2025-11-11@20:52:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6669

«kasar Aljeriya»:

    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
    An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.   Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.   Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.   Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da...
    Kungiyar kasashe da cibiyoyin kasa da kasa ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta yi Allah wadai da manyan laifukan da aka aikata a ƙasar Sudan bayan kwace El Fasher daga dakarn (RSF) suka yi, da kuma ƙaruwar tashin hankali a yankin arewacin Darfur da Kordofan. Wannan sanarwar, wadda ministocin harkokin waje da manyan jami’ai daga Australia, Belgium, Kanada, Denmark, Estonia, Hukumar Tarayyar Turai, Jamus, Iceland, Ireland, Luxembourg, New Zealand, Netherlands, Norway, Slovakia, Slovenia, Spain, Sweden, da Birtaniya, tare da goyon bayan Austria, Croatia, Cyprus, Czechia, Finland, Latvia, Poland, Romania, da Switzerland suka yi, ta nuna damuwa sosai game da rahotannin ta’asar da aka aikata a kan fararen hula. Wannan sanarwar haɗin gwiwa ta yi nuni da...
    Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno Mutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai. A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda...
    Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake yi na cimma matsaya ta siyasa. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Masar, Tamim Khallaf, ya bayyana cewa Minista Abdel-Aty ya tabbatar a lokacin taron cewa matsayin Masar kan rikicin Libya, ya dogara ne kan bin tsarin siyasa da Libya take a kai ba tare da wani umarni ko tsangwama daga waje ba, a matsayin hanya daya tilo ta dawo da tsaro da kwanciyar...
    ‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista zai kafa. A cewar jami’an zabe, za a sanar da sakamakon cikin sa’o’i 24 bayan kammala zaben. Firaminista Mohammed Shia al-Soudani ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana “a cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali,” yana yabon jami’an tsaro saboda kiyaye tsarin. Al-Soudani, wanda aka zaba a shekarar 2022, yana neman wa’adi na biyu kuma zai bukaci samun rinjaye a majalisar. A Iraki,...
    Ministan Harkokin Wajen Sudan Mohieldin Salem ya yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi game da ci gaba da cin zarafin dan Adam  da Rundunar Taimakon Gaggawa  ta (RSF) ke yi a yankunan El-Fasher, Darfur ta Arewa, da Bara, da Kordofan ta Arewa. Ya yi wadannan kalaman ne a lokacin wani taro a Port Sudan da Darakta Janar na Kungiyar Kula da kaura ta Duniya (IOM), Amy Pope, wacce ta isa Sudan don ziyarar kwanaki biyar, a cewar kamfanin dillancin labarai na SUNA. Salem ya yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi game da ci gaba da take hakkin dan adam da RSF ke yi a El-Fasher da Bara. Ya jaddada bukatar hada karfi...
    Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin...
    Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin...
    Daga Usman Muhammad Zaria    Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa jagoranci na gaskiya da tsari, yana mai cewa Jihar Jigawa ta zama abin koyi wajen gudanar da mulki da kuma ingantaccen aiki a ma’aikatu. Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin wata ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a Gidan Gwamnati da ke Dutse. Muhammad Idris ya tuna da wata ziyarar da ya taba kaiwa Jigawa a baya, lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin duba harkokin noma. Ya ce yadda ya ga ana yin noman rani ya sa shi shauki game da irin ci gaban da ake samu a jihar. Ya kuma bayyana godiyarsa kan kyakkyawan tarba...
    Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin  jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron dan adam , kuma ya bayyana cewa an shirya harba tauraron dan adam guda uku na:  Zafar, Paya, da Kowsar  a farkon hunturu. A cewar Pars Today, ya yi Ishara da hadin gwiwar da Iran ke yi da wasu kasashe a fannin sararin samaniya, yana mai ambaton ayyukan hadin gwiwar da China kan ayyukan  hadin gwiwar bincike da kasashen mambobin ECO. Wannan ayyukan hadin gwiwar...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin yana cikin shirin “Gwamnati da Jama’a” wanda ke karfafa al’umma, rage matsalolin sufuri da kuma karfafa harkokin kasuwanci. Ya ce shirin ya kunshi gina manyan hanyoyi guda shida a sassan jihar, masu tsawon kilomita 179 gaba daya, a kan kudin da ya haura Naira Biliyan 81. Hanyoyin sun hada da Mallam Madori zuwa Gari Uku zuwa Kanya Babba zuwa Malorin Kasim, ta ratsa ta...
