’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa
Published: 19th, August 2025 GMT
Wasu masu garkuwa da mutane sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa rabon kudin fansar mutanen da suka sace a Jihar Nasarawa.
Jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku da tsabar kudi Naira miliyan 6.9 daga motar ’yan bingidar bayan hatsarin motar a yankin Garaku, daura da wani shingen bincike na Jami’an Kula da Lafiyar Ababen Hawa (VIO)
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta ce ta kwato makamai masu haɗari da kuɗi sama da naira miliyan shida, bayan wani haɗari da ya faru a kusa da Angwan Mayo.
’Yan sanda daga yankin Garaku sun ce da misalin ƙarfe 9:08 na safe, suka samu kiran gaggawa dangane da haɗarin motar kirar Opel Vectra wadda shaidu suka ce mutane biyu da ke cikinta sun tsere.
Mutane 62 da aka sace sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Katsina Albashin sanatoci 109 zai biya farfesoshi 4,709Da isar jami’an wurin, sun tarar da taron jama’a, inda wani jami’in VIO ya mika bindigogin da kuma kudi Naira miliyan 6.9 da aka samo daga cikin motar.
Daga nan ’yan sanda da haɗin gwiwar sojoji shiga farautar waɗanda suka tsere, inda suka yi nasarar ɗaya daga cikinsu mazaunin yakin Barkin Ladi a Jihar Filato, bayan ya tsere zuwa daji.
Wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane guda bakwai, waɗanda suka sace wani lauya a yankin Nyanya, Abuja.
Ya bayyana cewa shi da abokinsa suna kan hanyarsu ta zuwa Jos domin rabon kuɗin fansa da suka karɓa kafin haɗarin ya faru.
An mika shi tare da abubuwan da aka kwato zuwa Sashen Binciken Laifuka na Jihar da ke Lafia, kamar yadda Kwamishinan ’Yan Sanda CP Shettima Jauro Mohammed ya umarta.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya yaba da wayar da kan jama’a, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da laifuka a jihar da kewaye.
Ya kuma roƙe su da su ci gaba da ba da goyon baya ga ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.
“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA