Arakci: Mun Yi Tattaunawa Mai Kyau Da Mahukuntan Kasar China
Published: 23rd, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar.
Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.
Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.”
Haka nan kuma ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da su ka tattauna da su ka hada siyasar Amurka da halayyarta ta nuna karfi, da kokarin da take yi na mamaye fagen siyasar kasa da kasa.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi Magana akan ziyarar da shugaban kasar Iran zai kai zuwa kasar China wacce za ta kasance ba da jimawa sosai ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China
Ambaliya sanadiyyar wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi ajalin mutane 30 a Arewacin China, lamarin da ya tilasta kwashe mutane fiye da 80,000 zuwa Beijing, babban birnin kasar.
Jaridar Beijing Daily ta ruwaito cewa ruwan saman ya haddasa rufe hanyoyi da dama da kuma katsewar lantarki a kauyuka sama da 130 yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto.
Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a AlkaleriA jiya Litinin ce Shugaban China, Xi Jinping ya ba da umarnin daukar matakan gaggauwa a yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliya sakamakon mamakon ruwan da ake hasashen za a ci gaba da tafkawa.
Xi Jimping ya bukaci mahukuntan yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliyar da su gaggauta samar da tsare-tsare domin kubutar da jama’a.
A yanzu haka ana hasashen samun saukar mamakon ruwan sama har zuwa gobe Laraba a wasu yankuna sama da 10 na China.
Tuni dai mahukunta suka sanar da bayar da tallafin kudi yuan miliyan 550 — kwatankwacin dalar Amurka miliyan 76.7 ga yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.
Gwamnatin kasar ta ce ta ware yuan miliyan 200 — kwatankwacin dalar Amurka miliyan 27.86 musamman ga birnin Beijing, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe akalla mutane 30 tare da haddasa barna mai yawa.
Bayanai sun ce ambaliyar ruwan ta kuma shafi lardunan Hebei, da Liaoning, da kuma Shandong, lamarin da ya haifar da asara mai yawa da asarar dukiya.