Aminiya:
2025-08-17@17:11:16 GMT

Wani mutum yanke makazutarsa a Borno

Published: 17th, August 2025 GMT

An ceto wani mutum mai shekara 50 ya yi yunƙurin kashe kansa a garin Bama na Jihar Borno.

Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Juma’a a unguwar Hausari, inda al’ummar yankin ne suka kai masa ɗauki.

Shaidu sun ce mutumin ya daɓa wa kansa wuƙa har sau uku a ciki, kafin ya yanke mazakutarsa da wuƙar.

An ce ya aikata hakan ne saboda tsohuwar matarsa, daga garin Konduga, wadda ya yi wa saki uku, ta ƙi komawa gidansa.

Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025) Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau

’Yan sanda sun jagoranci tawagar ’yan sintiri zuwa wurin, inda suka gano tare da ƙwace wuƙar, sa’annan suka kwashi magidancin zuwa Babban Asibitin Bama, inda yake karɓar magani.

Majiyoyi sun ce an miƙa lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) da ke Maiduguri, domin ci gaba da bincike

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yanke mazakuta

এছাড়াও পড়ুন:

Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki

Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan tsawon watannin da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba.

Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni su kawo musu ɗauki cikin gaggawa.

Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood

Sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu saboda rashin tiransufoma, lamarin da ya jefa su cikin ƙunci da wahala.

Muhammad Idris Gargajiga, wanda ya yi magana da wakilinmu a madadin mazauna yankin, ya ce duk lokacin da suka kai ƙorafi sai a ce musu yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da suka kira da rashin adalci.

“Yawancinmu mun fito daga birnin Gombe muka koma zama a nan. Amma duk da haka ana tauye mana haƙƙoƙi, ana nuna mana kamar ba mu da cikakken matsayi a yankin,” in ji shi.

Al’ummar yankin sun ce rashin wuta ya haifar musu da tsaiko a harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumar Jos Electricity Distribution Company (JED), amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki
  • Mutum 612 sun rasa matsuguni sanadiyyar ambaliya a Potiskum — NEMA
  • ’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo
  • An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza
  • Ba mu da tabbas na ci gaba da rijistar kaɗa ƙuri’a a Borno – INEC
  • Mutum 12 sun rasu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a Kano
  • Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC
  • Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda
  • An kama Mai Unguwa kan yi wa yarinya fyaɗe a Gombe