An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno
Published: 18th, April 2025 GMT
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba.
Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis.
Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a da sansanin sojan Yamtake.
“Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su dawo, amma mun sami labarin cewa mutane biyu daga cikin jami’anmu da wasu fararen hula harin ya shafe su. Ina ba da shawarar mu jira har sai sun dawo,” in ji shi.
Sai dai Sanata Ali Ndume, ya ce tun lokacin da lamarin ya faru yana tuntuɓar al’ummar unguwar Yamtake.
“Abin takaici ne cewa mutanenmu a ƙauyen Yamtake sun fuskanci mummunan harin Boko Haram a daren ranar Alhamis, ɗaya ne daga cikin unguwannin da suka karɓi ’yan gudun hijirar kwanan nan, gwamnatin Jihar Borno ta sake tsugunar da su.
“Abin baƙin ciki ne yadda sojoji biyu suka rasa ransu a bakin aiki, yayin da wasu fararen hula da ba a san ko su wanene ba na daga cikin waɗanda suka jikkata, Allah Ya gafarta musu.
“Amma kuma na yabawa Birgediya Janar Nasir Abdullahi, Birgediya Kwamanda na runduna ta 26 Task Force da jiga-jigan sojojinsa kan sadaukarwar da suka yi ba tare da ƙaƙƙautawa ba wajen daƙile hare-hare da dama, musamman waɗanda aka yi yunƙurin kaiwa farmakin a garin Gwoza.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Yamtake fararen hula
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13.
Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroDSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana.
Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar ’yan sanda, jami’an DSS, da kuma sojoji.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa suna matuƙar farin ciki da wannan nasara, musamman ganin cewa mutanen sun kwashe watanni a hannun ’yan bindiga cikin tsananin wahala.
Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere, tare da inganta matakan tsaro a yankin don kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin.
“Za mu ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi don tabbatar da cewa babu wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da za ta samu mafaka a Kaduna,” in ji DSP Mansir Hassan.