Amurka ta karbi Amurkawa 3 da suka yi yukurin juyin mulki a Congo
Published: 9th, April 2025 GMT
Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna hannun Amurka bayan yanke hukuncin da aka yi a kansu a makon jiya, kamar yadda wasu jami’an Amurka da na fadar shugaban kasar Kongo suka bayyana ga kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan Talata.
A ranar 19 ga Mayu, 2024, wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji sun mamaye ofishin shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi bayan da suka mamaye gidan ministan tattalin arzikin kasar mai barin gado kuma dan takarar shugaban majalisar dokokin kasar Vital Kamerhe.
An bayar da rahoton mutuwar mutane shida da suka hada da jami’an ‘yan sanda biyu a lokacin yunkurin juyin mulkin.
An kammala yanke shawarar mika Amurkawan ne yayin da babban mai baiwa shugaba Donald Trump shawara kan harkokin Afirka, Massad Boulos, ya gana da shugaba Felix Tshisekedi a Kinshasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran
A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya.
A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance kasa da abin da ake bukata, bisa la’akari da dama da karfin da bangarorin biyu ke da shi.
A yayin ganawar, Aref ya tunatar da ziyarar da ya kai birnin Qairawan na kasar Tunusiya shekaru ashirin da suka gabata, lokacin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar na farko na Jamhuriyar. Ya kara da cewa a lokacin yana jin kamar ya ratsa daya daga cikin garuruwan Khorasan na kasar Iran, yana daukar birnin Qairawan wata alama ce ta hadin kan al’ummar musulmi da alakar al’adu da addini tsakanin Iran da Tunisiya.