin Labo. Ashe sai mu ce, an samu nasara. Yanzu sai dai mu ji labari ana fama da matsala, amma mu kam Alhamdulillahi.”

Da sauran rina a kaba

Duk da wannan ci gaba, wasu yankuna kamar Ƙanƙara, Bakori, Faskari, Malumfashi da Ƙafur na ci gaba da fuskantar hare-hare. A kwanan nan, an yi garkuwa da mutane akalla goma sha takwas daga Ƙanƙara zuwa Sheme da Kakumi da sauran yankuna.

Manoman yankunan sun ce duk da akwai gonakin da aka noma, yawancin su na bakin gari ne, amma waɗanda ke nesa sun ɓar gonakin saboda tsoron hare-hare.

 

A cikin ƙananan hukumomin Batsari, Jibiya da ƊanMusa da ke Jihar Katsina, al’umma sun ɗauki matakin da ba a saba gani ba — sun yi sulhu da ’yan bindigar daji, waɗanda suka daɗe suna addabar yankin da garkuwa da mutane, kisan gilla da satar shanu.

Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya fara haifar da zaman lafiya da ci gaba.

Manoma sun koma gona

Manoman yankin sun fara komawa gonakinsu cikin daminar bana, suna noma ba tare da fargaba ba. Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa sulhun ya kawo sauyi mai ma’ana.

Malam Rabe, wani manomi daga garin Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Jibiya, ya ce: “Mu kam yanzu sai mu ce Alhamdulillahi. Lallai sulhu alheri ne a tsakanin al’umma. Ni rabon da na duƙa gonata da sunan noma gaskiya na fi shekara 8, ko in ce 10. Amma yanzu gashi ni ne har da yin huɗar shanu.”

Ya ƙara da cewa:  “Jiya sai kusan magariba na baro gona, wanda can baya ƙarfe sha biyu ba ta yi mani a cikin gonar. Ka san daga bisani rabinmu duk hijira muka yi, tun daga nan har Bugaje, ka tafi har can wajen su Gangara da su Zandam da sauran waɗannan yankuna.”

Sulhu ya canza rayuwa

Alhaji Surajo Jibiya, ɗaya daga cikin masu shirya sulhun, ya ce: “Lallai mun ga canji sosai. Manomanmu duk sun koma gona. Hatta da cikin lunguna mun samu labarin sun ci gaba da noma ba tare da wata fargaba ba. Duk inda ba a yi noma ba shekaru biyar da suka wuce, wannan shekarar an yi fiye da tunani.”

Abin ban mamaki shi ne, tsohon jagoran ’yan bindiga, Abdu Lanƙai, shi ma ya koma noma.

“Duk wata yarjejeniyar da aka yi da shi Lanƙai yana bin ta sau da ƙafa. In ya gano mai laifi, zai yanke hukunci nan take.”

Noman kankana ya kankama a Jibiya

Malam Salisu, mazaunin kan iyakar Jibiya da Batsari, ya ce: “Har waɗanda ba su yi noman kankana ba a baya, yanzu sun yi kuma an fitar da ita zuwa Abuja da sauran kasuwanni. Duk wata matsala da muke tunanin za ta kunno kai, Allah cikin ikon shi har yanzu babu wata matsala da aka samu.”

Batsari ta fara, sauran na bi

A Batsari, inda aka fara sulhun, ana tafiya da yarjejeniyar yadda ya kamata. Hassan Dogon Faci ya ce:

“Garuruwan da suka kusan zama kufai kamar Batsarin Alhaji, Watangakiyya, Ɗangeza, Zamfarawa, Madogara, Nahuta, Kofa da Dumburawa — a yanzu duk noma ake yi a cikinsu kuma babu wata matsala.”

Ya ƙara da cewa: “Ranar Juma’ar da ta wuce har wa’azi muka je muka yi a garin Labo. Ashe sai mu ce, an samu nasara. Yanzu sai dai mu ji labari ana fama da matsala, amma mu kam Alhamdulillahi.”

Da sauran rina a kaba

Ƙaramar Hukumar ƊanMusa ta baya-bayan nan ce da ta yi sulhu, kuma ana ganin tasirinsa. Sai dai a wasu yankuna kamar Ƙanƙara, Bakori, Faskari, Malumfashi da Ƙafur, harin ’yan bindiga bai tsaya ba.

