Kasashe 31 na duniya sun yi Allah wadai da kalaman fira ministan Isra’ila na shirin mamaye yankunan kasashe don kafa ‘Babbar kasar Isra’ila

Kalaman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbare kasar Isra’ila” ta janyo suka daga Larabawa da Musulunci.

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi 31, tare da manyan sakatarorin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kuma kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha, sun yi Allah wadai da kalaman Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbar Isra’ila”, tare da la’akari da furucin a matsayin rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma barazana kai tsaye ga tsaron kasashen Larabawa da ikon mallakar kasa, da tsaron yankin da kuma kasa da kasa.

Har ila yau, sun yi Allah wadai da amincewar da ministan Isra’ila Bezalel Smotrich ya yi na shirin samar da zaman lafiya a yankin E1 da kuma kalamansa na kin amincewa da kafa kasar Falasdinu.

Sun jaddada cewa, hakan ya zama babban cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da kuma kai hari kan ‘yancin al’ummar Falasdinu na kafa kasarsu mai cin gashin kanta a ranar 4 ga watan Yunin 1967, tare da kasancewan babban birninta Qudus.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’in Harkokin Shari’ar Kasa Da Kasa Na Iran Ya Yi Tofin Allah Tsine Kan Furucin Jami’ar Shari’ar Kasa Da Kasa August 16, 2025 Araqchi  Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een August 16, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin Majalisar Dinkin Duniya August 16, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza August 16, 2025 Mataimakiyar Shugaban Kotun ICJ Ta Ce Tana Goyon Bayan HKI August 16, 2025 Burtaniya Zata Gurfanar Da mutane 60 Saboda Goyon Bayan Falasdinawa August 16, 2025 Qalibof: Dole Ne Musulmi Su Hada kai Don Matsin Lamba Ga HKI August 16, 2025 Aragchi: Yiyuwan Sake Shiga Yaki Da HKI Nan Kusa Yana Da Wuya August 16, 2025 Putin da Trump sun bayyana aniyarsu ta kawo karshen rashin jituwa da warware batun Ukraine August 16, 2025 Takht-Ravanchi: Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan hakkinta na nukiliya August 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa Larabawa da

এছাড়াও পড়ুন:

Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka

Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje.

 

A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi.

 

Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga.

 

Idan ma Masar ta yi rashin nasara a wasan, za ta fatata da Guinea-Bissau a ranar Lahadi. Burkina Faso kuma wadda take kokarin zuwa ta biyu za ta buga wasa ne da kasar Saliyo, sai kuma kasar Habasha, amma tana bukatar samun nasara a wasannin kafin samun gurbin buga wasannin raba-gardama.

 

A rukunin (B) kuwa nasarar da Senegal ta samu a kan DR Congo ce ta ba ta damar darewa teburin rukunin, inda yanzu ta ba da tazarar maki daya. Tawagar ta Teranga Lions za ta je wasa da Sudan ta Kudu wadda ke karshen teburi, sai ta buga wasan karshe da Mauritania, inda take bukatar nasara biyu domin samun shiga gasar.

 

DR Congo dai na fatan Senegla ta yi rashin nasara, ita kuma ta samu nasara a wasannin biyu a gidan Togo da kuma Sudan a gida. Sudan na bukatar nasara a duka wasanninta, sannan Senegal ta yi rashin nasara wasanninta biyu domin samun gurbin zama ta daya a teburi, amma tana da damar zuwa ta biyu idan ta doke Congo.

 

A wannan rukunin kuma bayan hukuncin da FIFA ta dauka a kan kasar Afirka ta Kudu na cire mata maki uku saboda sanya dan wasan da bai cancanta ba a wasanta da kasar Lesotho.

 

Yanzu Benin ce kan gaba a rukunin, inda take saman Afirka ta Kudu da bambancin kwallaye, sai Nijeriya da Rwanda suke da maki da na hudu, amma duk suna da damar samun gurbi.

 

Benin na da wasa a gidan Rwanda da Nijeriya, sai tawagar Afirka ta Kudu za ta buga da Zimbabwe, sai Rwanda a gidanta. Nijeriya tana da wasa a gidan Lesotho sai Benin, kuma dole ne ta ci wasanninta guda biyu, amma ko da ta lashe wasannin, sai yadda ta wakana a sauran wasannin kafin sanin matsayarsa.

 

Nasarar da Cape Berde ta samu a kan Kamaru da ci daya mai ban haushi a watan jiya ta sa kasar ta kama hanyar kafa tarihin zuwa gasar cin Kofin Duniya na farko a tarihinta.

 

Yanzu kasar na bukatar nasara daya kacal a wasanta da Libya ko kuma a wasanta a gida da kasar da ke karshen teburi, wato tawagar ‘yan wasan kasar Eswatini. Kamaru za ta iya samun nasara da bambancin zura kwallaye idan ta doke Mauritus da Angola, ita kuma Cape Berde ta yi canjara a wasannin biyu, ko kuma idan Kamaru ta samu maki hudu a wasannin biyu,

 

ita kuma Cape Berde ta yi rashin nasara. Sai kuma Libya ce ta uku, kuma maki uku ne tsakaninta da Kamaru, kuma za ta iya bayar da mamaki.

 

Kasar Morocco ta riga ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniyar.

 

A cikin rukuni na E kuma kasashen Tanzania da Nijar da Zambia ne sauran kasashen da ke rukunin, kuma yanzu suna ta fafatawa ne domin samun gurbi na biyu wanda zai iya buga wasan raba-gardama.

 

A cikin rukuni na (F) kuwa, Ibory Coast na gaba da Gabon da maki daya bayan canjaras da ta yi da kasar Gabon a Francebille a watan Satumba. Kasar za ta je gidan Seychelles a ranar Juma’a, sai kuma ta fafata da Kenya a ranar Talata. Gabon za ta je gidan Gambia, sai kuma Burundi ta bakunce ta.

 

A cikin rukuni na G kuwa Algeria ita ma ta ba da tazarar maki hudu a saman teburi, kuma tana bukatar maki uku ne a wasanta da kasar Somalia wadda ta riga ta fita ko kuma ta biyu Uganda zai ta ba gurbi. Uganda ta zarce Mozambikue ne kawai da bambancin zura kwallo a matakin na biyu.

 

Can kuwa a cikin rukuni na H, Tunisia ta riga ta tsallake bayan samun gurbi duk da cewa akwai sauran wasaNNI biyu da za ta buga, inda ita kuma Namibia ta dage wajen neman zama ta biyu a rukunin. Namibia za ta je gidan Liberia a ranar Alhamis kafin ta karkare a birnin Tunis.

 

Daga rukuni na I kuma kasashe uku ne ke fafutikar samun gurbin na kai-tsaye, amma Ghana ce a sama da tazarar maki uku a saman Madagascar da Comoros. Ghana za ta samu gurbi idan ta yi nasara sannan Madagascar ta gaza samun maki uku. Wasan karshe na Ghana shi ne a gida da Comoros, ita kuma Madagacar za ta je gidan Mali a wasan na karshe.

 

Kamar yadda FIFA ta tsara, kasashe hudu da suka fi maki a cikin kasashen da suka kare a na biyu daga rukunoni tara din ne za su fafata wasannin raba-gardama a watan Nuwamba.

 

Zuwa yanzu dai kasashen Gabon da Madagascar da DR Congo da Burkina Faso ne a gaba a cikin tawagogi na biyu. Sakamakon za su iya canjawa bayan wasanni biyu na karshe, sannan kuma ba a riga an sanar da tsarin wasannin na raba-gardama ba.

 

Amma kasashen da suka samu nasara a wasannin na raba-gardama ne za su sake fafatawa a wasanin na raba-gardama da wasu kasashen na duniya kafin samun gurbi a gasar ta duniya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola October 12, 2025 Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
  • Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice  
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
  • An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Ka Tattauna Batun Falasdinu
  • An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan
  • Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta
  • Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar.
  • Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha