Iran ta yi gargadi game da katsalandan na EU akan tsibiran tekun Fasha
Published: 8th, October 2025 GMT
Iran ta yi watsi da sanarwar hadin gwiwa da kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf (GCC) da EU suka fitar tare da jaddada ikonta a kan tsibiran tekun Fasha nan guda uku: Greater Tonb, Lesser Tonb, da Abu Musa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya yi Allah wadai da tsoma bakin kasashen turai kan lamarin.
M.Baghai ya yi watsi da shishigin na kasashen turan da ya danganta da marar tushe da aka yi a cikin sanarwar hadin gwiwa na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin Gulf na Farisa (GCC) da kungiyar Tarayyar Turai, wanda ya ce wabi yunkuri na haifar da rarrabuwar kawuna da wasu kasashen Turai ke yi a yankin Gulf na Farisa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sake tabbatar da ikon mallakar tsibirin na dindindin, yana mai jaddada cewa wani bangare ne na kasar Iran.
Tsibirin Abu Musa, Greater Tonb, da Lesser Tonb, dake cikin Tekun Fasha, a tarihi sun kasance wani yanki na kasar Iran, kamar yadda bayanai na tarihi, na shari’a, suka tabbatar a Iran da sauran wurare.
Tsibiran sun kasance karkashin ikon Birtaniya a shekara ta 1921, amma a ranar 30 ga Nuwamba, 1971, kwana guda bayan ficewar sojojin Birtaniya daga yankin, kuma kwanaki biyu kafin Hadaddiyar Daular Larabawa ta zama kasa, Iran ta karbi ikon mallakar tsibirin.
Jami’in diflomasiyyar na Iran ya shawarci makwabtan da ke gabar tekun kudancin tekun Fasha da su mai da hankali kan karfafa zumunci a tsakanin kasashen yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da tattauwanar da ake a Masar October 8, 2025 Gaza : Spain na son gurfanar da Isra’ila gaban ICC kan cin zarafin masu fafutukar kai agaji October 8, 2025 Faransa : Ana ci gaba da kira ga Macron ya yi murabus October 8, 2025 Dubban Mutanen Moroko Sun Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa October 7, 2025 Kamfanin Jirgin Sama Na “Oman Air” Ya Maye Gurbin Isra’ila Da Falasdinu A Cikin Taswirarsa October 7, 2025 MDD Ta Yi Maraba Da Hukunta Mai Laifi Na Farko A Yankin Darfur Da Kotun Duniya Ta Yi October 7, 2025 Golpayagni: Jagoran Juyi Ne Ke Rike Da Tutar Gwagwarmayar Fada Da Azzalumai A Duniya October 7, 2025 Vatican:Duniya Ta Gaza Wajen Kasa Dakatar Da Isa’ila Kisan Kare Dangi A Gaza October 7, 2025 Kwamitin kula Da Yan Gudun Hijira Na Mdd Ya Jinjinawa Iran kan Afghanistan. October 7, 2025 Wani Mai Rajin Kare Hakkin Dan Adam A Spain Ya Yi Tir Da Isra’ila October 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik.
A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan dangantaka mai tsawo da ke tsakanin Iran da Pakisatan, da kuma bukatar a kara zurfafata.
Sharif a nasa bangaren ya bayyana cewa nan ba da dadewa waministan harkokin wajen kasar Mohammad Ishak Dar zai ziyarci Tehran inda ake saran zai rattaba hannu kan yarjeniyoyi na bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, daga ciki har da batun kammala aikin shimfida bututun gas daga kasar Iran zuwa Pakistan. Da kuma harkokin sadarwa.
A cikin wannan shekarar ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjeniyar bunkasa kasuwanci ta dalar Amurka billion 10 a tsakaninsu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci