Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu Bayan Yakin Gaza
Published: 15th, August 2025 GMT
An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da suka kashe kansu tun farkon wannan shekara zuwa 18, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka bayyana.
Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: Rundunar sojin ta bude bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa jami’in da ya kashe kansa yana shiyya ta 99 da ke yaki a zirin Gaza.
Jaridar Yedioth Ahronoth ya watsa rahoton cewa: Jami’in dan shekaru 28 ya shiga yakin da ake yi a zirin Gaza ne a makonnin da suka gabata.
Wani bincike da sojojin mamayar Isra’ila suka gudanar, wanda aka buga sakamakonsa a ranar 3 ga watan Agusta, ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka kashe kansu a cikin dakarunta, sun faru ne sakamakon yanayin fada a zirin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Mali Ta Bankado Wata Makarkashiyar Janyo Hargitsi A Kasar Tare Da Wargaza Shi August 15, 2025 Iran: Suna Bukatar Kawo Karshen Makaman Nukiliya Da Kuma Furuci Maras Daɗin Ji August 15, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen Ya Ce; Yahudawan Sahayoniyya Suna Yakar Al’ummar Falasdinu Duka Ne August 15, 2025 Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Hana Shigar Da Kayayyakin Jin Kai Yankin Gaza August 15, 2025 Laifukan Cin Zarafi Musamman Kisha Kiyashi A Kasar Siyasa Ya Doshi Laifukan Yaki August 15, 2025 Kungiyar Ba Da Agaji Ta Sanar Da Yadda Cutar Kwalara Take Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan August 15, 2025 Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a) August 14, 2025 Sayyid Huthi Ya Yi gargadi Yiyuwar Tarwatsewar kasashen yankin idan HKI Ta Tabbaga Shirinta August 14, 2025 An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London August 14, 2025 Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar August 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Suna Bukatar Kawo Karshen Makaman Nukiliya Da Kuma Furuci Maras Daɗin Ji
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da aka kai kasar Japan. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto wasu bayanai daga cikin sanarwar da masu rajin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan bikin cika shekaru 80 da hare-haren nukiliyar da Amurka ta kai a garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan.
Hare-haren nukiliya na Amurka, wanda ya kashe mutane 150,000 a Hiroshima da 80,000 a Nagasaki, ba wani bangare ne na yaki da ta’addanci ba, kawai farar hula aka tunkara a lokacin yakin duniya na biyu. Wannan ya haɗa da farfagandar wariyar al’umma da ke nuna Jafananci a matsayin mugayen mutane da ƙasƙanta su […] Bayan shekaru 80 da suka gabata, Amurka ba ta nemi afuwa a hukumance ba, ko kuma ta dauki alhakin mummunan sakamako da kuma mummunan laifin amfani da makaman nukiliya a kan fararen hular kasar Japan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen Ya Ce; Yahudawan Sahayoniyya Suna Yakar Al’ummar Falasdinu Duka Ne August 15, 2025 Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Hana Shigar Da Kayayyakin Jin Kai Yankin Gaza August 15, 2025 Laifukan Cin Zarafi Musamman Kisha Kiyashi A Kasar Siyasa Ya Doshi Laifukan Yaki August 15, 2025 Kungiyar Ba Da Agaji Ta Sanar Da Yadda Cutar Kwalara Take Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan August 15, 2025 Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a) August 14, 2025 Sayyid Huthi Ya Yi gargadi Yiyuwar Tarwatsewar kasashen yankin idan HKI Ta Tabbaga Shirinta August 14, 2025 An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London August 14, 2025 Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar August 14, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’ August 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’ August 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci