Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris
Published: 5th, October 2025 GMT
A ranar Talatar da ta shude ne dai aka ga gawar jakadan kasar Afirka Ta Kudu a kasar Faransa Nathi Matherhwa, da aka nuna cewa ya fado daga kan benen Hotel hawa na 22.
Babban sufeton ‘yan sanan kasar ta Afirka Ta Kudu Fenni Masemola ya sanar da aikewa da tawagar masu bincike su biyar da za su hada karfi da takwarorinsu na Faransa domin gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar jakadan.
A ranar Litinin din makon da ya shude ne dai matar jakadan ta sanar da cewa ya bace, lamarin da ya bude kofar bincike da ta kai ga ganin gawarsa a kasan Hotel din Hyatt Regency a ranar Talata.
Wani jami’in ‘yansanda Faransa ya fada wa manema labaru cewa; jakadan na Afirka Ta Kudu, ya aike wa da maidakinsa sako ta waya yana mai neman gafararta akan cewa zai kashe kansa.
Wasu rahotanni suna nuni da cewa a lokacin rayuwarsa a can kasar Afirka Ta Kudu, ya shiga cikin rikice-rikice masu yawa da su ka hada da hannu a kashe masu ma’aikatan hako ma’adanai 34 a lokacin da suke zanga-zanga a 2012.
Haka nan kuma an zarge shi da batutuwa masu alaka da cin hanci da rashawa, saboda kusancinsa da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya October 5, 2025 HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41 October 5, 2025 Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula October 5, 2025 Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London October 5, 2025 Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI October 5, 2025 Masar Ta Zargi Habasha Da karya Dokokin Kasa Da Kasa Kan Rikicin Madatsar Ruwan Kogin Nilu October 5, 2025 Shugaban Hamas Ya Bayyana A Fili Tun Bayan Harin Isra’ila A Kasar Qatar October 5, 2025 Dubban Mutane Ne Suka Yi Zanga -Zanga Nuna Adawa Da Isra’ila A Athens. October 5, 2025 The Guardian: Isra’ila ta azabtar da Greta Thunberg ‘yar kasar Sweden mai fafutuka October 5, 2025 Iran ta bukaci a haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na duniya October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha
Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa jiragen yakin kasar Rasha samfurin Mig 31 da Su 25 keta sararin samaniyar kasashensu.
Firay ministan kasar Poland Donal Tusk ya ce kasarsa a shirye take ta kakkabo duk wani abu da ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.
A taron majalisar don tattauna wannan batun dai wakilai 469 sun amince da bukatar a yayinda wasu 97 suka ki amincewa, sai kuma 38 wadanda suka ki kada kuri’unsu.
Jiragen yakin kasar Rasha masu tsananin sauri sun keta sararin samaniyar kasashen Poland, Estonia, Latvia, Lithuania, da kuma Romania. Sannan jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar ta Rasha sun keta sararin samaniyar kasashen Denmark, Sweden, and Norway.
Labarin yace jiragen yakin Rasha samfurin MiG-31 guda uku sun keta sararin samaniyar kasar Estonia a ranar 19 gawatan satumban da ya gabata, sannan an gawa wani jirgin Rasha yana shawagi kan kamfanin manfetur da gasa mai suna ‘ Petrobaltic oil and gas platform a kasar Poland ba tare da izini ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar October 10, 2025 Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci