Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025)
Published: 17th, August 2025 GMT
Sarkin Zuru, Alhaji Mohammed Sani Sami Gomo II, ya rasu a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke birnin London bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 82.
A cewar majiyoyin danginsa, ana sa ran za a kawo gawarsa daga London zuwa Najeriya nan da gobe (Litinin), domin gudanar da jana’iza.
Marigayin ya bar mata hudu, ’ya’ya bakwai da jikoki biyu.
Daya daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a Zuru, Muhammed Abba Zuru, ya bayyana cewa iyalan marigayin na jiran isowar gawarsa daga London kafin a kammala shirye-shiryen jana’iza.
An haifi Mohammed Sani Sami a Zuru, Jihar Kebbi, a ranar 24 ga Oktoba, 1943. Ya shiga Rundunar Sojin Najeriya a ranar 10 ga Disamba, 1962, inda ya samu horo tare da Ibrahim Babangida.
Daga bisani ya halarci Mons Officer Cadet School da ke Aldershot, Ingila, inda ya zama hafsan soji a ranar 25 ga Yuli, 1963.
Ya halarci yakin basasa na Najeriya, kuma ya jagoranci dakarun da suka fatattaki sojojin Chadi da suka kutsa Jihar Borno.
A watan Yuli 1975, Janar Murtala Mohammed ya naɗa shi kwamandan Brigade of Guards a matsayin Lieutenant Colonel.
Bayan juyin mulkin 31 ga Disamba, 1983 wanda ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki, an naɗa Sani Sami a matsayin Gwamnan Soja na Jihar Bauchi.
Ya riƙe wannan muƙamin har zuwa watan Agusta 1985 lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya karɓi mulki daga hannun Buhari.
A lokacin mulkinsa a Bauchi, ya inganta cibiyoyin lafiya tare da kaddamar da babban shirin noma mai taken “Back to Land.”
Haka kuma ya jagoranci shirya gasar cin kofin duniya ta wasan handball a jihar.
A watan Oktoba 1984, lokacin da ake fuskantar ƙaruwa na matsalolin addini, Sani Sami ya jaddada haramcin wa’azin addini a fili.
Ya kuma bayyana cewa rushe wasu coci-coci domin gina sabon ring road ba ya nufin hari ne kan addinin Kirista, tare da ƙara da cewa gwamnati ta ware fili domin Katolika su gina sabon coci.
Ya yi ritaya daga rundunar soji a matsayin Manjo Janar a ranar 3 ga Satumba, 1990. A shekarar 1995, aka naɗa shi Sarkin Zuru na 11, mukamin da ya riƙe har zuwa rasuwarsa.
Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Alhaji Garba Umar-Dutsinmari, ya mika ta’aziyyar gwamnatin jihar ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zuru, al’ummar Zuru da Jihar Kebbi baki ɗaya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin da Aljannah Firdausi, tare da bai wa iyalansa haƙuri da juriyar rashin.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen jana’iza yayin da ake jiran isowar gawarsa daga London.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda ya miƙa wa mataimakinsa ragamar mulkin Katsina
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.
An zabi sabuwar firaminista a Luthuania Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INECA cewar Gwamna Radda, hutun zai ba shi damar samun kulawar likitoci da kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin koshin lafiya.
“Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi aiki cikin yanayi mai kyau, na ɗauki wannan matakin tafiya hutu, kuma zan dawo da zarar likitoci sun gama duba ni,” in ji gwamnan a cikin sanarwar.
A watan Yuli ne gwamnan ya gamu da hatsarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin jama’a.