A nasa bangare kuwa, To Lam cewa ya yi Vietnam a shirye take ta yi aiki tukuru don kyautata tsare-tsare da hadin gwiwa da bangaren Sin ta yadda za a daga martabar cudanyar sassa daban daban, da nacewa ka’idoji 5 na zaman jituwa, da kare dokokin gudanar da cinikayya na kasa da kasa, da martaba yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin sassan biyu, da hada hannu wajen ba da gudummawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban daukacin bil’adama.

(Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030

Majalisar Wakilai ta umarci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Shirya Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) da su dakatar da shirin fara amfani da tsarin jarabawa ta kwamfuta a jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2026.

Umarnin ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa da Kelechi Wogu ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya

Kudirin na Wogu mai taken: “Bukatar Daukar Mataki Don Kaucewa Yawan Faduwa a Jarabawar Kwamfuta da WAEC ke Shirin Gudanarwa a 2026,” ya yi gargadin cewa gaggauta amfani da tsarin na iya haifar da yawan faduwa da kuma jefa dalibai cikin damuwa.

Wogu ya nuna damuwa kan yadda Ma’aikatar Ilimi ke da niyyar ci gaba da tsarin jarabawa ta kwamfuta duk da adawar da ke fitowa daga Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa da shugabannin makarantu, musamman a yankunan karkara inda fiye da kaso 70 cikin 100 na masu jarabawar ke zaune.

Ya ce yawancin makarantu, musamman a yankunan karkara, ba su da dakunan kwamfuta masu aiki, babu intanet, babu wutar ingantacciyar lantarki, kuma ba su da malamai masu ƙwarewa a fannin fasahar zamani.

Ya jaddada cewa fara amfani da tsarin a irin wannan yanayi zai zo da matsala, yana ambato matsalolin fasaha da suka shafi shafin sakamakon WAEC na 2025 a matsayin shaidar rashin shiri.

Domin magance waɗannan ƙalubale, Majalisar ta umarci Ma’aikatar Ilimi da ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin saka ayyukan daukar malamai masu koyar da kwamfuta, gina dakunanta, samar da kayan intanet da kuma wutar lantarki a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 zuwa 2029.

Majalisar ta kuma yanke shawarar cewa kada a fara amfani da tsarin jarabawar kafin shekarar karatu ta 2030.

Majalisar ta amince da kudirin gaba ɗaya, tare da umartar kwamitocinta kan Ilimi a matakin farko, Fasahar Zamani da Bayani, Hukumomin Jarabawa, da Ma’aikata da su tattauna da masu ruwa da tsaki sannan su gabatar da rahoto cikin makonni huɗu domin ɗaukar matakin dokoki na gaba.

An kirkiro da tsarin jarabawa da kwamfuta ne a Najeriya ne domin rage yawan magudin jarabawa da kuma sabunta tsarin ilimi na ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli
  • Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato
  • Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  
  • Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 
  • Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
  • Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe
  • Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati
  • Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
  • Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030