Aminiya:
2025-08-17@19:15:53 GMT

Kano: NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ghari/Tsanyawa

Published: 17th, August 2025 GMT

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ɗan majalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari/Tsanyawa.

Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wasu ’yan siyasa sun yi maguɗi.

Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki APC ta lashe zaɓen cike gurbi a Zariya

Shugaban jam’iyyar na jihar, Kwamared Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya shaida wa ’yan jarida cewa INEC ta “tauye wa jama’a haƙƙinsu” bayan ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ya ce zaɓen ya kamata a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 10 da kotun ɗaukaka ƙara ta soke.

NNPP ta ce INEC ta ƙwace sakamakon da aka gudanar a rumfunan 10, tare da yin amfani da tsohon sakamakon da kotu ta riga ta soki.

“A Ghari, jama’a sun yi zaɓe lafiya a rumfunan 10, amma saboda maguɗi da wasu ’yan siyasa da jami’an INEC suka shirya, sai aka bayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya yi nasara,” in ji jam’iyyar.

NNPP ta kuma zargi INEC da bayyana sakamakon a hedikwatarta ta Kano maimakon a cibiyar tattara sakamako na mazaɓar, abin da ta ce ya bayar da damar tafka maguɗi.

Jam’iyyar ta yi alƙawarin ci gaba da ƙalubalantar abin da ta kira rashin adalci da nuna son kai.

Ta kuma ce sakamakon da jami’an rumfunan zaɓe suka sanya hannu a kai shi ne ya kamata a tabbatar da shi.

Sai dai NNPP ta yaba da zaɓen cike gurbi da aka yi a Shanono/Bagwai inda ɗan takararta ya yi nasara.

Jam’iyyar ta bayyana zaɓen a matsayin mai inganci, ta kuma gode wa jami’an tsaro da kuma jama’a da suka fito ƙwansu da kwarkwata suka kaɗa ƙuri’a.

“Muna girmama jarumtar jama’armu da suka tsaya tare da mu, suka kuma zaɓi ’yan takarar NNPP a dukkanin zaɓukan da aka gudanar,” in ji shugaban jam’iyyar.

INEC da APC ba su ce komai ba tukuna.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Zaɓen Cike Gurbi

এছাড়াও পড়ুন:

An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna.

Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya

Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.

Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu.

Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda.

A gefe guda kuma, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ra lamunci tashin hankali ko rikicin siyasa a Kano ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • APC ya lashe zaɓen cike gurbi a Zariya
  • APC ta lashe zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa a Kano
  • NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a Kano
  • APC ta nemi INEC ta soke zaɓen cike gurbin Kano
  • APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano
  • An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano
  • Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC
  • Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe
  • Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC