Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
Published: 31st, March 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka amsar wasikar da ta aiko mana, inda a cikinta, muka kara jaddada cewa babu wata tattaunawa kai tsaye da Amurka, kuma an tura wasikar ta inda na Amurkan ta fito wato ta kasar Omman.
Daga karshe shugaban ya kammala da cewa duk wata mu’amala da gwamnatin kasar Amurka ba zai taba yiyuwa kai tsaye ba, wannan kuma saboda mummunan tarihin da Amurkawa suke da shin a karya al-kawali a duk wata yarjeniyar da aka cimma da ita a baya.
Ya dukkan tarihin JMI bata taba sabawa alkawalin da ta dauka da wata kasa ba, amma gwamnatin Amurka kuma tana da mummunan tarihi na sabawa alkawali don haka a halin yanzu ya rage mata ta sauya halayenta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.