Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato
Published: 17th, August 2025 GMT
Wani jirgin ruwa ɗauke da mutum sama da 30 da kuma babura takwas, ya nutse a garin Kojiyo da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin yankin mai suna Nasiru Goronyo, ya ce jirgin ya yi hatsari ne a kogin garin bayan ya ɗauki mutane da kaya da suka fi ƙarfinsa.
Kano: NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ghari/Tsanyawa Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025)Ya ce: “Mutane 30 da jirgin ya ɗauka ba a ga ko ɗaya daga cikinsu ba tukuna.
“Sai dai an fitar da babur guda ɗaya daga cikin takwas da suka nutse, amma kayan da mutane duk sun ɓace.”
Ana jiran ƙarin bayani daga hukumomi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hatsari Jirgin ruwa Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.
Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.
“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.
RN