    Shahararren ɗan wasan wrestling, John Cena, ya samu nasarar lashe kambun Intercontinental a karon farko a tarihinsa. Cena ya lashe kambun ne da yammacin jiya Litinin, bayan ya doke Dominic Mysterio a birnin Boston, ƙasar Amurka. Sanata Jarigbe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP Da wannan nasarar, yanzu John Cena ya cika burinsa na lashe dukkan manyan kambuna da ake bugawa a gasar wrestling. Ɗan wasan mai shekaru 48, wanda ake sa ran zai yi ritaya a watan Disamba mai kamawa, ya zuwa yanzu ya lashe kambuna 17 a gasannin daban-daban da ya shiga. Tuni dai Cena ya bayyana cewa bayan ritayarsa zai mayar da hankali wajen fitowa a fina-finan Hollywood,...
    Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani. A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron saboda rashin bin ƙa’idojin doka, ciki har da gaza bayar da sanarwar kwanaki 21 kafin gudanar da taron kamar yadda doka ta tanada. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya November 11, 2025 Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025...
    Sanata Jarigbe Agom Jarigbe, mai wakiltar Arewacin Jihar Kuros Riba, ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Sanatan ya bayyana sauyin shekarsa ne a wasiƙar da Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya karanta a zauren Majalisar ranar Talata. Sauyin shekar ta kara yawan mambobin APC a Majalisar Dattawa zuwa 77
    ’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.” Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga. “Mun kai wani matsayi da ’yan...
    A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?” Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a...
    Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin Kebbi. Sarkin Argungu, wanda ya yi jawabi a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufofin Gidauniyar Sarkin Musulmi na inganta ilimi da...
    Ƙungiyar Tsofaffin Sojoji ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace. Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi. Ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari ganin cewa muryar zawarawan sojojin da suka rasu ta isa inda ya kamata, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kuma tabbatar da samun tallafin da suka cancanta. Allison-Alamini ya kuma sha alwashin ba da muhimmanci ga walwalar tsoffin sojoji a jihar, tare da gode wa mambobin ƙungiyar bisa yadda suka ba shi amanar shugabanci. Wani mutum ya...
    Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba. Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike. Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi. Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil. Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma  masu rajin kare muhallin na...
    An kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na takwas (CIIE) a yau Litinin, inda aka samu daddale kulla cinikin dalar Amurka biliyan 83.49 a cikin yarjejeniyoyi da aka cimma na shekara guda, wanda adadin da aka samu ya karu da kashi 4.4 cikin dari idan aka kwatanta da na baya kuma ya kai wani sabon matsayi, kamar yadda hukumar kula da bajen kolin na CIIE ta bayyana. Dandalin baje kolin ya kai fadin murabba’in mita 367,000, inda ya jawo hankulan kamfanoni 4,108 daga kasashe da yankuna 138, lamarin da ya karya tarihin yanayin girma da adadin mahalartan na baya da aka gudanar. Baje kolin na tsawon kwanaki shida ya kunshi sabbin kayayyaki, da...
    Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, ta rasu tana da shekaru 89 a duniya. Iyalai sun tabbatar da cewa ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Litinin, bayan fama da doguwar jinya. Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa kuma Hakimin Shagari, Kyaftin Bala Shagari (mai ritaya), shi ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da aka fitar daga Sakkwato. Sanarwar ta ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna baƙin cikin sanar da rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, mata ɗaya tilo da da ta rage wa tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November 10, 2025
    Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kudin kujerar aikin da lokacin da za a rufe karbar kudin maniyyata. Wannan dai ya biyo bayan kulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 da hukumar ta yi a madadin Najeriya da hukumomin kasar Saudiyya, a lokacin wani biki da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya. Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar. Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da rage kudin kujerar aikin hajji ne, bisa umarnin shugaban ƙasa. Share 0 0 votes...
    Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata. Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka  yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji,  wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji  dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari. Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
    Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi. Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya “Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris. Ministan ya ziyarci...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia. An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan...
    Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Lawal Aliyu, ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajji daga Abuja su bi ƙa’idojin da aka shimfida. An bayyana cewa tabbataccen kuɗin Hajjin ya samu ne bisa ƙayyadadden tsari daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), sannan duk biyan kuɗin za a yi ne ta hanyar Banki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, ba tare da karɓar kuɗi a hannu...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025 Manyan Labarai Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya November 8, 2025 Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025
    Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban.   “Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.”   Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar kiwon lafiya a gwamnatinsa, inda take gaba-gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5 November 10, 2025 Labarai Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta  November 10, 2025 Labarai Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC November 10,...
    ‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a kauyen ‘Yan Kwada da ke cikin garin Farun Ruwa a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar, ciki har da masu shayarwa. Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a yankin a ranar Lahadi da yamma, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi sannan suka afka cikin gidaje da dama, sannan suka tafi da matan. Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno “Na samu labarin cewa, an sace mata biyar, wasu daga cikinsu, masu shayarwa ne...
      Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba. Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari, Keke da Doka. Mazauna sun bayyana cewa an katse musu wuta na makonni saboda ƙin karɓar mitocin da kamfanin ya kawo. Sun ce matakin Kaduna Electric ya saba da umarnin Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC), wadda ta tanadi cewa dole a tattauna da al’umma kafin a yi canjin mita ko a sauya tsarin biyan kuɗin wuta. Mazauna sun kuma yi ƙorafi cewa kamfanin...
    Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana  mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira       ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa; sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 44 da suke a cikin sansanonin ‘yan hijira mabanbanta a yankin Gaza. Sanarwar ta ce, wannan adadin, yana a karkashin jumillar ‘yan jarida 254 da su ka yi shahada a tsawon lokacin yakin da ya fara daga watan Oktoba na 2023, zuwa watan Oktobar wannan shekarar ta 2025. Kwamitin dake kare ‘yancin aikin jaridar dake karkashin kungiyar ‘yan jaridar ta Falasdinawa, ya ce; Kashe ‘yan jarida da HKI take yi wani shiryayyen tsari ne da ya hada kai hare-hare akan sansanon ‘yan hijira da suke a kusa da asibitoci da sauran cibiyoyin da hukumar ‘yan hijirar Falasdinawa ta MDD, Unrwa take kula da su....
    Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.   “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
    ’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa. Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane. “Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar. Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2...
    Pars Today – Kimanin masu jefa ƙuri’a miliyan 1.3 na Iraki sun je rumfunan zaɓe jiya, Lahadi (9 ga Nuwamba). An gudanar da wannan zaɓen na musamman kwanaki biyu kafin babban zaɓen ‘yan majalisar dokoki na Iraki, wanda za a gudanar a ranar Talata ta wannan makon (11 ga Nuwamba). An ci gaba da gudanar da zaɓen har zuwa ƙarfe 6 na yamma agogon ƙasar, bayan haka aka rufe akwatunan zaɓe ta hanyar lantarki. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar da cewa an shirya cibiyoyin zaɓe 809, ciki har da akwatunan zaɓe 4,501, a faɗin ƙasar don ranar zaɓen musamman. A wannan zagayen zaɓen, ‘yan takara sama da 7,744 daga ƙungiyoyin zaɓe 31 sun tsaya takarar kujeru...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027. Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano. “Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu. An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama  a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
    Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93. Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya. Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Ana sa ran gudanar da Sallar jana’izarta a safiyar Litinin daina nan da misalin ƙarfe 11, a gidan nata da ke Bambale, Birnin Zariya.
    A taron CELAC na biyar tare da Tarayyar Turai a Colombia, shugabannin Latin Amurka sun yi Allah wadai da karuwar jibge  sojojin Amurka a yankin Caribbean, suna gargadi game da tsoma bakin kasashen waje da kuma yin kira da a hada karfi da karfe wajen kare ‘yancin kai da zaman lafiya. Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya aika wa kasashe mambobin CELAC wasika yana mai kira da su yi tir da abin da ya bayyana a matsayin tsokana da neman tyar da zaune tsaye da Amurka ke yi a yankin Caribbean. Da yake magana kan hare-haren da aka kai kwanan nan kan jiragen ruwa na kamun kifi da kuma tura sojojin Amurka kusa da iyakokin ruwa na Venezuela, Maduro ya bayyana...
    Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta,  yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.” A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne  ƙasa ta tsaya musu. Ya ƙara da cewa: “Dangane da wannan hari na  Isra’ila a kan ƙasarmu, sojojin Lebanon ba...
    Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.” A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan ta yanke, wacce shugabanninta suka goyi bayanta baki daya, ta tabbatar da cewa “babu wani sulhu da masu kisan gillar al’ummar Sudan.” Ya kara da cewa, “Ba za mu yi sulhu a kan wannan kasa ba, kuma ba za mu bari a sauke tutarta ko a lullube ta a cikin laka tare da ta wulakanta ta ba.” Gwamnan Darfur ya nuna cewa rikicin da ake...
    A yau Lahadi 9 ga wannan wata, an rufe taron koli na Wuzhen na ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya na shekarar 2025 mai taken “kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa mai bude kofa da hadin gwiwa da tsaro don kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo”, inda wakilai fiye da 1600 daga kasashe da yankuna fiye da 130 suka halarci taron da tattauna taswirar kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa.   Babban sakataren taron Ren Xianliang ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, an zartas da rahoton aiki na taron yanar gizo na duniya na shekarar 2025 a gun taron koli a...
    Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu. Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa. Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga “Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi. Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025 Wasanni Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax November 6, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
    Daga Usman Mohammed Zaria Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Abba Zari Malamawa a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Dutse. A jawabinsa yayin kaddamarwar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci sabon shugaban da ya kasance mai gaskiya da rikon amana wajen hulda da ya’yan kungiyar tare da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar da ake bukata. Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci masu sana’ar dako a karamar hukumar Dutse da su nuna cikakken goyon baya ga sabon shugaban, tare da mutunta ‘yan kasuwa a matsayin su na jigo wajen ciniki da kasuwanci wanda ke bude kofar samu ga ‘yan dako. Ya kuma yi...
    Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, yau Lahadi, inda suka tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Mista Araghchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yanzu tsakanin Afghanistan da Pakistan, yana mai jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da taimakon kasashen yankin masu tasiri, don sasanta takaddamar da rage tashin hankali. A watan da ya...
    A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar. Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin watsi da ikirarin na Trump na “kisan kiyashin Kiristoci.” Masu zanga-zangar sun zargi Washington da amfani da addini domin tsoma baki da a cikin harkokin cikin gidan Najeriya, suna gargadin cewa duk wani matakin soja na Amurka zai keta hurumin Najeriya. A ranar 1 ga Nuwamba, ne Trump ya ce ya umarci Pentagon da ta shirya daukar matakin soji a Najeriya, yana mai ikirarin cewa...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe. Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki. Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta. Tashar...
    Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata.  Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul ya fitar da sammacin kamo mutane 37 masu hannu a kisan kiyashin Gaza daga cikinsu da akwai Netanyahu, ministansa na yaki, Kats, da babban hafsan hafsoshin sojan ‘yan sahayoniya Iyal Zamir. A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo Fira minista Netanyahu da tsohon ministansa na yaki Yoav Gallant saboda amfani da yunwa...
    Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo. ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar. Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya...
    Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445. George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401. Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban...
    Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma  zai share fagen...
    ‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. ‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin...
    Hare-haren daukan fansa da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar janyo hasarar dala miliyan 200 Harin da aka kai wa matatun mai na Haifa na ɗaya daga cikin ayyukan da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin da Isra’ila ta kai a lokacin yaƙin kwanaki 12. Shirin “Lambar” a cikin ɓangarensa na “Sa ido”, ya magance wannan aikin. Waɗannan matatun mai suna daga cikin muhimman wurare na dabaru a Isra’ila, waɗanda ke cikin ɗaya daga cikin muhimman tashoshin jiragen ruwa kuma suna aiki a matsayin babbar cibiyar jiragen ruwa da ke jigilar mai zuwa ƙasar. A cewar ƙididdiga da ƙayyadaddun fasaha, matatun mai na Haifa suna da ƙarfin samar da tan miliyan 9.8 a...
    Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne  har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
    Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan. Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta. Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace. Haka kuma,...
    Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya taɓa zargin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ƙirƙiro Boko Haram. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya mara tushe. Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Ya ce bai taɓa yin wata hira ko yi wa wani bayani da ya shafi Shettima game da kafa Boko Haram ba. “Wannan labari ƙarya ne gaba ɗaya, kuma an shirya shi ne domin rikita jama’a da kawo rabuwar kai,” in ji sanarwar. Sheriff, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce waɗanda...
    Fidan ya ci gaba da cewa akwai bukatar fara aiwatar da kudirin da aka cimma yayin taron kasashen Musulmi na OIC da kuma Arab League dangane sake gina Gaza don karfafa da kuma tallafar rayuwar dimbin Falasdinawan da Isra’ila ta tagayyara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga November 8, 2025 Manyan Labarai Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya November 8, 2025 Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025
    Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar. Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne. Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar...
    BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”.   Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
    Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi  ya zo na daya a duniya  da maki 170.80  kuma yana mataki na 4  a bangaren Olympic, A gefe...
    Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya taɓa zargin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ƙirƙiro Boko Haram. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya mara tushe. Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Ya ce bai taɓa yin wata hira ko yi wa wani bayani da ya shafi Shettima game da kafa Boko Haram ba. “Wannan labari ƙarya ne gaba ɗaya, kuma an shirya shi ne domin rikita jama’a da kawo rabuwar kai,” in ji sanarwar. Sheriff, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce waɗanda...
    Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
    Prime ministan kasar Iraki shiya Al-sudani ya sanar a birnin bagadaza cewa sun fara shirin kula wata yarjejeniya a hukumace da kasar Amurka, da zai kai ga ficewar sojojin kasashen waje daka kasar, daga nan zuwa wata satumbar shekara ta 2026, wanda wannan wata ishara ce ta bude wani sabon shafi a kasar na zaman tabbaci da tsaro mai dorewa. Kasar iraki na kokari wajen ganin an kawo karshen zaman sojojin mamayar Amurka dake kasar fiye da shekaru 20 da kuma tsoma bakin kasashen wajen, da ya fara daga lokacin da Washington ta shiga kasar a shekara ta 2003 domin kaddamar da hare-hare da dukkan duniya ta yi tir da shi da kuma bayyana shi a matsayin wanda ya sabama...
    Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin keta hakkin bil adama da kuma yin kisan kare dangi kan alummar Gaza a lokacin yaki, Wannan yana nuna irin mataki mai tsauri na doka da aka dauka kan jami’an Isra’ila a baya bayan nan, kan laifuka yaki da suka tafka kan bil adam a yakin Gaza, da kuma karfafa kasashen duniya daukar matakin da ya dace kan zargin da ake mata na kai hare-haren kan fararen hula. Sabanin tsakanin Ankara da tel aviv ya kara tsananta ne tun bayan da ta fara kai hare-haren kan fararen hula a yankin gaza a shekara ta 2023...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da takwaransa na kasar Saliyo, Shugaba Julius Maada Bio, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, da yammacin jiya  Juma’a. Shugaba Bio ya isa fadar Villa da misalin ƙarfe 9:08 na dare, inda aka yi masa tarbar ban girma, kafin ya wuce ofishin Shugaba Tinubu domin gudanar da ganawar ta sirri. An gudanar da tattaunawar ne kofa kulle, inda ake ganin manyan batutuwan da suka shafi karfafa dangantakar diplomasiyya, hadin gwuiwar tattalin arziƙi da tsaro tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban hadin kai a kungiyar ECOWAS su ne suka fi ɗaukar hankali. Taron ya zo ne watanni hudu bayan da Shugaba Bio ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ECOWAS daga hannun Shugaba Tinubu,...
    A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
      Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro): Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025
    Bishop Matthew Kukah, na Cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato, ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo wa Najeriya ya farkar da shugabannin ƙasar nan.  Trump, ya zargi Najeriya da cin zarafin Kiristoci tare da barazanar janye tallafin Amurka ko kuma ɗaukar matakin soja domin “ceto Kiristoci” a ƙasar. Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Sai dai Shugaba Bola Tinubu, ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cikakkiyar dimokuraɗiyya mai mutunta ’yancin yin addini. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 60 na ɗan jarida Reuben Abati a Jihar Legas, Kukah, ya ce kalaman...
    Nama ko kaza ko kifi, Man gyada ko gyada da aka nika, Daddawa, Yakuwa (ko kubewa, ko danyen ganyen kuka bisa ga nau’in da ake so), Attaruhu da tattasai, Albasa,Maggi da gishiri, Citta da tafarnuwa (idan ana so)   Yadda ake hadawa: Da farko za a wanke nama, a saka a tukunya, a zuba albasa, daddawa, maggi da gishiri, a dafa har sai ya fara dahuwa. Sannan sai a nika kayan miya, tattasai, attaruhu, da albasa tare (idan ana so, a hada da tafarnuwa da citta). Sai a kaka kayan miya bayan naman ya tafasa, a zuba kayan miya da aka nika a ciki, a barshi ya tafasa sosai. Sannan a zuba man gyada Idan ana da man gyada, a...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi.   Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.”   Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025 Manyan Labarai Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma November 7, 2025
    Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki. Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa. Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.” Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025 Manyan Labarai Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma November 7, 2025 Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025
    Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’.   Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai. A babban aikinsu na farko, ’yan...
    Tarayyar Afirka ta yi kira da a girmama ‘yancin kai na tarayyar  Najeriya kuma ta yi watsi da barazanar Trump Kwamitin Tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa game da kalaman da Amurka ta yi kwanan nan game da zargin gwamnatin Najeriya da hannu a kisan Kiristoci da kuma nuna alamun yiwuwar shiga tsakani na soja a karkashin hujjar “kare ‘yancin addini.” A cikin wata sanarwa a hukumance, wacce Al Jazeera ta samu kwafinta, Kwamitin ya jaddada jajircewarsa ga ka’idojin ‘yancin kai, rashin tsoma baki, ‘yancin addini, da kuma bin doka, kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Tsarin Mulki ta Tarayyar Afirka da sauran kayan aikin da suka shafi hakan. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Tarayyar Najeriya kasa ce mai muhimmanci...
    Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi November 7, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil November 7, 2025
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a. Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gana da Shugaban Ƙasa ba tare da ’yan jarida ba. Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya gana da Archbishop Ignatius Kaigama na Katolikan Abuja, a wani yunƙuri na inganta dangantakar addinai da zaman lafiya a Najeriya. Ko da yake ba a bayyana abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙarfafa...
    Samun rinjayen da APC ta yi na kaso biyu bisa uku a dakunan majalisa biyu yana da babban tasiri ga tsara dokoki, gyaran kundin tsarin mulki da kuma tsarin iko a cikin majalisar tarayya. Dangane da gyare-gyaren kundin tsarin mulki, bisa sashe na 9 (2) da (3) na kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara), kowane kudiri da ke neman canza kundin tsarin mulki dole ne ya sami goyon bayan akalla kashi biyu cikin uku na dukkan mambobin kowanne majalisa kuma a tabbatar da kashi biyu cikin uku na majalisun jihohi 36 (jihohi 24). Bisa adadin mambobinta a yanzu, cikin sauki APC na iya tura dokokin gyaran kundin tsarin mulki a majalisar tarayya, ko da yake amincewar matakin...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata. Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa. Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai A wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada zumunta, a ranar Juma’a, ya ce ƙalubalen tsaro a Najeriya, da suka haɗa da ta’addanci da aikata laifuka, ana magance su da sabbin tsari da sauye-sauyen dabarun dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar. “Haƙiƙa muna fuskantar ta’addanci – ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta kusan...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata. Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa. Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai A wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada zumunta, a ranar Juma’a, ya ce ƙalubalen tsaro a Najeriya, da suka haɗa da ta’addanci da aikata laifuka, ana magance su da sabbin tsari da sauye-sauyen dabarun dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar. “Haƙiƙa muna fuskantar ta’addanci – ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta kusan...
      Bugu da kari, Amurka ta bayyana a fili cewa batun sauyin yanayi shi ne mafi girman yaudara da aka yi a tarihin dan Adam, kuma ta fice daga “Yarjejeniyar Paris” sau biyu, wanda hakan ya yi mummunar illa ga kokarin al’ummun duniya na kyautata yanayin duniya, kana ta zama babban cikas ga hadin gwiwar duniya a fannin magance sauyin yanayi.   Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, a kan batun magance sauyin yanayi, abun da al’ummar duniya ke bukata shi ne dunkulewa da hadin gwiwa, ba zargi da dora laifi kan wasu ba. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil November 7, 2025 Daga Birnin Sin...
    Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...