Gyaruwar Alakar Kasuwancin Sin Da Amurka Ta Zarce Bukatun Kasashen Biyu
Published: 14th, August 2025 GMT
Muryoyi daga ko’ina cikin duniya sun nemi a warware matsalar bisa turbar adalci. Shugabannin tarayyar Turai sun yi ta kira ga kasashen Sin da Amurka da su kiyaye bude kasuwanni da gudanar da gasa ta gaskiya. Kasashen kudu maso gabashin Asiya, sun ba da shawarar tabbatar da kwanciyar hankali. Kasashen Afirka da na Latin Amurka sun nuna damuwa da halin da ake ciki saboda barazanar da lamarin yake yi ga damarmakin zuba jari da kasuwancin kasashensu.
Gyaruwar dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka za ta iya haifar da wani sabon zamani na hadin gwiwa, da kirkire-kirkire, da ci gaban da ya kunshi kasashen duniya baki daya. A wannan duniyar tamu wadda bukatar hada hannu da juna ke kara bayyana, kiran a bayyane yake, wato duniya tana bukatar Sin da Amurka ba kawai don zama tare ba, har ma su zama ababen buga misali a bangaren aiki tare. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna
Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa. Ya ce sakamakon binciken farko ya nuna tayar ɗaya daga cikin tankokin ce ta fashe, lamarin da ya sa tankar da ke biye ta bugi ta gaba, wanda ya haddasa fashewar gas da tayar da gobara.
Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na ƘasaKwamandan hukumar kashe gobara ta ƙasa a Zariya, Aminu Ahmadu Kiyawa, ya ce jami’ansa sun isa wurin cikin gaggawa bayan samun kiran wayar gaggawa. Ya tabbatar da cewa mutum uku sun jikkata sakamakon fashewar gas, yayin da aka ceto mutum guda daga ɗaya tankar, kuma duka huɗun an garzaya da su zuwa asibitin ABU domin samun kulawar likitoci.
Kiyawa ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa haɗarin ya rutsa da ƙananan motoci irin su Gulf, yana mai cewa “Lokacin da muka isa wurin, tankoki biyu ne kawai muka gani. Babu wata ƙaramar mota da ta shiga hatsarin.” Shaidun gani da ido ma sun tabbatar da cewa tankoki biyu kacal ne suka shiga haɗarin, kuma babu wanda ya rasu a lokacin da ake haɗa wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp