Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129
Published: 13th, August 2025 GMT
129-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam Ali (a) ya kammala hujja a kan mutanen Jamal bayan bin hanyoyi da dama na hana zubar da jinin musulmi amma suka ki amincewa. Sannan ya bijiro masu da alkurni mai girma suka kashe manzon nasa. Sai aka fara yaki, da farko ya bawa dansa Muhammad dan Hanafiyya tutarsa, sai ya karbeta ya rike ta da kansa ya kutsa tsakiyar yaki. Sannan ya hadu du Zubai ya tunatar da shi hidisin manzon All..(s), dangane da shi da yakin , sai ya fice daga yakin. Amma wasu ashararu suka kasasheshi.
Sannan Imam ya sa aka buge kafafuwa rukumin Aisha rakumin ta fadi sai mutanenta suka waste sai aka kawo karshen yakin.
Sai da farko ya aiki Muhammad dan Abubakar ya dauko Aisha ya shigar da ita Basra, sai ya je ya daukota ya shigar da ira Basra a gidan Abdullahi dan Khalaf al-khuza’ii, wanda an kasha shi a yakin tana goyon bayan Aisha. Wajen matarsa Asmau. Inda ta zauna nay an kwanaki, sannan ya aiki ibnu Abbasin, ya je ya fada mata cewa: Tashirya zata koma Madina. A lokacinda Abbas ya nemi izinin shiga wajenta sai ta ki yi mata izinin, sai ya shiga ba tare da izininta ba. Sai ta ce yaya zai shigo mata dakin ta, ba da izininta ba, sai yace, nan ba dakinkinba, dakinki shi ne wanda All..ya umurceki ki zauna a can sai kika saba masa kiki fito. Sun yi mangan-ganu da dama , daga karshe ta amince da koma Madina.
Sai Imam (a) ya hada mata ayarin tafiya ta musamman, wacce bata rasa kome ba. A randa zata tafi sai Imam (a) tare da yayansa Limamai biyu, Al-hassan da Al-hussain(a), da wasu sahabbansa.
A lokacinda matan suka ganshi sai suka fara koka suna kuwa a gabansa, safiyatu mai gidan ta ce masa. Ya kai mai kashe masoya, – idan baku manta ba, an kashe mijinta Abdullahi dan Khalaf al-khuza’ii, sai Imam (a) yace mata: Da na makashance mai kisan masoya ne da na kashe wadanda (kika boye) a wannan dakin, sai ya yi ishara da hannunsa, zuwa wani daki a gidan, inda wasu daga cikin masu adawa da shi suka boye. A nan sai wadanda suke tare da shi, sun so su bude dakin don fito da wadanda Imam (a) yace sun boye a cikinsa, sai ya hanasu.
Daga nan sai yayi magana da Aisha, sai tace: Ina son in zauna da kai, in je tare da kai don yakar makiyanka. Sai Imam yace baya so, ya kuma umurceta da je ta zauna a dikin da manzon All..ya barta a cikinsa. Da haka kuma ta fita ta hau rakumin da aka tanadar mata. Akwai magana dangane da irin mutane da yawansu da ya hada a cikin ayarin nata, wacce zata kaita madina cikin aminci, wanda ita ma bata sani ba har saida ya bayyana a gareta bayan ta isa Madina lafiya.
Yakin jamal shi ne fitina na farko tsakanin musulmi wanda ya kai ga zubar da jininsu a tsakaninsu, don haka al-ummar musulmi kafinyakin Jamal, wanda Aisha mantar manzon All..(s) ta jagoranya, ba zata kuma sake komawa kamar yadda take ba, har abada.
Don, tun farko All..bai dorawa mata yaki ba, sai idan ya kin ya zo cikin gari, to dole ne ta kare kanta. Don haka ina mata da yaki, musamman matan manzon All..(s) wadanda All… a cikin Alkur’ani ya umurcesu su zauna a gidajensu kada su fiya, sai saboda wasu abubuwan da ya ayyanasu. Daga ciki akwai aikin Hajji da sauransu.
Amma Yakin jamal ya budewa al-ummar musulmi kufar musibu da fitina daga lokacin har yau, mai yuwa har zuwa ranar kiyama. Don yakin ne ya bude kofar musulmi ya yi shugaban muminai ko sarkin musulmi. Daga har sai da ya dawo kujerar Amirul muminin ta zaman a wanda yayi rinjaye mumini ko fajiri.
Don bayan jamal ne Mu’awiya ya yaki Amirulmuminina (a) da sunan neman jinin Uthman, wanda karyace, amma suka maida shi hujja ta yakarsa. Da kuma danya Imam AL-Hassan daga baya, da kuma kwace daular musulunci gaba daya daga yadda manzon All..(a) ya barta. Wannan halin ya ci gaba har sai da tulaka da yayansu suka zama khalifofi. Tulaka sune wadanda suka musulunta bayan fatahin Makka, manzon All..(s) ya tarasu ya ce me kuke tsammanin zan muku sai suke ce dan uwa dan danuwa, sai yace to je dukkanku entattu ne. wato sun shiga musulunci shekaru biyu kafin wafatin manzon All..(s). to wadannan ne suka zama khalifofi daga baya. Ba abinda suka sani a addini. Wannan duk yakin jamal ce ta bude wannan bala’ina cikin musulmi.
Yakin Jamal ya budewa banu umayya kofa ta amfani da hujjar neman jin Halifa Uthman har suka kwace mulki a hannun jikan manzon All..(s) Imam Hassan, (a) sannan suka kashe Imam Hussain (a) daga nan suka maida musulmi bayinsu. Suka kasksantar da musulmi daga cikin har da sahabban manzon All..(s) da suka rage a lokacin.
Malaman addinin musulunci gaba daya daga ko wace mazhaba sun gamu a kan cewa, wadanda suka yi wa Imam Ali (a) tawaye sun yi kusre babba, kuma basu da hujja karbebben na yi masa tawaye. Kuma duk sun kirasu da suna –bughat- masu tsokana, ko azzalumai kamar yadda ya zo cikin al-kur’ani mai girma inda All..yake cewa:
{Kuma idan jama’a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa. } Al-hujuraay -09.
Dangane da wannan ayar. Abu Hanifa shugaban mazhab yana cewa: Ba wanda Aliyu (a) ya yaka face shi ne kan gaskiya, kuma ba don Aliyu (a) yayi wadannan yake-yake b aba wanda zai san wasu hukunce-hukunce a tsakanin musulmi. Kuma babu shakka kan cewa Aliyu (a) ya yaki Talha da Zubai ne bayan sun masa bai’a sun kuma kwance bai’ar ba tare da dalili ba. A yakin Jamal Aliyu (a) yayi adalci a cikin nlamarinsu. Don shi ne shugaban musulmi, don haka sai hakan ya zama sunna wajen yakar wadanda suka yi zalunci cikin musulmi).
Ibnu Hajar askali ya ce: Lalle ne mutanen Jamal da Siffin sun tuhumi Aliyu (a) da hannu cikin kisan Uthmanu, amma ya barranta da hakan, kuma yayi nisa da yin hakan). Sannan ya kara da cewa (Wajibi ne a kan shugaban musulmi ya yi wadanda suka yi zalunci, tare da ijmain sahabbai, kuma ba zai yakesu ba sai ya aika masu wani mai ilmi da hikima ya je ya tambayesu dalilin tawayen da suka yi wa limaminsu, ko me suke zargin limaminsu da shi, don koyi da Aliyu (a) a lokacinda ya aiki inbnu Abbas zuwa wajen hawarijawa, da suka yi tawaye a Nehrawan). Wannan kamar yadda ya zo cikin littafin Tuhfatul Muhtaj na Annawawi Jz 4 sh 110.
Don haka tare da wannan lalle shari’ar musulunci ya halatta a yaki wadanda suka yi tawaye, don fitarsu daga shugabancin musulinci, kawo baraka ne da kuma hana hadin kai a tsakaninsu da kuma warware yan’uwantaka da ke tsakaninsu.
Imam Hassan (a) wanda muke karanta siransa, ya ga dukkan wadannan al-amura masu ban tsoro a cikin musulmi, musamman yadda wasu suke kiyayya ga mahaifinsa Amirul muminina (a).
