Janar Pakpour: Duk wani shishigi a kan Iran zai fuskanci martani mai tsanani
Published: 6th, October 2025 GMT
Kwamandan dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya yi rangadi a sananonin sojin ruwa na kasa Iran da ke yankin Gulf, inda ya yi duba shirye-shiryen da suke yi na tunkarar kowace irin barazana daga waje a kan kasar.
Da yake jawabi ga sojojin ruwa na kasar ta Iran a yayin wannan rangadi, kwamandan na IRGC ya bayyana cewa, kamar yadda sojojin ruwa suka taka rawar gani wajen tunkarar shishigi na makiya a lokacin yakin kwanaki 12, har yanzu ma suna a cikin Shirin ko ta kwana domin mayar da martani da dukkan karfinsu a kan duk wani aikin wuc gona iri a kan kasar.
Janar Pakpour ya kuma duba hotuna na jiragen Ruwan yaki na Amurka da suke sintiri a cikin tekun Farisa, wanda sojojin Ruwan kasa Iran din suke dauka kai tsaye da wasu na’urori na musamman.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwan zaman dar-dar da Rashin tabbas a yankin, sakamakon barazanar da Isra’ila ke yi na sake shiga wani sabon yaki tare da Iran.
A ranar 2 ga watan Oktoba, ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya tabbatar da cikakken shirin kasar na kare ikonta da al’ummarta a dukkanin fadin iyakokinta.
Nasirzadeh ya bayyana cewa “Iran a shirye take ta kare kasarta ba tare da la’akari da la’akari da duk wani sintiri da kai komo na sojojin makiyanta a cikin tekun farisa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yancin Falasdinawa October 6, 2025 Babban mai shiga tsakanin na Hamas ya isa Masar domin tattaunawa da Isra’ila October 6, 2025 Rahoto: A cikin shekaru biyu Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a Gaza October 6, 2025 Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza October 6, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris October 5, 2025 Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya October 5, 2025 HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41 October 5, 2025 Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula October 5, 2025 Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London October 5, 2025 Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha
Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa jiragen yakin kasar Rasha samfurin Mig 31 da Su 25 keta sararin samaniyar kasashensu.
Firay ministan kasar Poland Donal Tusk ya ce kasarsa a shirye take ta kakkabo duk wani abu da ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.
A taron majalisar don tattauna wannan batun dai wakilai 469 sun amince da bukatar a yayinda wasu 97 suka ki amincewa, sai kuma 38 wadanda suka ki kada kuri’unsu.
Jiragen yakin kasar Rasha masu tsananin sauri sun keta sararin samaniyar kasashen Poland, Estonia, Latvia, Lithuania, da kuma Romania. Sannan jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar ta Rasha sun keta sararin samaniyar kasashen Denmark, Sweden, and Norway.
Labarin yace jiragen yakin Rasha samfurin MiG-31 guda uku sun keta sararin samaniyar kasar Estonia a ranar 19 gawatan satumban da ya gabata, sannan an gawa wani jirgin Rasha yana shawagi kan kamfanin manfetur da gasa mai suna ‘ Petrobaltic oil and gas platform a kasar Poland ba tare da izini ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci