Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m
Published: 11th, April 2025 GMT
Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita.
Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su.
NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita.
Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) da Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC), Kamfanin Rarraba Lantarki na Jos da kuma Kamfanin Rarraba Lantarki na Yola.
Sauran su ne Kamfanin Rarraba Lantarki na Legas da takwarorinsa na Enugu da kuma Ikeja.
Sanarwar da Hukumar NERC ta fitar ta ce wannan tarar ta shafi kamfanonin guda takwas ne daga watan Yuli zuwa Satumbar shekarar 2024.
Ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna kamfanonin sun yi watsi da umarnin nata da ya ƙayyade cazar kwastomomi marasa mita da ke kan layin lantarki guda a duk wata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwastomomi Lantarki marasa mita
এছাড়াও পড়ুন:
NAFDAC ta lalata kayayyakin Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta lalata kayayyaki marasa inganci da suka kai sama da Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa.
Kayayyakin da aka ƙwato daga jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Nasarawa, Benuwe da Kogi da Filato, an lalata su ne a wurin zuba shara a Angwan Rere da ke Lafiya.
Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a YobeDarakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Christianah Adeyeye, wanda Daraktan shiyyar Arewa ta Tsakiya, Mista Kenneth Azikiwe ya wakilta, ya bayyana cewa an ƙwace kayayyakin ne a lokacin gudanar da aikin sa ido.
Ta kuma jaddada cewa hukumar na da burin hana waɗannan kayayyaki masu hatsarin gaske su sake shiga kasuwa tare da haifar da illa ga jama’a.
“Wasu daga cikin waɗannan kayayyakin an ɓoye su ne da gangan, an kuma sake sabunta su da gangan bayan ƙarewar wa’adin amfanin da su, an ajiye su da mugun nufi, wasu marasa kishi ne suke sayar da su ga ‘yan Najeriya.
“Har ila yau, lalata kayayyakin da wa’adinsu suka ƙare don son rai ga wasu ’yan kasuwa maza da mata, inda wasu masu kishi da tsoron Allah suka miƙa mana rahoton.”
Kayayyakin da aka lalata sun haɗa da abinci mara kyau, magunguna na jabu, na’urorin likitanci na jabu, ƙayatattun kayan kwalliya da sinadarai da wa’adinsu suka ƙare.