Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
Published: 22nd, April 2025 GMT
A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki.
Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon.
Shugaba Tinubu, wanda yayi tafiya tun a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, ya fara ziyarar ne a Paris, Faransa, kafin daga bisani ya tafi Landan, Birtaniya.
Duk tsawon lokaci da yake wannan tafiya a Turai, shugaban ya ci gaba da tuntuɓar manyan jami’an gwamnati, yana bayar da umarnin aiwatar da muhimmancin al’amuran ƙasa, musamman ma na tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya
Wasu manyan motocin dakon sun yi bindiga a yankin Ɗan Magaji da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Ana fargabar mutuwar mutane da dama sakamakon gobarar tankokin man bayan sun yi hastari a safiyar Litinin.
Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a kusa da Makarantar Rochas Foundation, kan titin Kaduna–Kano bypass daga Kwangila zuwa Dan Magaji.
Hatsarin ya haɗa da manyan motoci biyu masu ɗauke da man fetur da kuma motoci biyu ƙirar Golf ɗauke da fasinjoji.
A sakamakon haka, tankokin biyu suka yi bindiga, wanda ya tayar da wutar gobara mai ƙarfi tare da hayaƙi mai kauri ya lulluɓe hanyar.
Jami’an ceto da tsaro sun rufe hanyar, tare da gargaɗin direbobi da su guji bi ta wurin yayin da ake ci gaba da aikin ceto da dawo da gawarwaki.