2025-10-13@20:21:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10144
«Farfesa Salim»:

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin October 13, 2025 Daga Birnin Sin Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba October 13, 2025 Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025
Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina. A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA October 13, 2025 Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025
A matsayin birnin dake karbar bakuncin taron, Dunhuang mazauni ne ga wurare 3 dake cikin jerin wuraren gargajiya na hukumar UNESCO da kuma wuraren kayayyakin gargajiya sama da 260, wanda kuma ke nuna hadaddun dabarun da aka dauka a shekarun baya-bayan nan da nufin kare al’adun gargajiya yayin da ake bunkasa birnin. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba October 13, 2025 Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin...
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa...
A yau litinin ne kungiyar Al-qassam brigades bangaren soji na kungiyar Hamas ta mika yahudawa guda 7 daga cikin guda 20 da ta kama su take rike da su ga hukumar kula da bada a gaji ta duniya a yankin Gaza Kungiyar hamas ta cika alkawarin da ta dauka na mika sauran mutane da take tsare da su domin nuna gaskiyar aniyarta na kulla yarjejeniyar zaman lafiya da tsaro a yankin Gaza, duk da yake cewa Isra’ila ta kafa tarihin cin amana da rashin cika alkawari kan duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakaninta da alummar falasdinu. Wannan shi ne zangon farko na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma bayan shiga tsakani da aka yi a sharma El-shaikh...
Shugaban kasar iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana a yau a wajen taron da yayi da gwamnoni jihohin kasar baki daya cewa jamhuriyar musulunci ta iran tana da karfin juriewa duk wata matsin lamba kuma ba zata taba risunawa duk wani nuna karfi ko cin zarafi ba. Yace kasa kamar iran mai makwabta 16 ba abu ne mai sauki a kakaba mata takunkumi ba, idan muka kara gyara dangantakarmu da makwabtanmu cin sauki zamu iya shawo kan matsin lambar da muke fuskanta, Har ila yau ya kara da cewa ba zasu sa ido kan iyakokin ko wacce kasa ba, amma zamu rufe ido kan duk kasar da ta nemi shiga harkokin kasar ba tare da bata lokaci ba, Iran tasha nanata...
Rahotanni sun bayyana cewa an gano daruruwan gawawwaki a karkashin burabutsai a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta tsakanin isra’ila da kuma kungiyar Hamas, adadai lokacin da tawagar agaji ke ci gaba da gano gawarwaki da suka makale a karkashin duwatsu bayan kwashen shekaru 2 Isra’ila na kisan kare dangi, Majiyar Asibiti a yankin Gaza ta sanar a yau litinin cewa akalla an gano gawarwakin mutane 323 da suke karkashin burabutsai, kuma har yanzu akwai gawarwarki sama da 10,000 da ke karkashin gine –gine da aka rusa a yankin Gaza. Bisa kidddigar da majalisar dinkin duniya ta gabatar ya nuna cewa an rusa gidaje 430,000 a yankin Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai...
Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya October 13, 2025 Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina October 12, 2025
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar. Don haka sun fara yajin aiki daga yau na gargadi na tsawon mako biyu. Ana ta bangaren Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmed, sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar...
Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA October 13, 2025 Labarai Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi October 13, 2025
Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da alkaluman dake nuna cewa, cikin watanni tara na farkon shekarar nan ta 2025, hada-hadar cinikayyar shige da fice ta hajojin kasar Sin, ta karu da kaso hudu bisa dari a mizanin shekara-shekara, inda darajarta ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 33.61 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.73. Hukumar ta ce ci gaban hada-hadar ya karu ne daga kaso 3.5 bisa dari da aka samu a watanni takwas na farkon shekarar ta bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya October 13, 2025 Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da...
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP. Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya. Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar. Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary...
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama. Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano. Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025 Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu. “A cikin sa’o’i 24 da...
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Jamhuriyar Kamaru da ake ci gaba da kirgawa ya nuna jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya samu gagarumin rinjaye a yankunan da a bayan Shugaba Paul Biya ya saba rinjaye. Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 yana fuskantar abokan hamayya 11 cikin har da tsofaffin mukarrabansa, da ma tsoffin ministocinsa da ke neman kujerarsa da ya shafe shekara 43 a kai kuma yake namen wa’adi na takswas. Cikinsu har da tsohon Ministan Yawon Bude Ido, Bello Bouba Maigari, da tsohon ministan Ayyuka, Bakary, wanda ya yi murabus a watan Yuli domin shiga takara kuma ya sama mafi shahara bayan doka ta haramta wa madugun adawa Maurice Kamto shiga zaben.. Biya ya ki yin tsokaci...
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano. Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22. Sauran wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren. Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano Ambaliyar Ruwa...
A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang. Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau. A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya...
Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka. Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin. Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Iragchi ya bayyana cewa yana ganin HKI ba zata mutunta yarjeniyar tsagaita wuta da ta cimma da kungiyar Hamas, yace bai amince da alkawalinHKI haka da kasashen yanna. Yace sune suka zama masu lamuni a tsagaita budewa junawuta a kasar Lebanon tsakanin Hizbullah da kuma HKI, amma manufarsu a tsagaita wuta ne kawai sai suka kyale HKI tana ci gaba kai hare- hare a kan kasar Lebanon ba tare da sun yimagana ba. Y a ce HKI ta ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon tun watan Nuwamban shekara ta 2024 har zuwa yanzu. Tana ci gaba da kashe mutanen kudancin kasar Lebanon, sun kuma hana mutanen yankin su sake gina wurarensu da suka...
A safiyar yau litinin ce majiyar gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ko kuma ministan harkokin wajen kasar ba zasu halarci taron sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin HKI da Falasdinawa a birnin Sharm sheikh na kasar masar ba. Saboda ba sa son haduwa da shuwagabannin kasashen yamma azzalumai wadanda da makaman sune aka kashe falasdinawa kimani 70,000 a gaza a cikin shekaru 2 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin na cewa shuwagabannin kasar Iran ba zasu amince su zauna kusa da wadanda suka kashe iraniyawa a cikin watan yunin da ya gabata, da kuma jinin mutanen da dama a yankin ba, suna mika masu hannu ba. A taron...
Shugaban kasar Amurka Donal Trunp ya isa HKI a safiyar yau Litinin, inda ake saran zai yi jawabi a majalisar dokokin HKI, kafin ya wuce zasu Sharm sheikh na kasar Masar inda zai halarci bikin sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da kuma HKI wanda aka fara aiki da shi a wannan makon. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto hotunan bidiyo kai tsaye daga Telaviv a lokacinda jirgin shugaban kasar ya sauka, sannan shuwagaban HKI da kuma firai ministan HK Benyamin Natanyahu ne suka tarbe shi a tashar jiragen sama na Bengerion. Shugaban ya iso HKI a dai dai lokacinda kungiyar Hamas ta mika fursinonin HKI 7 ga kungiyar Red Cross a zirin Gaza. Wanda daya...
Labaran da suke fitowa daga kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross ta fara karban fursinoni yahudawa daga hannun kungiyar Hamas kamar yadda aka tsara. Tashar talabijan ta Almayadeen ta bayyana cewa kungun fursinoni yahudawa masu rai 7 ne kungiyar ta Karba daga dakarun Hamas a yankin da ake kira Nitsarin a tsakiyar zirin gaza, da misalign karfe 8 na safe a yayinda gungu na biyu kuma wanda ya kunshi yahudawa 10 masu rai kungiyar Agajin ta karbesu a garin Khan Yunus dake areacin gaza da misalign karfe 10 na safe. Labarin ya kara da cewa an ga motocin bas -bas suna isa kurkukun da ake tsare da falasdinawa. Sannan ana saran yahudawan zasu...
Magu ayyukan ceto a gaza sun gano gawakin Falasdinawa fiye da 320 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun bayan fara yakin tufanul Aksa shekaru biyu da suka gabata Falasdinawa kimani fiye da 10,000 suka bace. Kuma a zatun mafi yawansu suna bisne a karkashin burbushi na gine-ginan da HKI ta rusa a kansu a zikin gaza. Asbitoci a gaza ya zuwa yansu sun bada sanarwan karban gawakin Falasdinawa 323 wadanda aka zakulo karkashin burbushin gine-gine. Da HKI ta rusa a kansu. Labarin ya kara da cewa a lissafin MDD ya zuwa tsagaita budewa juna wuta a gaza HKI ta rusa gidajen falasdinawa 430,000 a gaza. Banda haka akwai...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”. Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa. Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27...
An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a kusa da Goni Dunari a Karamar Hukumar Magumeri. Sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025 ta ce, “Dakarun mu sun yi gaggawar daukar matakin dakile barazanar bayan da suka ga yadda ’yan ta’addan suka kona gidaje tare da tsoratar da mutanen yankin.” Ya bayyana cewa sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne bayan sun shafe sa’o’i hudu suna...
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya. Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su...
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja. Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025. Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan...
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya. Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A...
A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza. A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako. Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya. Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila. Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
Gidajen mai da dam aka rufe, yayin da wadanda suka kasance da dan sauran mai kuma, layuka ne marasa iyaka suka makare su, lamarin da ta kai har kwana mutane ke yi a gidajen man. A kan titunan babban birnin kasar, bayanai sun ce ba kasafai ake ganin motoci suna kai komo ba, ko kuma mutane na tura babura, bisa alama dai mutane sun ajiye ababen hawansu a gida. Sai dai duk da wannan karancin man da ake fama da shi, farashinsa ya ci gaba da kasancewa a yanda yake, domin kuwa farashin lita na mai CFA 775 yayin da dizal yake akan CFA 725. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba. Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci muqaddashin jakadan kasar Oman a kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci babban jami’in ofishin jakadancin kasar Oman a birnin Tehran a jiya Lahadi, bayan wani rade-radin da ake yadawa cewa; Mutane biyu a kasar Oman sun mutu sakamakon shan ruwan ma’adinai da aka shigo da su daga kasar Iran. Bayan wasu zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na kasar Oman suka wallafa na alakanta mutuwar mutane biyu a masarautar Oman da shan ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, a ranar Lahadin da ta gabata ne Abdul Rasoul Shabibi, shugaban sashen ma’aikatar kula da tekun Farisa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gayyaci mai kula...
Kasar Yemen ta gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan fuskantar hare-hare masu zafi idan har ta karya yarjejeniyar Gaza A ranar Lahadin da ta gabata, Hazam al-Assad, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullahi ta Yemen, ya gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan karin fuskantar hare-hare masu zafi idan ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. A wata sanarwa da ya fitar ta hanyar gidan radiyo Sputnik ta kasar Rasha, Hazam al-Assad ya tabbatar da cewa: Yemen za ta dakatar da kai hare-hare kan gwamnatin mamayar Isra’ila, idan har ta yi aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza. Tun da farko dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da kungiyar Hamas sun rattaba hannu...
Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta. Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani. Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin...
