Mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ta rasu
Published: 18th, August 2025 GMT
Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta rasu.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Filato, Shittu Bamaiyi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Lahadi.
Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato Adam A. Zango ya auri jarumar KannywoodA cewar Bamaiyi, Mama Lydia ta rasu ne da safiyar ranar Lahadi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos tana da shekaru 83.
Ya ce, rasuwarta babban rashi ne ba ga Shugaban APC kawai ba, har ma da iyalinsa da kuma jam’iyyar APC a Jihar Filato da Najeriya baki ɗaya.
Bamaiyi, ya bayyana Mama Lydia a matsayin mace mai tsantseni wajen ibada, jajirtacciyar shugabar mata a Cocin Christ in Nation.
Ya ce tare da mijinta marigayi Fasto Toma Goshewe Yilwatda sun yi ƙoƙari wajen bunƙasa coci a jihohin Borno, Yobe, Bauchi da Filato.
Ya ƙara da cewa Mama Lydia ta bar tarihi mai kyau ta hanyar gina ’ya’yanta da kuma hidimar da ta yi wa coci da al’umma.
Jam’iyyar ta yi addu’ar Ubangiji Ya jiƙan ta kuma ya bai wa Farfesa Yilwatda da iyalinsa haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mahaifiyar Shugaban Jam iyyar APC jam iyyar APC
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.
Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki.
Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,”
A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake kaiwa da komowa domin kare muradun al’ummar Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kammala aikin cikin lokaci. Ya bayyana cewa an umarci kamfanonin da ke aikin da su rika aiki sau biyu a rana domin hanzarta cigaba ba tare da rage inganci ba.
Ministan ya kara da cewa amfani da fasahar siminti mai ɗorewa wanda zai tabbatar da cewa titin zai dawwama tare da rage kudin gyara nan gaba.
Kamfanonin da ke aikin sun yi alkawarin ƙara gaggautawa musamman a yankin Jere dake jihar Kaduna, inda ake sa ido sosai kan ci gaban aiki. Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma tabbatar da ci gaba da haɗin kai da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya domin magance ƙalubalen da ke iya janyo tsaiko.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA