Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Published: 8th, October 2025 GMT
Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce da ta’addanci ya yi wa illa. Ya ce kungiyar ETIM wadda kwamitin sulhu na MDD ya ayyana a matsayin ta ta’addanci, ta taba tada rikice-rikicen ta’addanci da dama a cikin kasar Sin, kana ta gudanar da ayyukanta a kasar Syria, da Afghanistan da sauransu. Ya jaddada cewa, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da su dauki matakai don yaki da kungiyoyin ta’addanci ciki har da kungiyar ETIM.
এছাড়াও পড়ুন:
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza.
A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako.
Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya.
Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila.
Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya taka muhimmiyar rawa a sulhun, yake ziyara a ƙasar Isra’ilan a safiyar Litinin.
Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — AtikuWannan na zuwa ne bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da ɓangarorin biyu suka sanya hannu a kai a baya-bayan nan.
A bangare guda kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako, a matsayin ɓangarenta na musayar fursunonin yaƙin.
Ma’aikatar Harkokin Gida ta Isara’ila ta fitar da jerin sunayen mutanen da aka saki da shekarunsu:
Eitan Abraham Mor, 25 Gali Berman, 28 Ziv Berman, 28 Omri Miran, 48 Alon Ohel, 24 Guy Gilboa-Dalal, 24 Matan Angrest, 22Na gaba ake da ran muka su ga iyalansu a wani sansanin soji a Kudancin Isra’ila.
A ɗaya bangaren kuma kungiyar kula da Fursunoni ta Palastinu ta fitar da jerin sunayen mutane 1,718 da Isra’ila za ta sako.