Hamas ta bayyana muhimman bukatunta a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
Published: 8th, October 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana manyan sharudan ta a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta bayyana cewa tana kokarin shawo kan duk wani cikas domin cimma yarjejeniyar da ta dace da muradun al’ummar zirin Gaza.
Kakakin kungiyar Fawzi Barhoum ne ya bayyana hakan a daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa a Masar kan shirin tsagaita bude wuta da shugaban Amurka ya gabatar da nufin kawo karshen yakin Gaza.
Ya bayyana cewa, bukatun Hamas sun hada da tsagaita bude wuta na dindindin, da janyewar Isra’ila gaba daya daga Gaza, da shigar da kayayyakin jin kai da na agaji ba tare da sharadi ba, da mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu, da kuma yarjejeniyar musayar fursunoni ta gaskiya.
M. Barhoum ya zargi fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da neman dakile zagayen tattaunawar da ake yi a halin yanzu, kamar yadda ya yi a baya.
A ranar 6 ga watan Oktoba ne tawagogin Isra’ila da Hamas suka fara tattaunawa a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh a Masar kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na Gaza.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan shirin Trump na Gaza mai daftarori guda 20, shirin da gwamnatin Tel Aviv ta amince yayin da ita kuma Hamas ta amince da wani bangare.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta yi gargadi game da katsalandan na EU akan tsibiran tekun Fasha October 8, 2025 Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da tattauwanar da ake a Masar October 8, 2025 Gaza : Spain na son gurfanar da Isra’ila gaban ICC kan cin zarafin masu fafutukar kai agaji October 8, 2025 Faransa : Ana ci gaba da kira ga Macron ya yi murabus October 8, 2025 Dubban Mutanen Moroko Sun Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa October 7, 2025 Kamfanin Jirgin Sama Na “Oman Air” Ya Maye Gurbin Isra’ila Da Falasdinu A Cikin Taswirarsa October 7, 2025 MDD Ta Yi Maraba Da Hukunta Mai Laifi Na Farko A Yankin Darfur Da Kotun Duniya Ta Yi October 7, 2025 Golpayagni: Jagoran Juyi Ne Ke Rike Da Tutar Gwagwarmayar Fada Da Azzalumai A Duniya October 7, 2025 Vatican:Duniya Ta Gaza Wajen Kasa Dakatar Da Isa’ila Kisan Kare Dangi A Gaza October 7, 2025 Kwamitin kula Da Yan Gudun Hijira Na Mdd Ya Jinjinawa Iran kan Afghanistan. October 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha
Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa jiragen yakin kasar Rasha samfurin Mig 31 da Su 25 keta sararin samaniyar kasashensu.
Firay ministan kasar Poland Donal Tusk ya ce kasarsa a shirye take ta kakkabo duk wani abu da ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.
A taron majalisar don tattauna wannan batun dai wakilai 469 sun amince da bukatar a yayinda wasu 97 suka ki amincewa, sai kuma 38 wadanda suka ki kada kuri’unsu.
Jiragen yakin kasar Rasha masu tsananin sauri sun keta sararin samaniyar kasashen Poland, Estonia, Latvia, Lithuania, da kuma Romania. Sannan jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar ta Rasha sun keta sararin samaniyar kasashen Denmark, Sweden, and Norway.
Labarin yace jiragen yakin Rasha samfurin MiG-31 guda uku sun keta sararin samaniyar kasar Estonia a ranar 19 gawatan satumban da ya gabata, sannan an gawa wani jirgin Rasha yana shawagi kan kamfanin manfetur da gasa mai suna ‘ Petrobaltic oil and gas platform a kasar Poland ba tare da izini ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci