Tawagogin gwamnatin Kongo da kungiyar M23 sun isa Doha domin tattaunawa
Published: 11th, April 2025 GMT
Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin, kamar yadda wasu majiyoyi hudu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Alhamis.
Wakilan tawagogin biyu sun tabbatar da kasancewarsu a babban birnin kasar Qatar, kuma sun ce za a yi ganawar ido-da-ido a ranar Laraba, amma har yanzu suna tattaunawa kan tsarin tattaunawar.
Dukkanin majiyoyi – jami’an gwamnati biyu da wakilan ‘yan tawaye – sun bukaci a sakaya sunansu saboda masu shiga tsakani na Qatar sun nemi kada su yi magana da manema labarai.
Qatar ta yi wata ganawa a watan da ya gabata tsakanin shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame. Wannan ita ce ganawa ta farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan da kungiyar ta kaddamar da hari a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata. Yunkurin yin shawarwarin zaman lafiya na baya-bayan nan shi ne yunkurin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru ana yi, wanda ya samo asali daga kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda a shekara ta 1994.
Wata majiya da ke da masaniya kan shiga tsakani na Qatar ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa bangarorin biyu sun yi wata ganawar sirri a birnin Doha a farkon wannan wata domin shirya tattaunawar sulhu. Sai dai har yanzu tattaunawar da aka shirya fara a ranar Laraba na fuskantar cikas.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.
AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.
Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.
‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.
Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.