Aminiya:
2025-07-08@06:25:59 GMT

Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Published: 19th, March 2025 GMT

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda.

Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi

Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar.

‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’

Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya kasance yana aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce duk da tankiyar siyasa, ya ci gaba da gudanar da aiki don tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutanen Jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa bayan shugaban ƙasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya kiyaye duk yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karɓar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.

Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar da doka da oda suka tanadar.

‘Majalisar dokokin Ribas ta hana ruwa gudu’

Gwamnan ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi domin samar da zaman lafiya, ’yan majalisar dokokin jihar sun kawo cikas.

Ya ce yana aiki ne don tabbatar da an kare dimokuraɗiyya da ci gaban mutanen jihar amma majalisar ta riƙa hana ruwa gudu.

A cewarsa, duk da saɓanin siyasa da ake fama da shi, gwamnatinsa na biyan albashin ma’aikata tare da aiwatar da manyan ayyuka don ci gaban jihar.

Fubara ya bayyana cewa duk da ƙalubalen siyasar, ya tabbatar da jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu wata barazanar tsaro da ake fuskanta.

A ƙarshe Fubara ya buƙaci mutanen jihar da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace don kare dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Siminalayi Fubara tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Ambaliyar Texas Ya Haura 80

Hukumomi a jihar Texas da ke Amurka sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 80 sakamakon ambaliyar da ta auka wa jihar tun a ranar Juma’a.

Mutum 68 daga cikin waɗanda suka mutu ciki har da ƙananan yara 28, a gundumar Kerr suke.

Har yanzu akwai ƴanmata 10 da mai kula da wurin shaƙatawar Mystic da ba a ji ɗuriyarsa ba.

Alƙaluman waɗanda suka mutu na sauyawa cikin hanzari, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da lalubo gawarwaki.

Shugaba Trump ya ce ya tsara zuwa yankin da lamarin ya faru cikin wannan mako

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutum 38,000 a Yobe
  • An ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutum 38,000 a Gombe
  • Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi
  • Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa ta Kwace Gurbatattun Kayayyaki na Miliyoyin Naira
  • Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos
  • Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Ambaliyar Texas Ya Haura 80
  • China Ta Maida Martani da Haka Kayakin Kiwon Lafiya Na Tarayyar Turai Shigowa Kasar
  • Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato
  • Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC
  • Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano