HausaTv:
2025-07-30@16:06:53 GMT

Iran: Tattaunawa kai tsaye da Amurka a yanzu ba shi ne zabinmu ba

Published: 9th, April 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo.

Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya.

Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya.

Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma matsaya, inda za ta halarci tattaunawa a kasar Oman a ranar Asabar.

Ya kuma kara da cewa, wannan ba sabon lamari ba ne, domin ita kanta Amurka tana tsakiyar yin shawarwari kai tsaye game da batun Rasha da Ukraine, batun da ya fi zafi da sarkakiya ta fuskar siyasa da tattalin arziki a mataki na kasa da kasa.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya bayyana cewa yana da gogewa a baya a tattaunawar kai tsaye da Amurka wacce kungiyar EU ta shiga tsakani a shekarar 2021.

Araghchi ya bayyana cewa duk da cewa ba a cimma matsaya ba a lokacin, amma da farko lamarin  ya faru ne saboda rashin azama ta gaskiya daga gwamnatin Biden.

Ya ci gaba da cewa tattaunawar kai tsaye zabi ne wanda zai iya yiwuwa, amma kuma saboda masaniya a kan abubuwan da suka faru a baya Iran tana da cikakiyar masaniya da gogewa game da salon tattaunawa da Amurka, domin kuwa Iran ba ta amince da Amurka ba, amma kuma hakan ba zai hana tattaunawa ba.

Ya kara da cewa, Iran ba za ta taba amincewa da tattaunawa karkashin matsin lamba da kuma barazana ta sojia  kanta ba, amma za ta amince da tattaunawa ne kawai a karkashin fahimta da kuma girmamma juna.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Araghchi ya

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Tattaunawar Nukiliya Wani Zabi Ne Mai Muhaimmanci Wanda Ya Karfafa Matsayin Iran A Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na                         kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan.

Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar Iran da ma matakan da aka dauka na yin shawarwari da kasashen yammacin duniya. Ya yi bayanin cewa, manufar yarjejeniyar makamashin nukiliyar ta ginu ce bisa ka’ida mai ma’ana, ta yadda Iran za ta dauki matakai na karfafa kwarin gwiwa domin dage takunkumin kanta.

Jami’in na Iran ya yi nuni da cewa, a lokacin da gwamnatin Trump ta Amurka ta bayyana burinta na yin shawarwari kan batun makamashin nukiliyar, Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawa bisa wannan manufa, tare da jaddada cewa, ba za ta amince da duk wani sharadi da zai kawo cikas ga shirinta na nukiliya ko kuma dakatar da ayyukan inganta sinadarin Uranium ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
  • Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
  • Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
  • Araqchi: Tattaunawar Nukiliya Wani Zabi Ne Mai Muhaimmanci Wanda Ya Karfafa Matsayin Iran A Duniya
  • Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Iran Da Rasha                                                                                                                       
  • Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Kasashen Iran Da Rasha