UBEC Ta Bayyana Jihar Jigawa A Matsayin Abin Kuyi A Fannin Ilimi
Published: 11th, April 2025 GMT
Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar.
Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja.
Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin kasar nan.
Kazalika, ta jaddada irin yadda gwamnati ta zage damtse wajen zuba jari a harkar ilmi, tana mai cewa Jihar ta karɓi fiye da Naira biliyan 21 daga tallafin UBEC tun daga shekarar 2004, wanda ya sanya ta cikin jihohin da suka fi cika sharudan samun tallafin UBEC.
Ta kuma lissafa wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin Gwamna Namadi wadanda suka hada da gina fiye da ajujuwa 3,000 da rijiyoyi 500 da daukar malaman makaranta fiye da 7,000.
Tace Gwamnatin ta kuma horas da malamai sama da 17,000 da kaddamar da Kungiyoyin Iyaye Mata da Ƙarfafa Kwamitocin Gudanarwar Makarantu wato SBMC da kuma kulla haɗin gwiwa da wani kamfani a shirin Jigawa UNITES.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jaddada cewar, gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya tsarin karatu da inganta sakamako ta hanyar amfani da bayanai da kuma haɗa kai da al’umma.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar.
Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin aikin hajjin na kananan hukumomi.
Ya ce masu gudanar da aikin, an zabo su ne daga kowace karamar hukuma 27 na jihar domin gudanar da aikin hajjin mai zuwa.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce su kuma masu gudanar da aikin za su horas da maniyyatan a cibiyoyin da aka kebe a kananan hukumominsu na jihar.
Ya bayyana cewa, an shirya taron bitar ne domin wayar da kan jami’an ayyukan da gwamnatin jihar ta dora masu aikin.
Ya ce an yi hakan ne domin a tabbatar da horar da alhazan jihar yadda ya kamata kan abubuwan da suka shafi aikin Hajji.
“An umurci masu gudanar da aikin Hajji su horar da mahajjata kan wajibai, rukunan da ka’idojin aikin Hajji a Saudiyya.”
Labbo, ya yi nuni da cewa, tarbiyyar alhazai yadda ya kamata, zai shiryar da su gudanar da aikin Hajji kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da kuma zama jakadu nagari na jiha da kasa baki daya.
A cewarsa taron bitar zai baiwa maniyyatan damar sanin ayyukan hajjin da ya dace kuma karbabbe.
Ya kuma bayyana cewa, hukumar za ta nada masu gudanar da aikin a cikin kwamitoci daban-daban domin ganin an samu nasarar gudanar da ayyukan Hajji na shekarar 2025.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ci gaba da bayanin cewa, a matsayinsu na jagororin alhazai, dole ne su kasance kusa da mahajjata don samun taimako a Najeriya da Saudiyya idan bukatar hakan ta taso.
Yayin da yake tsokaci kan shirye-shiryen, DG ya lura cewa, hukumar ta riga ta tattara tare da mika fasfunan kasa da kasa na maniyyata aikin hajjin na zuwa tsarin biza.
Ya bayyana daukar nauyin malamai daga dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar zuwa kasar Saudiyya a matsayin irinsa na farko da gwamnatin jihar ta jigawa ta yi.
Tun da farko, Daraktan wayar da kan jama’a da yada labarai na hukumar Alhaji Abdullahi Aliyu ya yi wa jami’an jawabi a kan ayyukan da suka rataya a wuyansu a lokacin gudanar da aikin hajjin 2025.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da gidan rediyon Najeriya sun yabawa Gwamna Umar Namadi da Darakta Janar na hukumar Ahmed Umar Labbo bisa amincewa da su na kasancewa cikin jami’an da za su jagoranci alhazan jihar domin gudanar da aikin hajjin nan gaba.
Sun kuma yi kira ga maniyyatan da su ba su hadin kai domin cimma burin da ake so.
USMAN MZ