Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki
Published: 16th, April 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al’adu.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin na tabbatar da tsarin aiki mai cike da mutuntaka, da daidaito.
Ya ce, majalisar zartarwar ta kuma amince da kaddamar da makon kirkira da kere-kere na jihar (JISCIW) daga shekarar 2025.
Ya jaddada cewa, wannan tsari na nuna jajircewar gwamnatin wajen bunkasa basira da hazakar matasa, da kuma inganta kirkire-kirkire da tunani mai zurfi a fadin jihar.
Sagir ya bayyana cewa, JISCIW zai kara zaburar da matasa a fannoni daban-daban kamar fasaha, zane, kasuwanci da kuma harkokin fasaha.
Ya kara da cewa, majalisar ta amince da fitar da sama da Naira miliyan 516 domin sayen tikitin jirgi ga daliban jihar Jigawa 185 da ke karatu a fannin likitanci da kimiyyar kiwon lafiya a Jami’ar Near East dake kasar Cyprus, domin shirye-shiryen zangon karatu na shekarar 2024/2025.
Kwamishinan ya kara da cewa, wannan tallafi ya nuna yadda gwamnatin ke ci gaba da daukar nauyin ilimi da jin dadin daliban da ke karatu a kasashen waje, musamman a muhimman fannoni kamar likitanci da kiwon lafiya.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.