Limami ya rasu a hannun ’yan sanda a Kano
Published: 28th, September 2025 GMT
Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda.
An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba.
2027: APC za ta ƙwace Kano ba tare da taimakon Kwankwaso ba – Jigon APC Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram safarar man fetur a BornoAn zarge shi da siyan buhun fulawa, wadda aka ce an sace a bara.
Mahaifinsa, Sheikh Adam Usman, ya bayyana cewa bidiyon na’urar CCTV ya nuna yadda jami’an ’yan sanda biyu suka yi wa ɗansa dukan tsiya a lokacin da suka zo su kama shi.
Ya ƙara da cewa an ci gaba da dukansa a ofishin ’yan sanda, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Sheikh Usman, ya ce wani abokin Salim ya bi jami’an zuwa ofishin ’yan sanda, sannan daga baya ya sanar da shi abin da ke faruwa.
Ya ce ya garzaya ofishin a daren da aka kama shi, amma aka hana shi ganin ɗansa, aka ce ya dawo washegari.
“Da na koma washegari, suka ce min ɗana ya yi rashin lafiya a daren da ya gabata aka kai shi asibiti. Amma daga baya na gano cewa tuni ya rasu.
“Da farko, an kai gawarsa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad a matsayin gawar ‘wanda ba a sani ba,’ amma aka ƙi karɓa.
“Sai aka kai shi Asibitin Ƙwararru na Abdullahi Wase, inda aka ajiye shi a ɗakin ajiye gawarwaki,” in ji mahaifin matashin limamin.
Ya cw tuni suka kai ƙara hukumar ’yan sanda, kuma an shaida musu cewa an kama wasu jami’ai bisa rashin ƙwarewa a aikinsu, ana kuma gudanar da bincike.
An bayar da gawar Salim a ranar 26 ga watan Satumba, domin a binne shi bayan kotu ta bayar da umarnin a yi gwaji a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Sakamakon gwajin zai fito cikin makonni huɗu.
Mutanen unguwar sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai sauƙin kai da son zaman lafiya, inda suka ce mutuwarsa ta jefa su cikin damuwa.
Ƙoƙarin samun jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Gawa zargi
এছাড়াও পড়ুন:
An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies.
Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci.
An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara baDokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci gaba ɗaya.
Indonesia na daga cikin ƙasashen da har yanzu ake cin naman karnuka da kyanwa, duk da cewa wasu birane sun daina wannan al’ada a ’yan shekarun nan.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun yaba da sabon matakin, suna mai cewa ya dace da manufofin kare lafiyar al’umma.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane da dama kan mutu da cutar rabies a kowace shekara a Indonesia, inda rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa mutane 25 suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris 2025.
Duk da cewa a yawancin yankunan Indonesia ana kallon karnuka a matsayin dabbobin da ba su da tsabta, wasu ƙananan ƙabilu na ci har yanzu, musamman ma saboda samun naman a farashi mai sauƙi.