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth October 12, 2025 Daga Birnin Sin An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje October 12, 2025 Daga Birnin Sin Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace October 12, 2025
Ya ce barazanar kakaba karin haraji ba hanya ce da ta dace ta hulda da Sin ba, yana mai nanata cewa, kasar Sin ba ta sauya matsayarta kan batun yakin cinikayya ba, wato ba ta son hakan, amma kuma ba ta tsoro. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje October 12, 2025 Daga Birnin Sin Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace October 12, 2025 Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
An wallafa wasu kundi 2 masu kunshe da ra’ayoyin shugaba Xi Jinping na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi mata da yara da kungiyar mata ta kasar, da kuma ra’ayoyinsa kan karfafa zumunci da akidu da al’adun iyali, cikin harsunan Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci, bayan irinsu da aka wallafa cikin harsunan Ingilishi. Madabba’ar tattara bayanai da fassara ta kwamitin tsakiyar JKS ce ta wallafa kundin, wadanda ake sa ran za su taimakawa masu karatu na kasa da kasa kara fahimtar ra’ayoyin shugaba Xi da dabaru da shawarwarin da Sin ta gabatar game da daukaka daidaiton jinsi da raya dukkan harkokin da suka shafi mata a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025 Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025. Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na...
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi:...
Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta. Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga kasashe fiye da 20. Manufar taron ita ce “kawo karshen yakin Gaza, da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar. A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar...
Yau Lahadi al’ummar Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar. Masu kada kuri’a miliyan takwas ne aka tantance domin kada kuri’a a zaben zagaye na farko da Shugaban kasar mai ci Paul Biya mai shekara 92 dake neman wa’adi na takwas. A cikin makonni biyu na yakin neman zaben, Shugaba Biya wanda aka dade ba a gan shi a bayyanar jama’a ba ya gudanar da gangami guda daya kacal, a garin Maroua dake yankin Arewa mai Nisa, daya daga cikin yankuna uku na arewa, inda ya sha alwashin magance matsalar tsaro da rashin aikin yi. A hukumance dai ‘yan takara goma sha biyu ne ke fafatawa a wannan zaben, amma biyu sun janye. Manyan masu kalubalantar Paul Biya guda...
Kotun daukaka kara ta Marseille ta tabbatar da soke dokar da ta bayar da umarnin rufe makarantar sakadare ta Musulinci da ke birnin Nice. A cikin wata sanarwa da ya fitar, lauyan makarantar, Sefen Guez Guez, ya yaba da nasarar ta uku a jere” tare da bayyana fatan cewa “za a daina tsananta wa wannan makaranta gaba daya. Takadammar data shafi makarantar ta hana da Rashin haske kan kudadenta, wanda hukumomjin yankin ke zargin makarantar da ta ina take samun kudadenta kamar yadda doka ta tanada. ” An bude makarantar ne a cikin shekarar 2016 a gundumar Ariane, kuma makarantar mai zaman kanta a halin yanzu tana da dalibai 130. Rahotanni sun ce makarantar, wadda wata kungiya ce mai alaka...
Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine. Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin...
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere. Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha. Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru. Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025 Daga Birnin Sin Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata October 11, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta October 11, 2025
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5. An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje. ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda. Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa. Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya...
Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe. A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi. Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB...
Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje. A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi. Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga. Idan ma...
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau? A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove) Yadda za a hada: Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya. Za a samu waraka da yardar Allah. Ciwon Sanyi Abubuwan bukata: Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda yadda za a hada: A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi. In sha Allah za a samu sauki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Dalilin...
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News. Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki. Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi birnin Rome na Ƙasar Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan sha’anin tsaro. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya ce za a fara taron ne a ranar 14 ga watan Oktoba, kuma zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar yankin Yammacin Afirka. ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Taron na ‘Aqaba Process’ an kafa shi ne a shekarar 2015 ta hannun Sarki Abdullah II na Ƙasar Jordan, kuma ana gudanar da shi tare da haɗin gwiwar Jordan da ƙasar Italiya. Taron na nufin tattauna hanyoyin yaƙi...
Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
Matar da ta daina ganin girman mijinta ta riga ta fara ruguza aurenta, da zarar kin yi masa maganganu na cin mutunci, kin yi kamar kin tozarta kanki da kanki ne, saboda girman mace a cikin aurenta yana da alaka da girman mijinta. 2. Rashin adalci tsakanin mijinki da danginsa Ki sani, mijinki zai iya jure miki a kuskuren da kike masa kai tsaye, amma zai dade yana daukar zafin abin da kika aikata wa iyayensa, ‘yan uwansa ko danginsa, wannan babban kuskure ne da mata da dama suke yi su kuma yi nadama daga baya. 3. Rashin Tausayi da Kulawa Ki sani, koda kuwa mijinki yana da kudi, yana bukatar jin tausayi daga gare ki. Idan ya dawo gida...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi wa Falasdinawa, amma ya kara da cewa HKI ba abar amincewa bace, don haka tana iya yaudara da kuma kawo karshen tsagaaita budewa junan wutar gaba daya. Abu ne da saba yi don haka Falasdinawa su yi hattara. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, Iran tana maraba da dukkan abinda zai kai ga kawo karshen kisan kiyashi a gaza, wanda ya dau shekaru 2 ana yi. Ministan ya jawo hankalin Hamas da sauran Falasdina kan amincewa da duk abin HKI...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Makaie ya tir da HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a kudancin kasar, Lebanon wanda ya sabawa da farko yarkeniyar tsagaita wutan da ta cimma da kungiyar Hizbulla a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Baghaei ya bayyana cewa ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon a kai a kai, da kuma shirun da kasashen duniya suka yi duk sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda HKI da wadanda suke riya daukar nauyin kola da cewa an dabbaka yarjeniyar MDD na kuduri mai lamba 1107. Ya zargi kasashen Faransa da kuna Amurka wadanda suka gabatar da kansu a matsayin masu lamuni don aiwatar...
A jiya Asabar ce aka gudanar da taron farkawar musulmi wanda aka saba gudanarwa a ko wace shekara don tattauna al-amuran kawancen kasashe masu gwagwarmaya da kuma kasashen musulmi a yankin da kuma sauran kasashen duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa taron wanda aka gudanar a dakin taron shahida Muhammad Addurrah a nan Tehran ya sami halattar baki daga cikin gida da kuma kasashen waje. Bakin dai sun hada da Nasser Abu Sharid wikilin kungiyar Jihadul Islami a nan Tehran, Mohammad Hassan Akhtari, shugaban kwamitin kwamitin goyon bayan juyin juya hali a kasar Falasdinu. Mehdi Shoushtari daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran. Da kuma wasu daga baki daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran. Nasser Abu...
Shugaban kasar Amurka Donal trump da shugaban kasar Masar Abdulfatta Assisi ne zasu jagoranci bikin rattaba hannu kann yarjeniyar Sulhu wacce ta kawo karshen yaki da kuma kissan kiyashin da HKI ta yi a Gaza na tsawon shekaru 2, daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa ranar Alhamis 8 ga watan Octoban shekara ta 2025. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews ya bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gutteres da shuwagabanin kungiyoyin kasashen Larabawa da Turai zasu halittu taron na gobe litinin a sharam Sheikh na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa za’a gudanar da taron ne a gobe litinin, bayan azahar kuma ana saran shuwagabannin kasashe fiye da 20. Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer,...
Kasar China ta maida martani kan kasar Donal Trump na kasar Amurka, wanda ya karawa kasar kudaden fito 100% na kayakin kasar da ke shigowa Amurka. SHafin yanar gizo na ArabNews ya nakalto kasar China a jiya Asabar tana cewa zata dauki matakan da suka dace kan Karin kudanen fito na 100% wanda shugaban Trump yayi. Kuma ta yi kira ga Trump kan cewa ya rungumi tattaunawa da kasar China ya fi masa kan barazana gareta. Ma’aikatar kasuwanci na kasar China ta bayyana cewa, basa son yakin kudaden fito amma basa tsoronta. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.” Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
An yi girgizar kasa mai karfin daraja 5.7 a ma’aunin Richter a kasar Habasha a jiya Asabar. Cibiyar dake kula da ilimin kasa ta kasar Jamus ta bayyana cewa, an yi girgizar kasar ne da zurfin kilo mita 10 a karkashin kasa. Girgizar kasar ta Jiya dai tana cikin jerin girgizar da aka yi ne a cikin kasar ta Habasha a lokuta mabanbanta a wannan shekarar. Sai dai kuma a wannan loakcin ana tsoron cewa za a iya fuskantar aman duwatsu a cikin yankunan da girgizar kasar ta afku. Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu an yi girgizar kasa har sau 29 a cikin kasar ta Habasha, da karfin wasu daga cikinsu ya wuce daraja 5. A ranar 3 ga...
Abubuwan da ake bukata: Semovita (kamar kofi 3-4), Yis (Babban Cokali da rabi, idan kuna so ya tashi sosai), Suga (Babban cokali 2), Gishiri ( rabin cokali), Man gyada ko buta (Babban Cokali 2), Ruwa mai dumi (kusan 1–1½ kofi, gwargwadon yadda Semon ya sha) Yadda za a hada: Za a samu roba sai a zuba Semobita, yis, Sikari da Gishiri a kwano, a juya su da kyau, sannan a zuba ruwa, a zuba ruwan dumi a hankali a cikin hadin, a na gaurayawa har sai ya koma kulli. Sai a zuba man gyada ko Bota a ciki, a ci gaba da murzawa har kullun ya yi laushi ba ya manne ba. Sannan sai a rufe rubar da leda...
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025 Wasanni Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025
Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017. Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021. Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995. Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki....
Rahotannin da su ke fitowa daga kasashen biyu sun ce a jiya Asabar an yi musayar wuta a tsakanin masu tsaron kan iyaka, bisa zargin da Islamabad take yi wa Kabul da taimakon kungiyoyi masu dauke da makamai. A can kasar Afghanistan kuwa majiyar tsaro ta ce ana yi fada da sojojin Pakistan akan iyakokin jahohi 7. Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce, sun kai wa sojojin Pakistan hari akan iyakar Diyorand a matsayin mayar da martanin ta sama da Pakistan ta kai wa birnin Kabul da jahohin Khust da Nangarhar. Pakistan tana zargin kungitar Taliban ta kasarta da kai hari daga cikin kasar Afghanistan,lamarin da Kabul take korewa. Harin da kungiyar Taliban din Pakistan a yankin Kahibar dake kan iyaka,...
Mahukuntan kasar Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa, ya zuwa yanzu ba a sami wani dalili na musabbabin mutuwar jakadan kasar Nathi Mthethwa A Afransa ba. Jami’an tsaron kasar Faransa suna aiki tare da takwarorinsu na kasar Afirka Ta Kudu da su ka isa kasar domin gano musabbabin mutuwar jakadan. An ga gawar jakadan na kasar na Afirka Ta Kudu a kasar Faransa,Mthethwa a Hotel din Hyatt Regency dake birnin Paris. Alamu sun nuna cewa ya bude kofar dakinsa dake hawa na 22 ya fado kasa, ba tare da wata alama dake nuni da cewa turo shi aka yi baa. Gabanin faruwar lamarin jakadan ya aike da sako na waya ga maidakinsa da a ciki ya bayyana mata shirinsa...
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki. Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki. Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,” A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba...
Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru. Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.” Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro. Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro...
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
Ta ce, “Dole ne akwai kalubale da dama, wanda daga cikinmu muke fuskanta a yayin shigowa wannan masana’anta, amma dai ni babu wani abu da zan iya tunawa, illa wani wanda na iske a masana’antar ya karbi zunzurutun kudi har Naira 50,000 a mabanbantan lokuta da sunan zai yi min rijista a masana’antar, kuma bai yi ba, daga karshe ma na gano cewa; kudin rijistar duka-duka Naira 5,000 ne. A wata hira da Khadija ta yi da gidan Rediyon Hikima, ta bayyana cewa, matukar ta samu abin da ya kawo ta masana’antar (Kudi), to nan da shekara daya ma; za ta iya shiga daga ciki, ma’ana za ta samu miji ta yi aurenta na Sunna. Khadija, wadda ta...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko. A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13. Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro DSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana. Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025 October 11, 2025 Daga Birnin Sin Tarihin Hassan Usman Katsina (1) October 11, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique October 11, 2025
Haka zalika, sun ki bayyana takamaiman wajen da za a daura auren, har sai bayan an kammala, inda suka bayyana yin hakan a matsayin wata hanya ta kawar da cece-kuce daga al’umma. Kazalika a ‘yan watannin da suka gabata kuma, an sake daura auren jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau tare da angonta Ibrahim Garba, a wani biki wanda za a iya kira da na sirri da aka gudanar a birnin Kaduna, daura auren shahararriyar jarumar Kannywood din, Rahma Sadau da mijinta Ibrahim Garba, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya yi matukar bai wa mutane mamaki, duba da cewa; kafin daurin auren babu wata alama ko sanarwa da aka fitar daga makusantan mijin ko matar. An yi...
Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar. Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya...
Ya ci gaba da bayanin cewa, “Da zan koma Kaduna sai ya ba ni takarda na kai wa Wazirin Katsina, Alhaji Isa Kaita. Na zo Kaduna na yi jarrabawa, bayan mun kare na koma gida ina sauraren sakamakon jarrabawar. Ba zan taba mantawa ba, ana zaune wajen Hawan Daba don tarbar Sarauniyar Ingila sai na sami telegiram mai cewa na ci jarrabawa ana nema na a Kaduna. “Na fadawa mahaifina. Muka kintsa muka bar Katsina sai Kaduna, daga Kaduna muka tafi Legas. Da isa ta Legas sai na ga abokan nawa da suka sami nasarar wannan tafiyar duk ‘yan Kudu ne. Ni kadai ne dan Arewa kuma Bahaushe cikin daga cikin mu takwas ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...
Rahotanni sun tabbatar da cewa bababn jami’in kungiyar Hamas Basen Naim yayi watsi da duk wani kokor nai ya yiyuwar sanya hannu tsohon fira ministan birtaniya Tony Blair a gwamnatin da za’a kafa a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta da aka yi a baya bayan nan. Har ila yau Basem ya kara da cewa kungiyar tana maraba da kokarin da shugaban Amurka Donal trump yake yi na kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ta kwashe shekaru 2 tana yi a yankin Gaza, sai dai sun yi gargadin cewa basa maraba da tony Blair game da taka wata rawa a sabuwar gwamnatin Gaza da za’a kafa bayan tsagaita wuta. Yace idan aka zo batun Blair kila mu...
A nasa tsokaci kuwa, sakataren gwamnatin Mozambique mai kula da ma’adinai Jorge Daudo, cewa ya yi lardin Shandong yana daya daga cikin larduna masu kwazo da ci gaban masana’antu a Sin, kuma yana da karfi a fannonin hakar ma’adinai, da sarrafa karafa da masana’antu. Sabo da haka, Mozambique na fatan kara yin hadin gwiwa da lardin na Shandong. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia October 11, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa October 11, 2025 Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila...
Shugaban kasar Cuba miguiel Diaz –canel yayi tir da matakin da kwamitin dake bada kyautar noble a duk shekara ya dauka na bada kyatutar ta wannan shekarar ta 2025 ga dan adawan kasar venuzela maria corina machado inda ya bayyana shi a matsayin abin ban kunya . Matakin na Diaz canel yana nuna irin yanayin zaman tankiya tsakanin gwamnatocin latin Amurka da kuma kasashen yamma , kuma yana nuna cewa rabuwar kawuna kan wanda aka amince shi a matsyin mai inganci a bangaren dimokuradiya kuma ya haifar da rashin zaman lafiya a yankin. Yana mai cewa babban abin kunya ne ace kyutar Nobel ta zaman lafiya a mika ta ga wadda ta janyo tsoma bakin sojoji a kasarta, Wannan yana...
Bayanan da suka fito daga kasar Indunusiya sun nuna cewa gwammnatin kasar ta ki bada visa ga tawagar wasan jiminastik din HKI da aka shirya za’a yi wasa a birnin Jakarta a wannan watan, domin nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin Gaza. Wannan matakin yana kara nuna irin yadda batun kisan kiyanshin gaza yayi tasiri sosai hatta a harkar wasanni, kasar dake da yawan musulmi tana aikewa da sako na siyasa ne ta hanyar takawa yan wasan isra’ila birki, da kuma neman goyon bayan duniya ga alummar falasdinu. An tsara cewa tawagar wasan Jemanastik din HKI ta za shiga gasar jiminastik na duniya da za’a yi a Jakarta daga ranar 19-25 ga wannan...
Rahotannu sun bayyana cewa sayyid Ammar Hakim shugaban kungiyar wisdom movement na kasar Iraqi ya kaddama da yakin neman zabe inda yayi kira da hadin kai tsakanin alummar kasar kuma ya gargadi kasashe waje da su guji tsoma baka a cikin alamuran kasar. Wadannan bayanai suna zuwa ne adaidai lokacin da kasar Amurka take matsin lamb akan kasar Iraqi na ta rusa kungiyar Hashdu shaabi, musamman bayan abubuwa da suka faru a kasashen siriya da kuma kasar Labanon. An kafa kungiary ta Hshadushaabi ne karkashin umarnin babban malamin Addini na kasar Ayatullah Sisitani domin tunkarar kungiyar ta’adda ta da’aesh Daga karshe Hakim ya jaddada cewa alummar iraki ne kawai suke da hakkin yanke hukumci ba tare da ingizasu ba, duk...
Kungiyoyin matasa na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Morocco, Sarkin Mohammed na shida, ya bukaci zababbun jami’ai a kasar da su daina jan kafa wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar, yana mai cewa inganta harkonin ilimi da kiwon lafiya shi ne abinda ya kamata a fi ba muhimmanci. An jima ana dakon jawabin sarkin na wannan juma’a, tun bayan da masu zanga-zangar, suka fara mamaye titunan biranen kasar kusan ko wanne dare tun daga ranar 27 ga watan da ya gabata na Satumba. Masu zanga-zangar dai wadda ake yiwa lakabi da Gen Z, na ci gaba da ƙ kiraye-kirayen kawo sauyi, ko da yake a yayin jawabin Sarkin na wannan Juma’a bai yi magana kai tsaye game da ita...
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce talauci da nuna bambanci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata damar samun ilimi a jihar. Ta bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Yara Mata ’Yan Makaranta ta Duniya ta shekarar 2025, wanda Shirin AGILE tare da Access Initiative Africa da Nudge Initiative suka shirya a Gombe. Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno A wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba da yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a bar wata yarinya a baya wajen samun ilimi....
Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida. Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar. Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko...
Ta wadanne hanyoyi cutar Kansa ke farawa? Kowace kwayar halitta ta jikin mutum akwai aikin da take yi, asalin kwayar halittar ta kan kasu kashi-kashi; suna mutuwa idan aka fitar da su ko kuma suka lalace, sai wata kwayar ta maye gurbinsu. A irin wannan lokaci ne, Kansar ke samun gurin zama sai ta zuba tata kwayar halittar ta kori asalin kwayar halittar da ke jikin Dan’adam, wanda hakan ke jawo matsaloli a sassan jikin da Kansar ta kama. Saboda haka, kwayar cutar Kansa; ta kan watsu a sauran sassan jiki, misali Kansar huhu ta kan tafi cikin kasusuwa ta girma, a yayin da kwayar ta yadu; ana kiranta da suna ‘meh-TAS-tuh-sis’, ita kuma Kansar huhu idan ta tafi...