An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi
Published: 19th, April 2025 GMT
An shiga ruɗu da fargaba a garuruwan ƙasar Chadi da dama, sakamakon jita-jita da kafofin sada zumunta na yanar gizo ke yaɗawa cewa wasu matsafa na satar al’aurar maza.
Tun daga birnin Moundou da ke kudancin kasar da lamarin ya fara samun asali, inda wasu matasa hudu suka yi ikirarin cewa an sace musu al’aurarsu ta hanyar bakar tsafi, na yaduwa kamar wutar daji a wasu manyan biranen ƙasar Chadi.
Sakamakon jita-jita da bidiyoyi iri-iri da ake yadawa a shafukan sada zumunta, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi a likitanci ko a hukumance ba, lamarin ya bazu tare da tada hankula har a tsakiyar N’Djamena, babban birnin kasar, inda wasu fusatattun mutane suka yi yunkurin kashe wani mutum wanda suka zarga da sace al’aurar wasu yara maza uku bayan ya yi musabaha da su, sai dai ya tsira da ransa sakamakon shiga tsakani da ’yan sanda suka yi, amma ya ji jiki da ɗan karen duka.
Babu tushe a zahiriA yayin da ake fuskantar wannan al’amari wanda a halin yanzu girmansa na iya haifar da hargitsi na zaman lafiyar jama’a, gwamnati ta yanke shawarar tashi tsaye don ƙoƙarin kawo karshensa.
Kakakin gwamnatin Chadi, Gassim Cherrif ya ce lamarin na neman wuce gona da iri, domin kuwa ana kai wa mutane hari tare da jikkata da dama saboda zargi marasa tushe a zahari, yana mai cewa gwamnati ba za ta zuba ido tana gani har lamarin ya girma ba, ta yadda mutane ke ɗaukar doka da hannunsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Satar Al aura
এছাড়াও পড়ুন:
Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe
Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da kuma jikkatar wasu 13, sakamakon tashin wutar lantarki a unguwar Tudun-Wada, Pantami a jihar.
Wutar ta tashi ne da safiyar ranar Asabar sakamakon matsala da ta taso daga wata tiransifoma a yankin, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana.
Sojoji sun kama ɗan China da wasu 4 kan zargin safarar makamai a Borno da Yobe Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwaCikin waɗanda suka rasa rayukansu har da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka ta Musamman ta jihar, Alhaji Muhammad Yusuf Kulani, tare da ’ya’yansa da wasu mazauna unguwar.
Marigayin shi ne shugaban ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Jihar Gombe (ANAN).
’Yan sanda daga ofishin Low-Cost sun isa wajen don tabbatar da tsaro da kuma kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bello Yahaya, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.
Ya kuma ce za su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin tashin wutar da kuma ɗaukar matakan kare faruwar hakan a gaba.
Ya kuma roƙi al’umma da su kasance masu bin doka tare da bayar da haɗin kai yayin gudanar da binciken.