’Yan majalisar kasar Mexico sun yi naushe-naushe a zauren majalisa
Published: 28th, August 2025 GMT
’Yan Majalisar Dattawan kasar Mexico sun yi naushe-naushe a ranar Laraba lokacin da muhawara ta yi zafi a zauren majalisar.
Rahotanni sun ce an fara ba hammatar iska ne bayan shugabannin ’yan adawa a majalisar sun bukaci sojojin Amurka su shiga kasar su taya su yaki da dillalan miyagun kwayoyi.
Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makareShugaban marasa rinjaye a makalisar, Alejandro Moreno, shi ne dai ya je wajen yin jawabi a fusace bayan kammala zaman majalisar, inda ya tunkari shugaban majalisar, Gerardo Fernandez Norona, saboda hana shi damar yin Magana.
A cikin wani bidiyo a kafafen sada zumunta dai, an ga Alejandro yana tutture shugaban majalisar, yana dukansa a wuya, sannan ya bangaje wani wanda ya yi yunkurin shiga Tsakani a kasa.
Rikicin dai ya biyo bayan zargin da aka yi wa jam’iyya mai mulki da ta adawa cewa suna goyon bayan shigar da sojojin Amurka cikin kasar, zargin da dukkan jam’iyyun suka karyata.
Shugaban majalisar dai ya sha alwashin zai rubuta korafi a hukumance a kan dan majalisar da ya ci zarafin nasa, domin ya tabbatar da an hukunta shi t hanyar cire masa rigarsa ta kariya a matsayin dan majalisa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025
Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025
Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025