Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa
Published: 30th, August 2025 GMT
Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan.
Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye.
Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu ne shiryayye da Allah SWT.
Saboda haka, wannan ilhama ta tsotsar nono; tana daukewa a tsakanin watanni sha biyu (12), lokacin da ake shirye-shiryen yaye yaro daga shayarwa.
Har wa yau, bayan ilhamar tsotsa da ake kira a turance ‘Sucking refled’, akwai kuma wata ilhamar da ake kira da ‘Rooting refled’, ita kuma wannan ilhamar tana taimaka wa jarirai, su iya lalubo kan nonon mahaifiyarsu, ko da kuwa idonsu a rufe yake ko kuma a cikin duhu.
Bugu da kari, akwai kuma ilhamar hadiya, wato ‘Swallowing reflex’, bayan an tsotsi nonon; ana kuma bukatar a hadiye shi.
Don haka, ta kan wadannan ilhamomi guda uku ne da Ubangiji ya yi wa jarirai suke iya lalubo nonon mahaifiyarsu, sannan su tsotsa; har kuma su hadiye ba tare da wani mahaluki ya koya musu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp