Kungiyar Tuntuba Ta Arewa Ta Yi Kira Ga Ƙarin Hakuri Da Tsari Yayinda Take Shirin Cika Shekaru 25
Published: 7th, October 2025 GMT
Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa, Alhaji Bashir M. Dalhatu, Wazirin Dutse, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ƙara haɓaka ɗa’a, bin ƙa’ida da ƙulla zumunci yayin da ƙungiyar ke shirin gudanar da bikin cika shekaru 25 da kafuwa a watan Nuwamba 2025.
Yayin jawabin sa a taron Kwamitin Amintattu da aka gudanar a ofishin ƙungiyar dake Kaduna, Alhaji Dalhatu ya jaddada muhimmancin zama masu daidaito da kulawa a cikin bayanan da jami’an ƙungiyar ke yi wa kafafen yaɗa labarai.
Ya bayyana cewa taron da ya samu halartar shugabanni da sakatarorin jihohi da mambobin ƙungiyar Arewa 100% Focus Group, zai tattauna kan batutuwa biyu — yadda jami’an ƙungiyar Tuntuba ta Arewa za su riƙa sadarwa da shirye-shiryen bikin cika shekaru 25.
A cewar sa, sabbin al’amura na rashin daidaito a cikin bayanan da wasu jami’an ƙungiyar ke fitarwa daga matakin ƙasa da jihohi sun sa dole a samar da cikakken tsari na sadarwa. Ya ce, “Kwamitin Amintattu yana da alhakin da kuma ikon tsara da aiwatar da irin waɗannan ƙa’idoji.” Ya ƙara da cewa an riga an kammala takardar da ta ƙunshi waɗannan ƙa’idojin ta hannun sakatariyar ƙungiyar.
Da yake kwatanta kundin tsarin mulkin ƙungiyar Tuntuba ta Arewa, Alhaji Dalhatu ya tunatar da mambobi cewa Kwamitin Amintattu yana da cikakken iko wajen bayar da shawara, jagoranci da fassarar doka kan dukkar harkokin da suka shafi manufofin ƙungiyar, kuma duk shawarar da kwamitin ya bayar tana da ƙarfi ta doka.
Dangane da bikin cika shekaru 25 da kafuwar ƙungiyar, ya bayyana cewa za a gudanar da bikin daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Nuwamba, tare da abubuwa uku da za su zama ginshiƙai — tattara kuɗaɗe domin gina sabuwar cibiyar ƙasa, ƙaddamar da Asusun Tallafi domin taimaka wa ayyukan ci gaban mata da matasa a Arewa, da kuma gabatar da jerin littattafai na musamman.
Ya yaba wa kwamitocin shirya bikin bisa jajircewa, tare da kira ga mambobi da su halarci taron a Kaduna cikin ƙarfi da yawa.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa ya kuma tunatar da mambobi cewa ƙungiyar ba ta da alaƙa da kowace jam’iyyar siyasa, musamman yayin da ake gab da zaɓen 2027. Ya ce, “Ko da yake mambobi na iya kasancewa a jam’iyyun siyasa daban-daban, ƙungiyar Tuntuba ta Arewa a matsayinta na ƙungiya ba za ta goyi bayan jam’iyya guda ba.”
Alhaji Dalhatu ya nuna damuwa kan yawaitar ƙirƙiro ƙungiyoyi masu kama da Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa a Arewacin Najeriya, yana mai cewa irin waɗannan ƙungiyoyi suna rage haɗin kai da ƙarfi. Ya tuna cewa Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa an kafa ta ne a shekarar 2000 daga manyan shugabannin Arewa ciki har da tsoffin shugabanni, gwamnoni, sarakuna da masana, domin haɗa ƙungiyoyi daban-daban ƙarƙashin inuwa ɗaya. “Wadanda ke ƙirƙirar ƙananan ƙungiyoyi su sake tunani su dawo cikin ƙungiyar Tuntuba ta Arewa — akwai isasshen wuri ga kowa,” in ji shi.
Ya ƙarfafa shugabannin jihohi da su ƙara yawan mambobi tare da kafa rassan ƙananan hukumomi da haɗin gwiwar hedkwatar ƙasa.
Dangane da matsalar tsaro, Wazirin Dutse ya yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen yaƙar ta’addanci da ‘yan fashi, tare da addu’ar rahama ga waɗanda suka rasu.
Yayin da yake tsokaci kan rikicin da ya kunno kai a Dangote Refinery, Alhaji Dalhatu ya la’anci abinda ya kira “ƙungiyoyin marasa kishin ƙasa” da ke samun goyon bayan wasu ɓoye-ɓoyen mutane masu son durƙusar da masana’antar. Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa, yana mai cewa lamarin barazana ce ga tattalin arzikin ƙasa.
Ya kammala da gode wa mambobin ƙungiyar bisa halartar taron, ta zahiri da ta yanar gizo.
COV: Shettima Abdullahi
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Arewa Kungiyar Ƙarin Shekaru Tsari Yayinda
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa.
Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama.
A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin.
Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi.
Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake birnin Kano don yi masu aikin.
Wakilan shirin na kananan hukumomin Malam Madori and Kaugama, Malam Bashari Suleiman da Dan-Alhaji sun ce a mako mai zuwa ne za’a gudanar da aikin ga wadanda aka tantance.
Da yake jawabi a madadin wadanda zasu ci moriyar aikin, wakilan mazabun Garun-Gabas da Mairakumi, Mustapha Bala da Suraja Garba sun yabawa kokarin Alhaji Umar Jambola.
A nasu jawaban, Shugabannin kananan hukumomin Kaugama da Malam madori, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas da Alhaji Masaki Usman Dansule sun yaba da hobbasan Umar Jambola na taimakawa masu karamin karfi a kananan hukumominsu.
Usman Mohammed Zaria