Daga nan sai yakin Siffin yakin da ya sauya al-amura sama ta koma kasa, kasa ya koma sama, yakin da ya zama musiba. A yakin siffin musulmi suka yi rashin da basu taba rashi irinsa ba.
Don a wannan yakin ne, ko kuma a karshe ne aka aiwatar da makirci, mafi muni a tarihin bil’adama, inda gaskiya ta zama kariya karya ta zama gaskiya. Wannan yakin, duk da cewa a karshensa saura kadan Amirulmuminina (a) ya sami nasar a kan Mu’awiya kamar yadda zamu gani, amma sai aka samar da wasu wadanda suke riyawa suna tare da Imam (a) amma suka yi masa tawaye, suka kuma maida nasarar da ya samu a kan Mu’awiya faduwa. Sannan bayan taron sulhun daumata jandal sai abubuwa suka kara lalacewa, inda da sunan neman jinin Khalifa Uthman aka kwace yabkuna da dama daga hannun Amirul muminina (a) yana da ransa a Kufa, yay a magana kan mutane su fita su yaki makiyansu sun ki har sai ya yi shahada, sannan aka tilastawa dansa Imam ya mikawa mu’awiya shugabanci.
A randa mu’awiya ya karbi shugabancin musulmi ya bayyana kafirci da munafurci a fili. Kuma ba wanda ya isa yayi magana. Daga nan kuma mulki ya koma hannun Banu Umayya, a cikinsa ne iyalan gidan manzon All…(a) suka zama abin kyama a cikin al-ummar musulmi, suka zama basu isa su yada addinin musuluni na gaskiya ba sai a moye.
Sun sarrafa takobi a kan iyalan gidan manzon All..(s) da mabiyansu, yadda ba’a taba kyamar wasu mutane a tarihi kamar yadda aka kyamacesu ba. Saboda hasada da kuma son duniya. Da yardar All..zamu bi wadannan abubuwa guda guda kuma dalla –dalla. Don mu fahinci abinda ya sa musulmu suka zama abinda suka zama a yau. Don tasirinn abinda ya faru a Jamal da siffin yana da tasiri kan yadda musulmi yake a yau. Ya zama mai daukan kaskasci, kafirai sun maida su kazi suna yankawa, duk duniya suna gani ba za su iya daga ko kara ba. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu don jin abinda ya faru a Siffin,a cikin shirimmu na gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Alhininsa Kan Kashen Masanan Kasar Iran Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Yi August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wadanda suka yi masu sauraro yakin jamal kamar yadda yakin Jamal
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Allah Wadai Da Hana Amfani Da Hijabi A Jami’ar LandMark, Omu-Aran Kwara
Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta yi Allah-wadai da wata sanarwa da ake zargin Bishop David Oyedepo kan amfani da hijabi da daliban Musulman Jami’ar Landmark ta Omu-Aran ta Jihar Kwara suka yi.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun wakilinta na kasa Sheikh Abu Sheriff, kungiyar ta yi Allah wadai da Bishop David Oyedepo da take hakkin dalibai musulmi da ma’aikatan cibiyar da ke da hakkin dan Adam kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar.
A cewarsa a cikin wani faifan bidiyo da aka yada sosai, Oyedepo ya yi kira ga iyaye da masu kula da Musulmai da su janye ‘ya’yansu mata idan suka dage ba za ayi amfani da hijabi ba.
Kungiyar ta bayyana dokar hana amfani da hijabi a jami’ar Landmark Omu-Aran a matsayin ‘wani abin da ba za a lamunta dashi ba’ kuma tauye hakkin addini ne.
Ya yi nuni da cewa ba a daukar musulmi aiki a wannan jami’a, kuma idan aka dauki shi bisa kuskure, to ba za su barshi yin salloli sau 5 ko azumin watan Ramadan ba.
Kungiyar ta ci gaba da cewa haramta wa dalibai musulmi ‘yancin yin amfani da hijabi cin zarafi ne ga ‘yancin yin imani da ibadarsu.
Sanarwar ta bayyana cewa neman iyaye da su janye ‘ya’yansu saboda amfani da Hijabi yana tauye musu hakkinsu na dan Adam.
Kungiyar ta kuma yi kira ga ma’aikatar ilimi ta tarayya, NUC, NBTE da sauran su da su binciki duk masu take hakkin dan adam a cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU