An Bude Bikin Nune-Nune Na Masana’antar Manyan Bayanai Ta Big Data A Kudu Maso Yammacin Sin
Published: 29th, August 2025 GMT
A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare.
Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen hada bayanai da fasahar kirkirarraiyar basira ta AI. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900. A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna.
Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma ya kasance na biyu a duniya.
Masu zuba jari na waje suna kara zuba jari a Sin saboda babbar kasuwa. A halin yanzu, Sin ta zama abokiyar ciniki ta uku mafi girma a kasashe da yankuna 157, kuma ita ce kasa ta farko a fannin cinikin kayayyaki da ta biyu a fannin cinikin ba da hidima a duniya. A gun bikin na wannan shekara, Sin ta sanar da matakai da yawa, ciki har da “hanzarta aikin gwaji a yankunan gwajin ciniki cikin ’yanci da kuma yankunan ba da misali kan ayyukan ba da hidima na kasa” da “gaggauta bude kasuwar hada-hadar ba da hidima”. Wannan ya samu karbuwa sosai a wajen kamfanonin kasashen waje.
Ta hanyar tarurrukan baje kolin, duniya ba kawai ta ga sabbin abubuwa na tattalin arzikin Sin ba, har ma ta fahimci azamar Sin na hadin gwiwa da duniya da gina tattalin arzikin duniya mai bude kofa cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp