Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista
Published: 6th, October 2025 GMT
Ministan Bunƙasa Harkokin Fasaha, Kimiyya da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji, ya bayyana cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar kammala karatun digiri ba.
Nayanin ministan ya yi daidai da binciken shekaru biyu da kafar yaɗa labarai ta PREMIUM TIMES ta gudanar, wanda ya gano cewa ba jami’ar ba ce ta ba shi takardun digirin da ya gabatar wa Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa ba lokacin tantance shi a matsayin minista.
Tun daga watan Yulin 2023 ne ake zargin cewa ministan da amfani da takardun karatu na bogi, bayan da Shugaba Tinubu ya saka sunansa cikin mutane 28 da ya miƙa wa Majalisar Dattawa domin tantancewa a matsayin ministoci daga jihohi 25, watanni biyu bayan rantsar da shugaban ƙasar a 29 ga Mayu, 2023.
Masu suka sun yi zargin cewa Mista Uche Nnaji bai kammala karatunsa a jami’a ba, kuma takardar digirinsa da ta yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ya gabatar wa hukumomi na bogi ne.
NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’ Tinubu ya fi damuwa da siyasa sama da rayukan ’yan Najeriya — ADCBayan tsawon lokaci bai ce uffan kan zargin ba, a ƙarshe ministan ya tabbatar da cewa Jami’ar UNN ba ta taɓa ba shi takardar kammala karatun digiri ba.
Maganar na gaban kotuBayanin ministan ya fito ne daga takardun shari’a da ya gabatar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya shigar da ƙara kan Ministan Ilimi da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da Jami’ar Najeriya (UNN) da Shugaban Jami’ar da Rajista da tsohon mukaddashin shugaban jami’ar, da Majalisar Jami’ar.
A cikin roƙonsa na wucin gadi, Mista Nnaji ya nemi kotu ba da umarnin hana jami’ar da jami’anta “tsoma baki” ko ci gaba da “tsoma baki” a kan bayanan karatunsa.
Haka kuma ya nemi a tilasta wa jami’ar ta saki takardar bayanin karatunsa (transcript), tare da roƙon a umarci Ministan Ilimi da Hukumar NUC su tilasta wa jami’ar ta miƙa masa takardar.
Haka kuma ya nemi umarnin wucin gadi da zai hana jami’ar da jami’anta canzawa ko lalata bayanan karatunsa kafin a kammala sauraren ƙarar.
A hukuncin da Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta yanke a ranar 22 ga Satumba 2025, kotu ta amince da wasu daga cikin roƙonsa amma ta ƙi bayar da umarnin hana aiki ga jami’ar. Daga nan aka ɗage sauraren ƙarar zuwa 6 ga Oktoba da muke ciki.
Wasu majiyoyi sun ce ministan ya shigar da ƙarar ne don hana Jami’ar UNN fitar da cikakken bayanin tarihin karatunsa, musamman ga PREMIUM TIMES, kuma yana son a sakar masa ‘transcript’ ɗin ne don “tuna inda ya tsaya” lokacin da ya daina karatu.
Abin da ya bayyanaA cikin takardar shaida mai sakin layi 34 da ya gabatar, Mista Nnaji ya bayyana cewa a shekarar 1981 Jami’ar UNN ta ɗauke shi a matsayin ɗalibi domin karatun Microbiology/Biochemistry, kuma ya “kammala” a 1985.
Sai dai a sakin layi na 13 ya bayyana cewa: “Ko da yake ban karɓi takardata daga jami’ar ba, saboda rashin haɗin kai daga shugabannin jami’ar, amma jami’ar ta rubuta wasiƙa ranar 21 Disamba 2023 ga People’s Gazette, inda ta tabbatar cewa na yi karatu a UNN kuma na kammala karatun digiri a shekarar 1985 da matakin ‘Lower Credit’.
Wannan wasiƙa, wacce Misis Rajista Celine Nnebedum ta sanya hannu, an aika ta ne a matsayin amsa ga tambayar People’s Gazette.
Amma daga baya Misis Nnebedum ta janye bayanin a wata wasiƙa da ta aika wa Hukumar Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a (PCC) a watan Mayu 2025, inda ta ce bayan binciken da aka yi cikin kundin masu kammala karatun digiri na shekarar 1985, ba a samu sunan Uche Nnaji ba.
Daga bisani Shugaban Jami’ar UNN, Farfesa Simon Ortuanya, ya tabbatar da hakan a wata wasiƙa da ya rubuta wa PREMIUM TIMES ranar 3 Oktoba 2025, yana cewa Mista Nnaji bai kammala karatunsa ba kuma jami’ar ba ta ba shi takardar shaidar digiri ba.
Wani babban jami’i na jami’ar ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa: “Ko dai an saye wasu ma’aikata a ofishin rajistara da wani dalili, ko kuma kuskure ne da gaske. Amma gaskiyar magana ita ce — bai taɓa kammala karatu a nan ba. Fayil ɗinsa yana nan, har zuwa a daidai inda ya tsaya.”
Ministan ya ƙi maganaDuk da yawan ƙoƙarin da PREMIUM TIMES ta yi don jin ta bakinsa, Minista Nnaji ya ƙi yin magana kai tsaye.
An kuma aika masa da cikakken tambaya a rubuce ranar 8 Janairu 2024, wacce ofishinsa ya tabbatar da karɓa ranar 18 Janairu 2024, amma bai ba da amsa ba.
Haka kuma bai amsa kiran waya da sakonnin tes da imel da aka tura masa ba.
Muhimman tambayoyiYardar ministan cewa jami’ar ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba ta haifar da tambaya cewa, idan jami’ar ba ta ba shi takardar digiri ba, ta yaya ya samu takardar da ya gabatar wa hukumomi? Kuma idan bai taɓa kammala digiri ba, ta yaya ya samu damar yin aikin NYSC?
Kafin tantance shi a matsayin minista a ranar 1 ga Agusta 2023, Mista Nnaji ya gabatar da kwafi 109 na bayanan kansa ga Majalisar Dattawa, inda ya bayyana kansa a matsayin: “Mai hangen nesa a fannin masana’antu, ƙwararren mai aikin mai da iskar gas, babban mai harkar gine-gine, ma’ikacin jinya, mai fafutuka wajen dimokuraɗiyya, kuja ƙwararren masanin muhalli.”
A shafi na uku na takardarsa, ya ce ya samu samu digiri a Biochemistry da Microbiology daga UNN, amma bai bayyana shekarar kammalawa ba. Ya kuma yi iƙirarin cewa ya yi aikin NYSC a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos a 1985, da kuma a Jos International Breweries a 1986.
Daga cikin takardun da ya gabatar akwai takardar WAEC, sanarwar shekaru, takardar dukiya ta Hukumar Kula da Ɗa’ar Ma’aikata (CCB) takardar biyan haraji ta 2022, da kuma takardun digiri da NYSC da ake tuhumar sa da cewa na bogi ne.
Yanzu da Mista Nnaji ya amince cewa Jami’ar UNN ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, tambayar ita ce, ta yaya ya samo takardun da ya gabatar wa hukumomi har aka tantance aka naɗa shi a matsayin minista?
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami ar UNN takardu Takardun bogi ba ta taɓa ba shi takardar kammala karatun digiri takardar digiri ba da ya gabatar wa Mista Nnaji ya shi a matsayin kammala karatu cewa Jami ar cewa jami ar Jami ar UNN ministan ya Ministan ya
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”.
Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa.
Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA