’Yan sanda sun kama matashi kan zargin aikata fashi a Gombe
Published: 14th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi mai shekara 18 bisa zargin aikata fashi da makami a jihar.
An kama shi ne a garin Kwadon bayan samun sahihin bayani daga jama’a.
NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa TuraiKakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama matashin ne ranar 9 ga watan Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 2:30 na rana.
Hakazalika, ya ce an samu ƙunshi ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.
Bincike ya nuna cewa matashin na cikin mutanen da ’yan sanda ke nema game da aikata fashi da makami, waɗanda ake shari’arsu a babbar kotun jihar.
A cewar DSP Abdullahi, matashin ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka kai hare-haren.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Bello Yahaya, ya umsrci a miƙa shi zuwa sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike kafin gurfanar da shi a kotu.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba ta bayanai da za su taimaka wajen yaƙar laifuka a jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama.
Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.
Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.