Leadership News Hausa:
2025-09-17@20:30:18 GMT

Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

Published: 14th, September 2025 GMT

Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan  ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1.

Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Ɗhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaye saboda Leɓerkusen ta rasa manyan ƴan  wasa da yawa.

Sai dai tuni ƙungiyar ta sanar cewa Ɗhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland. Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan  wasansa tare da cewa ba su da kuzarin da ya kamata duk da cewa shi da tawagarsa ne suka jagoranci tawagar.

Bugu da ƙari an zargi Ten Hag da rashin kwarjinin da ake koci ke buƙata domin jan ragamar babbar ƙungiya, musamman ma ƙungiyar da ta kawo sabbin ƴan  wasa da dama.

Za a iya cewa da alama ya riƙa shan wahala wajen shawo kan ƴan  wasa su bi tsarinsa, domin wasu majiyoyi sun ce bai iya yi wa ƴan  wasa wata ƙwaƙƙwarar huɗuba gabanin buga wasa. Sannan an bayyana cewa bai yi wa ƴan  wasan jawabi ba gabanin karawarsu ta farko da Hoffenheim. Akasin Alonso, wanda aka ce shi ya riƙa ƙarin ganin ya ƙara ƙwarewa a harshen Jamusanci tare da samun ƙarin gogewa lokacin da yake jagorantar ƙungiyar ta Leɓerkusen.

Abin ya ba da mamaki sosai yadda shugabannin Leɓerkusen suka yanke shawarar korar Ten Hag da wurwuri haka domin wannan ba abu ne mai alfanu ba ga daraktan wasanni na ƙungiyar Simon Rolfes – wanda ya dage kan a ɗauki Ten Hag a lokacin da ƙungiyar ke son ɗaukar sabon koci a watan Mayu – har ma da shugaban ƙungiyar Fernando Carro.

A ƴan  shekarun da suka gabata Ten Hag ya kasance ƙwararren mai horaswa lokacin da ya samu nasara sosai a Ajaɗ. Ya lashe gasar Holland sau uku sannan ya kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League a shekara ta 2019.

Ko a shekarar farko na jagorancin Manchester United aikinsa ya yi kyau babu laifi, kuma an alaƙanta barin aikinsa daga ƙungiyar kan rikicin da ƙungiyar ta fuskanta amma ba domin gazawarsa a matsayin mai horaswa ba. Amma a yanzu Leɓerkusen da alama tana cikin ruɗani. Kusan za a iya cewa a shirye suke su sayer da duk wani ɗan wasa da ya nuna aniyar barin ƙungiyar. A lokaci guda kuma ƴan  wasa irin su Malik Tillman da Jarell Ƙuansah sun tafi ƙungiyar tare da sa ran cewa Ten Hag ne zai ci gaba da horaswa.

A yanzu Leɓerkusen na buƙatar nemo wanda zai maye gurbinsa. Akwai rahotannin cewa sun tattauna da tsohon kocin Barcelona Ɗaɓi, haka nan kuma tsohon mai horas da Dortmund da Leipzig Marco Rose na cikin waɗanda ake ganin za su iya samun aikin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: ƙungiyar ta

এছাড়াও পড়ুন:

Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
  • Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana
  • Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba