A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
Published: 14th, April 2025 GMT
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya lashe zabe da kawo 90.35% kamar yadda sanarwar ma’aikatar cikin gida ta sanar.
Brice Nguema ne dai ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Ali Bango a watan Ogusta na shekarar 2023, ya kuma shiga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar a wannan zaben.
Dan takara na biyu da yake binsa a baya, shi ne Alain Claude Bilie Bie Nze da ya sami kaso 3.02% na jumillar kuri’un da aka kada.
An sami halartar kaso 70.4% na jumillar wadanda su ka cancanci kada kuri’a da ya zama mai muhimmanci da zai kawo karshen mulkin rikon kwarya na soja.
Zaben na wannan lokacin shi ne irinsa na farko tun 2023.
Yawan masu kada kuri’ar dai sun kai 920,000, sai kuma masu sa idanu daga kasashen waje da sun kai 28,000.
Adadin mutanen kasar Gabon ya kai miliyan 2.3 da mafi yawancinsu suke rayuwar talauci duk da cewa Allah ya huwace wa kasar arzikin man fetur.
Masu Sanya idanu akan zaben sun ce, a kalla san sami kula da dukkanin ka’idojin zabe a cikin kaso 94.8 na mazabun kasar, kuma an baje komai a faifai ba tare da kumbaya-kumbiya ba da kaso 98.6%. Gabanin yin juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin iyalan Bango na shekaru 50, Oligui Nguema ya kasance shugaban rundunar da take tsaron fadar shugaban kasa na kusan shekaru biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sayyid Fadhlullahi Ya Jaddada Muhimmanci Samar Da Makamai Ciki Har Da Kare Kasa Daga Dan Mamaya
Sayyid Fadlallah ya bayyana cewa: Ana samar da makamai ne domin kare kasa da kuma matsa wa abokan gaba
A cikin hudubar sallar Juma’arsa daga mumbarin masallacin Imamain al-Hassanain (amincin Allah ya tabbata a gare su) da ke Haret Hareik a kudancin birnin Beirut, Sayyid Ali Fadlallah ya yi kira da a dauki dukkan matakai na tursasawa makiya yahudawan sahayoniyya janyewa daga yankin kasar Lebanon da ta mamaye, da daina kai hare-haren wuce gona da iri kullum rana kan yankunan Lebanon, da kuma sakin mutanen da suka kama a matsayin fursunonin yaki.
Malamin ya bukaci dukkanin ‘yan kasar Lebanon, ba tare da la’akari da mazhabobin su ba, ko kungiyoyinsu, ko kuma matsayinsu na siyasa, da su tashi tsaye wajen gudanar da hakkokin da sukarataya a wuyarsu kan kasarsu, da kuma fuskantar wadanda ke yin zagon kasa ga ikon kasa da tsaro, da zaman lafiyarta, da kuma samun hadin kan muryarsu wajen tunkarar wadannan hare-haren da ke barazana ga zaman lafiyar cikin gida da zaman dukkan al’umma.