Jami’in Harkokin Shari’ar Kasa Da Kasa Na Iran Ya Yi Tofin Allah Tsine Kan Furucin Jami’ar Shari’ar Kasa Da Kasa
Published: 16th, August 2025 GMT
Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa ya mayar da martani ga son zuciya da wani jami’in kasa da kasa ke yi game da mamayar ‘yan sahayoniyya
Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya yi tsokaci game da kalaman mataimakiyar shugaban kotun kasa da kasa (ICJ) na goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila, yana mai cewa: “Wannan wani lamari ne mai ban mamaki da ya saba wa ka’idojin shari’a da kuma ka’idar rashin son kai na shari’a.
A wata sanarwa dayta fitar a dandalin X, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da harkokin kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya rubuta cewa: “Wannan wani lamari ne mai ban mamaki da ya saba wa ka’idojin shari’a. Mataimakiyar shugabar kotun kasa da kasa ta fito fili ta bayyana goyon bayanta ga hukumar Isra’ila, yar mamaya da ake ci gaba da gudanar da shari’a da dama a gaban kotu.”
Gharibabadi ya kara da cewa: Wannan ra’ayi na nuna son kai yana zubar da mutuncin kotun kasa da kasa da kuma saba ka’idar amincin shari’a da rashin son kai.
Ya kamata a lura cewa mataimakiyar shugabar kotun kasa da kasa (ICJ) ta Uganda Julia Sebutinde, ta bayyana cewa “Allah yana goyon bayanta, kan tsayawa tare da Isra’ila,” bisa la’akari da cewa “wannan alamun ƙarshen duniya ne da ya bayyana a Gabas ta Tsakiya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een August 16, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin Majalisar Dinkin Duniya August 16, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza August 16, 2025 Mataimakiyar Shugaban Kotun ICJ Ta Ce Tana Goyon Bayan HKI August 16, 2025 Burtaniya Zata Gurfanar Da mutane 60 Saboda Goyon Bayan Falasdinawa August 16, 2025 Qalibof: Dole Ne Musulmi Su Hada kai Don Matsin Lamba Ga HKI August 16, 2025 Aragchi: Yiyuwan Sake Shiga Yaki Da HKI Nan Kusa Yana Da Wuya August 16, 2025 Putin da Trump sun bayyana aniyarsu ta kawo karshen rashin jituwa da warware batun Ukraine August 16, 2025 Takht-Ravanchi: Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan hakkinta na nukiliya August 16, 2025 Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF August 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin shari a
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.
Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.
Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa bisa wannan babban rashi.
Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.