A kwanan nan, an yi garkuwa da mutane akalla goma sha takwas daga Ƙanƙara zuwa Sheme da Kakumi da sauran yankuna.

Manoman yankunan sun ce duk da akwai gonakin da aka noma, yawancin su na bakin gari ne, amma waɗanda ke nesa sun bar gonakin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Batsari Ɗanmusa Jibiya babu wata matsala Ya ƙara da cewa wata matsala da yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Liberia Don Inganta Noman Shinkafa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karbi bakuncin Mataimakin Ministan Noma na Jamhuriyar Liberia, David Akoi, a wata ziyara ta musamman domin nazarin dabarun noman shinkafa a jihar, wadda ita ce kan gaba a fitar da shinkafa a Najeriya.

A yayin ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Dutse, Mista Akoi ya ce wannan ziyara za ta ba tawagarsa damar fahimtar dabarun noma da sarrafa shinkafa, samun horo a aikace, tare da koyo game da dukkan sassan harkar noman shinkafa. Ya bayyana cewa, wannan zai taimaka wa Liberia rage dogaro da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje.

“A Liberia muna cin shinkafa safe, rana da dare. A shekarar 1979, an yi tarzomar shinkafa da ta kifar da gwamnatin Shugaba William R. Tolbert bayan yunkurin kara farashin shinkafa,” in ji shi. “Yanzu haka muna shigowa da kimanin kashi 70 cikin dari na shinkafar da muke ci.”

Ya ce gwamnatin Liberia ta kuduri aniyar samar da aƙalla kashi 70 cikin dari na bukatar shinkafar cikin gida. Ya bayyana cewa Shugaba Joseph Boakai ya zabi Najeriya, musamman Jihar Jigawa, saboda irin ci gaban da ta samu a harkar noman shinkafa.

“Mun zo ne domin koyo daga Jigawa yadda ta samu wannan nasara, da dabarun da ta yi amfani da su wajen shawo kan matsalolin noma.” In ji shi. “Manufarmu ita ce mu aiwatar da irin wannan nasara a kasarmu.”

Da yake mayar da martani, Gwamna Namadi ya yaba wa Liberia bisa zaben Jigawa, yana mai cewa wannan hadin gwiwa zai bai wa bangarorin biyu damar musayar dabaru da gogewa da za su amfani bangarorin noman su. Ya jaddada cewa noma ita ce ginshikin tattalin arzikin Jigawa.

“A shekarar 2023, Jigawa na noman kadada 60,000 zuwa 70,000 na shinkafa. Amma a 2024, mun kai sama da kadada 200,000, kuma bana muna fatan kaiwa kadada 300,000. Burinmu shi ne mu samar da kashi 50 cikin dari na shinkafar da Najeriya ke bukata nan da 2030,” in ji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa jihar na mai da hankali kan noman rani domin rage illar sauyin yanayi. “Muna gyara madatsun ruwa 10 da ke jihar, wanda hakan ke kara fiye da kadada 4,500 ga filayen noma,” In ji shi.

Don kara yawan amfanin gona, gwamnatin jihar ta samar da sababbin taraktoci 300 da  kayayyakin aikin su, injinan girbi 60, injinan shuka 150, da sauran kayan noma na zamani. Kowacce cikin mazabu 30 a jihar tana da akalla taraktoci 10 da ake ba manoma kananan haya a farashi rahusa rahusa.

Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa Jigawa za ta ci gaba da zuba jari a harkokin noma na zamani don karfafa sashen shinkafa, tare da bai wa Liberia goyon baya a yunkurinta na cimma wadatar shinkafa a cikin gida.

 

Usman Muhammad Zaria 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa
  • NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya
  • Gwamna Radda ya miƙa wa mataimakinsa ragamar mulkin Katsina
  • NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya
  • Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina
  • Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya
  • Farfado Da Karkarar Sin: Canjin Gaisuwa Daga “Shin Ka Ci Abinci?” Zuwa “Yaya Rayuwarka A Gari?”
  • Jihar Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Liberia Don Inganta Noman Shinkafa
  • Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno