Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
Published: 11th, April 2025 GMT
Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya.
A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna.
“Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu da zamantakewa da muke da ita da Masarautar Zazzau,” in ji shi.
Ya ci gaba da bayyana cewa Masarautar Kauru da Masarautar Zazzau na da alaka mai karfi ta fuskar kima da dabi’u da aka gada tun zamanin da.
Yayin da yake karin bayani kan dangantakar zamantakewa da ta tarihi, Malam Mukhtar ya bayyana cewa:
“Daga auratayya, zuwa hanyoyin kasuwanci, bukukuwa da tsarin shugabanci na gargajiya, dukkanmu muna da zumunci da mu’amala da jama’ar Zazzau. Kokarin cire mu daga wannan tsari da saka mu a wani sabon tsari ba zai haifar da alheri ba.”
Ya jaddada cewa Masarautar Kauru “ta yanke shawara a fili” cewa tana so ta ci gaba da kasancewa a cikin sabon tsarin Jihar Kaduna da ake shirin kafawa, tare da kin amincewa da duk wani yunkuri na saka ta cikin Jihar Gurara.
A karshe, Shugaban KECI ya bukaci masu rajin kafa Jihar Gurara, musamman daga Kudancin Kaduna, da su daina kokarin saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin jihar, yana mai bukatar a girmama ra’ayin jama’ar yankin.
Cov/Jibirin Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jihar Gurara Masarautar Kauru Masarautar Kauru
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.
Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013 zuwa 2020.
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewar sabon shugaban Kanada a fannin kuɗi da shugabanci za ta taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar ƙasar. Haka kuma, ya sake jaddada kudirin Najeriya na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da Kanada, musamman a fannonin ilimi, sauyin yanayi da hijira.
Shugaban Najeriya ya ƙara da cewa yana fatan kafa kyakkyawan hadin gwiwa da gwamnatin Carney, yayin da ya nuna godiyarsa ga kyakkyawar alakar da aka kula a tsakaninsu a zamanin tsohon Firayim Minista, Justin Trudeau.
Bello Wakili