An Kafa Dokar Kai Da Komowa A Kudancin Kasar Syria
Published: 11th, April 2025 GMT
Mahukunta a kasar Syria sun kafa dokar hana zirga-zirga a yankin Dar’a dake kudancin kasar Syria.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambato cewa; jami’an tsaron kasar ta Syria sun kafa dokar ta baci a yankin “Basra-sham’ dake yankin Dar’a.
Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin da ya sa aka kafa wannan doka, amma wasu majiyoyin sun ambaci cewa a cikin kwanakin bayan nan an sami rikice-rikice a yankin.
Wasu majiyoyin sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai sun yi harbe-harbe a yankin wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutane biyu a garin Basras-sham.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran.
A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko da yake ana gabatar musu da wani hoto na daban da ya yi hannun riga da hakikanin Iran da al’ummar kasarta a ketare, amma Iran kasa ce mai karbar baki, kuma al’ummarta masu tausayi da nuna jin kai.”
Yana mai jaddada cewa: Iran wata kafa ce da ta dace da zuba hannun jarin kasuwanci da yawon bude ido na ketare, Pezeshkian ya bayyana cewa da wannan karfin, kuma ta hanyar ciniki, zuba hannun jari, da hadin gwiwa, za a iya samar da makoma mai haske ga duniya, mai cike da tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma yi nuni da cewa: Yake-yaken da suka gani a duniya sun samo asali ne sakamakon rashin mutunta hakkokin bil’adama da na kasashe, Pezeshkian ya jaddada mutunta yankin kasar Iran da hakkokin kasashe, yana mai bayyana Shirin Iran na gudanar da duk wani hadin gwiwa a fannin kimiyya, tattalin arziki, siyasa, da zamantakewa da duniya, da kuma mika ilimi ga sauran kasashe ba tare da iyakancewa ba.